Rikicin Ukraine: Mene ne hatsarin harba makaman nukiliya?

    • Marubuci, Daga Gordon Corera
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC News kan sha'anin tsaro

Ranar Lahadi Shugaba Vladimir Putin ya umarci dakarunsa masu kula da makaman nukiliya su kasance cikin shirin ko-ta-kwana. Shin me wannan umarnin ke nufi?

Masu nazarin siyasar Yammacin Turai sun ce babu wanda ya san amsar wannan tambayar.

Jami'an gwamnatin Birtaniya na cewa kalaman na Putin ba su yi daidai da tsarin da Rasha ke amfani da shi a fagen yakin nukiliya ba.

Amma akwai wadanda ke cewa ya dauki matakin ne kawai domin ya aika da sako, ba domin da gaske yana son yin amfani da makaman ba.

Sakataren Ma'aikatar Tsaron Birtaniya Ben Walace ya ce a ganinsa, Putin ya yi sanarwar ce domin razanarwa kawai.

Sai dai wannan ba yana nufin babu hatsari dangane da manufar shugaban na Rasha ba ne.

Shin wannan sabon gargadi ne?

A makon jiya, Putin ya yi wani gargadi amma a fakaice, yana cewa idan wasu kasashe suka yi katsalandan cikin aikin Rasha, za su "fuskanci martanin da ba su taba gani ba". Ana fassara wannan kashedi ne ga kungiyar tsaro ta Nato.

Sai dai dama Nato ba ta ce za ta shiga cikin rikicin Rasha da Ukraine ba kai-tsaye, ganin cewa zai iya haifar da yaki da makaman nukiliya. Kashedin na ranar Lahadi an yi shi ne domin jama'a su ji.

Mene ne dalili wannan sabon gargadin?

Putin ya ce ya mayar da martani ne ga wasu "kalamai na tsokanar fada". A ranar Litinin fadar Kremlin ta yi nuni ga wasu kalamai da jami'an Yammacin Turai suka yi, ciki har da na Sakatariyar Harkokin Waje Liz Truss kan yiwuwar karawar Nato da Rasha.

Wasu na cewa Putin bai yi tsammanin Ukraine za ta nuna turjiya sosai ba a fagen-daga. Sun kuma ce bai yi tsammanin irin martanin da kasashen Yammacin Turai za su mayar ba ta hanyar saka wa Rasha jerin takunkumai.

"Wannan alama ce ta fusata da rashin samun yadda ya so," in ji wani tsohon Janar na sojan Birtaniya.

Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya linda Thomas-Greenfield ta ce kalaman da Putin ya yi amfani da su cewa Ukraine ce ta fara tsokanar fada, ya yi su ne domin kawai ya kai hari cikin kasar.

To mene ne hatsarin?

Ko da gargadin da Putin ya yi zai kasance kashedi ne kawai ba domin yana son kai harin nukiliya ba da gaske, amma akwai hatsarin wani bangare ya yi kuskuren fahimtar abin da daya bangaren ke nufi idan abubuwa suka rincabe.

Wata damuwar ita ce babu wadanda ke iya bai wa Putin shawara kan ainihin abubuwan da ke wakana saboda ana tsoronsa. Wasu na fargabar cewa tunaninsa ya raunana.

Wasu na cewa ko da Putin ya bayar da umarnin a harba makaman nukiliya, za a sami wasu cikin jami'ansa da za su taka wa al'amarin birki ta hanyar bijire wa umarnin nasa.

Hatsarin aukuwar amfani da makaman nukiliya ya karu amma da 'yar tazara kafin a kure mizanin da ke auna hatsarin yaki da makaman nukiliya.

Wane martanin kasashen Yammacin Turai ke mayar wa Rasha?

Kawo yanzu kasashen Yammacin Turai suna taka-tsantsan domin kaucewa kazancewar rikicin.

Amurka na da tsarin kare kasarta mai suna defcon, kuma a yau kakakin Fadar White House Jen Psaki ta ce babu dalilin sauya matakan tsaron kasar domin mayar da martani kan matakin da Rasha ta dauka.

Birtaniya na da jiragen karkashin ruwa da ke kai-komo a teku kuma da wuya ta ce komai a yanzu.

Dukkan alamu na cewa kasashen Yammacin Turai ba su dauki kalaman Rasha a matsayin na kaddamar da yaki da makaman nukiliya ba.

Jami'an gwamnatocin kasashen Yammacin Turai na cewa a yanzu dai babu yiwuwar a gwabza yaki da makaman nukuliya ba, kuma bai kamata a bari lamarin ya kai ga haka ba.