An jinjina wa sojan da ya taimaka wa mace ta haihu a gonar masara a Zambia

Asalin hoton, Zambia Reports
- Marubuci, Kennedy Gondwe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service, Lusaka
An jinjina wa wani sojan Zambia bayan ya taimaka wa wata mace mai ciki ta haihu.
Sojan, mai igiya daya mai suna Humphrey Mangisani, yanzu an yi masa karin girma zuwa cikakken mai igiya biyu saboda wannan bajinta da ya yi.
Ya samo wani babur aka dora ta a kai domin kai ta asibiti yayin shi kuma ya bi su a babur dinsa, amma sai nakuda ta kama ta a hanya inda suka tsaya a wata gonar masara ya taimaka mata ta haihu.
Ya samo reza ya yanke cibiyar jaririn.
"Na yi kasadar barin wurin aikina inda na bar sansaninmu domin na taimaka mata," in ji Mista Mangisani a hirarsa da jaridar Zambia Reports.
Ya ce ya dauki jaririn zuwa asibiti.
Mangisani ya ce an horas da shi kan yadda zai iya yin kundunbala kuma ya yi hakan ta hanyar taimaka wa mai cikin ta haihu a yankin Petauke da ke gabashin kasar.
Domin girmama shi kan bajintar da ya yi, an ba shi dama ya rada wa jaririn suna don haka ne ya sanya masa suna Raymond Tembo.
Shugabansa a rundunar sojin kasa ya ce abin da ya yi zai sauya irin kallon da ake yi wa sojojin kasar.
Maimakon a rika daukarsu a matsayin masu mugunta, Birgediya Janar Kelvin Kanguma ya ce Mangisani ya nuna cewa "soja mutum ne da zai iya taimako".
Jarirai sabbin haihuwa fiye da 100 ne suke mutuwa a Zambia duk mako sakamakon kura-kurai da matsalolin da ake samu wajen karbar haihuwa, a cewar ministar lafiyar kasar Sylvia Masebo.











