Dalilai biyar da suka janyo wargajewar Tarayyar Soviet

    • Marubuci, Daga Kateryna Khinkulova & Olga Ivshina
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian

A ranar 25 ga watan Disambar shekarar 1991, Mikhail Gorbachev ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban Tarayyar Soviet. Bayan kwana daya wato ranar 26 ga watan Disambar, majalisar dokokin kasar - a hukumance ta amince da samun 'yancin cin gashin kan sabbin jihohi 15, wanda hakan ya kawo karshen kasancewar Tarayyar Soviet.

An sauke jar tuta mai alamar guduma da kuma lauje zuwa kasan Kremlin, da a baya ta zama wata alama da daya daga cikin kasashen duniya mafi girma.

Gorbachev ya fara mulki a shekarar 1985, lokacin yana da shekara 54. Ya fara yin jerin garanbawul domin farfado da al'amuran tafiyar kasar da suka riga suka lalace.

Da dama wasu na ganin wadannan sauye-sauye da ake kira Perestroika (sake ginawa da farfadowa) da Glasnost (samar da bayanai da 'yancin fadin albarkacin baki), sun haifar da rugujewar kasar. Wasu kuma sun bayyana cewa al'amuran kasar Tarayyar Soviet sun wuce batun cetowa, idan aka duba yanayin yadda abubuwa suka yi mata kanta.

A nan za mu duba abubuwan da suka haifar da rugujewar wanda ke da tsananin tasiri a kan yadda kasar Russia ke kallon kanta da kuma yadda take mu'amalarta da sauran kasashen duniya.

1. Tattalin arziki

Durkushewar tattalin arziki shi ne abu mafi girma cikin duka matsalolin Tarayyar Soviet.

Kasar na da wani babban tsari na tattalin arziki, wanda ke cin karo da kasuwanci da tattalin arzikin sauran kasashe.

A Tarayyar Soviet, kasar ke yanke hukunci kan yawan abubuwan da za a sarrafa ko kera (ko motoci nawa, ko takalma nawa ko burodi nawa)

Tana kuma yanke shawarar ko nawa ne wadannan abubuwa ko wane dan kasa ke bukata, da kuma kididdige farashin ko wane kaya da kuma ko nawa ya kamata a biya mutane.

Dabarar ita ce wannan tsari zai kasance ingantacce kuma cike da gaskiya da adalci, amma a zahiri yana tangal-tangal ne.

A koda yaushe samun kayyaki na tafiyar hawainiya wajen bukata, kana kudi ya zama maras amfani.

Mutane da dama a Tarayyar Soviet ba matalauta ba ne, amma kuma ba za su iya samun wadatattun abubuwan amfanin yau da kullum ba saboda ba a samar masu da su a wadacen ba.

Kafin ka sayi mota sai ka shafe shekaru kana jira a kan layin sunan masu sayen. Kafin ka sayi kwat ko takalman sanyi dole sai ka shafe sa'oi kana bin layi, wanda daga karshe za ka iya samun cewa na daidai kafarka ya kare.

A Tarayyar Soviet mutane ba sa magana game da sayen wani abu (kupit'), sai dai mallakarsa (dostat').

Abin da ya kara ta'azzara abubuwa shi ne takaddamar Tarayyar Soviet da Amurka kan mallakar manyan makamai da aka fara a karshen shekarar ta 1950.

Tarayyar Soviet ita ce kasa ta farko a duniya da ta fara aikewa da mutum zuwa duniyar sama jannati, kana ta mallaki rumbun ajiyar makaman nukiliya da kuma manyan makamai masu linzami, amma kuma dukaninsu masu tsananin tsada ne.

Kasar ta dogara da arzkinta na karkashin kasa kamar sun man fetur da iskar gas wajen gudanar da wadannan ayyuka, amma a farkon shekarar 1980 farashin man ya karye ya kuma yi wa tattalin arzikin karan-tsaye da dama ya riga ya durkushe.

Manufofin Perestroika na Gorbachev Perestroika ya bullo da wasu dokoki amma kuma tattalin arzikin Soviet na da matukar wahalar yi wa garanbawul cikin sauri.

