Abin da ya sa matasa ke ƙara shiga harkar tsafi don neman kuɗi a Najeriya

tsafi

Asalin hoton, Getty Images

Mutane da dama sun sha mamaki lokacin da 'yan sanda suka gabatar da wasu yara da ake zargi da kisan budurwa ɗaya daga cikinsu don yin tsafi a makon da ya gabata a Najeriya.

Kafin kama yaran, rahotannin yin tsafi da zimmar neman kuɗi ya karaɗe ƙasar kuma mutane na ta mamakin yadda Najeriya ta tsinci kanta a wannan hali.

Hakan ta sa BBC ta tattauna da wasu ƙwararru kan tsaro da lafiyar yara da kuma wani lauya don amsa tambayar dalilin da ya sa lamarin ke ƙara ƙara ƙamari.

Yaya kisa don yin tsafi yake?

Alƙaluma na hukuma sun nuna cewa kashe-kashe don yin tsafi sun ƙaru a faɗin Najeriya, musamman kan mutanen da suka ɓace.

'Yan sanda kan gano wasu yayin da wasu kuma ba a ganin ko gawarsu. Ana yawan cewa akasarin waɗanda suka ɓace aka kasa ganinsu sama ko ƙasa, masu tsafi ne suka kashe su.

Mafi yawan lokaci bokaye ne ke umartar su da su yi yanka don su samu wani iko ko kuɗi ko kuma warkewa daga wata cuta. Sai dai ba abu ne mawuyaci a iya tabbatar da cewa maganin da ake ba su yana aiki.

'Yan sandan Najeriya da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa sun tsananta ayyukansu don gano masu aikata kisan tsafi, mafi yawansu matasa.

'Ƙarancin kulawar iyaye ce matsalar'

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta Jihar Delta da ke kudancin ƙasar, DSP Dafe Bright, ya faɗ wa BBC Pidgin cewa rashin tarbiyyar iyaye ce da kuma neman yin kuɗi cikin sauri ne ke haddasa irin wannan matsalar.

A cewar jami'in ɗan sandan, wasu iyayen ne ke ɗaukar nauyin yaransu su je su koyi zamba ta hanyar intanet.

"Matsalar rashin tarbiyyar iyaye ce. Wasu iyayen na neman kuɗin da za su tura yaransu koyon aikata zamba ta intanet, abin da ke faruwa yanzu kenan a al'ummarmu.

"Matsalar farko a wannan lamarin rashin tarbiyya ce, sai kuma son neman kuɗi cikin sauri. Matasa ba sa son zuwa makaranta yanzu, waɗanda ke zuwa kuma sun fi son su yi amfani da kuɗi su sayi sakamako. Yunwar neman kuɗi cikin sauri na daga cikin dalilan da ke haddasa hakan, amma dai rashin tarbiyya ce kan gaba."

Pipo wey dey do rituals

Asalin hoton, Getty Images

Gasar yin kuɗi

Kakakin tsaro ta Security and Civil Defence Corps (NSCDC) na Jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce gasar da matasa ke yi da junasu ce ke ƙara ta'azzara kashe-kashen don neman kuɗi.

Ya ce matasa 'yan damfara da ake kira Yahoo Boys sun yawaita ayyuka a ƙasar nan kuma gasa ce ke sa matasa shiga damafarata intanet.

"Yaho boys sun ƙwace komai. Idan yaro mai shekara 15 ya ga tsaransa da motoci na alfarma, shi ma sai ya ce sai ya samu irinta, sai kuma ya bi irin wannan hanyar. Ɗaya daga cikin matsalar kenan," a cewar Afolabi.

Shi ma jami'in na civil defence ya zargi iyaye game da matsalar, yana mai cewa ba sa sa ido kan yaransu.

'Ma'anar nasara ta sauya a tsakanin al'umma'

Barista Elizabeth Azubuike, wadda ta kafa ƙungiyar kare haƙƙin yara ta Total Child Initiative, ta ce daga cikin tushen matsalar akwai sauya ma'anar "nasara" da mutane suka yi a yanzu.

Ta ce abin da mutane suke kira nasara shi ne idan mutum ya samu kuɗi da zai dinga wadaƙa.

Ita ma ta zargi rashin tarbiyya daga wasu iyaye.

"Tasirin iyaye da na al'umma na daga cikin dalilan matsalar," kamar yadda ta faɗa wa BBC Pidgin.

Ta ƙara da cewa mutane da yawa ba sa ƙoshi da abin da suke da shi, saboda haka sai su shiga tsafi.

"Iyaye malalata ba sa kula da tarbiyyar yaransu, ka ga kuwa dole su shiga harkar tsafi."

Mece ce mafita?

tsafi

Asalin hoton, Getty Images

Afolabi ya ce iyaye da gwamnati na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen kawo ƙarshen matsalar a cikin al'umma.

"Matasan da suka gama makaranta ba su samu aiki ba dole su yi tunanin zaɓin da ya rage musu. Ya kamata gwamnati ta samar da ayyukan yi ga matasan don shawo kan matsalar," in ji shi.

Barista Azubuike ta shawarci iyaye da su san abubuwan da 'ya'yansu ke aikatawa da kuma abokansa.

"Idan kana tunanin ka gaza a harkar tarbiyya, ka koma ka zauna ka tsara hanyar da za ka ƙwato yaronka daga abin da ya ƙwace shi daga hannunka," a cewarta.

"Wasu daga cikin yaran nan na buƙatar bayanai kuma ya kamata gwamnati ta ɗauki ƙwararru don su horar da su kuma su dawo da su cikin al'umma."