Kayayyakin amfani na jama'a sun cigaba da kasancewa cikin karanci, kana farashinsu ya kara tashin gwauron-zabi.

A shekarar 1990, mahukunta sun bullo da sauye-sauye ga harkokin kudade wanda ya soke ajiyar kudade a asusun bankuna, duk da kankantarsu cikin miliyoyin mutane.

Me yasa hakan ke da muhimmanci a yanzu?

Karancin kayyakin amfanin yau da kullum na jama'a ya haifar da mummunan tasiri kan al'ummar Soviet na baya.

Ko a yanzu ma - masu tasowa nan gaba - akwai nuna fargaba game da tafiyar da rayuwa babu ababen amfani na yau da kullum.

Babban abin damuwa ne wanda za a iya amfani da shi cikin sauki lokacin gangamin yakin neman zabe.

2. Akida

Manufofin Glasnost na Gorbachev na da nufin samar da gagarumin 'yancin fadin albarkacin baki a kasar wacce ta shafe shekaru da dama karkashin mulkin danniya inda mutane ke tsoron fadin abin da ke ransu, ko tambaya ko kuma kokawa.

Ya fara bude ma'ajiyar kayayyakin tarihi da ke nuna tsagwaron gaskiyar mulkin danniya a karkashin shugabancin Joseph Stalin (daga tsakanin shekarar 1924 da 1953), wanda ya haddasa mutuwar miliyoyin mutane.

Ya karfafa guiwar gudanar da muhawara game da makomar Tarayyar Soviest da karfin tsarin mulkinta, kan yadda ya kamata a yi musu garanbawul don samun cigaba.

Ya kuma rika dari-dari da shawarar kawo tsarin siyasar mai jam'iyu da yawa, tare da kalubalantar kankanewar jam'iyar Kwaminisanci.

A maimakon kokarin amfani da shawarar Soviet, wadannan abubuwa sun haifar wa da mutane da dama a Tarayyar Soviet din amince cewa tsarin jam'iyar Kwaminisanci - inda jami'an gwamnati ko an nada su ne ko kuma an zabe su ne ta hanyar gudanar da zaben da ba ta hanyar takara ba - ba sahihi ba ne, kama-karya ne, kana bude hanyar cin hanci da rashawa ne.

Gwamnatin Gorbachev cikin sauri ta bullo da wasu hanyoyin samun 'yanci da kuma tsari zabe na gudanar da sahihin zabe, amma kuma ya yi kadan kuma latti.

Me yasa hakan ke da amuhimmanci a yanzu?

Shugaban kasar Russia Vladimir Putin ya gano muhimmancin tsarin kasa mai karfi, musamman ga gwamnatin da gabaki dayan ta ba mai bin tsarin gaskiya da tafarkin dimokaradiyya ba ce.

Ya yi amfani da tsare-tsare daga lokutan Russia da Soviet na baya wajen martaba tsarin kasarsa da shugabancinsa: dukiya da alfarmar kasar Russia mai girma, da kima, da sadaukarwa da nasarori a Yakin Duniya na Biyu karkashin Stalin da kuma kwanciyar hankali da zaman lafiyar lokacin Soviet a 1970 an hade su wuri guda don karfafa guiwar yin alfahari da nuna kaunar kasa.

3. Kishin kasa

Tarayyar Soviet kasa ce mai kasashe da dama a hade, wacce ta gaji tsarin masarauta na kasar Russia.

Ta kunshi jamhuriyoyi 15, da ke da daidaito a yanayin 'yancinsu a matsayin kasashe 'yan uwan juna.

A zahiri, kasar Russia ita ce mafi girma kuma mafi karfi, kana harshen kasar Russia da al'adu don mamaye yankunan.

Glasnost ya sa mutane da ana a sauran jamhuriyoyin tunawa da mulkin danniya da kabilancin da da sauran abubuwan da suka faru a baya, da suka hada da abkuwar fari a kasar Ukrainia a shekarar 1930, da karbe ikon kasashen yankin Baltic da yammacin Ukraine a karkashin kawancen Soviet da Nazi, da kuma tilasata tasa keyar kabilu da dama a lokacin Yakin Duniya na Biyu.

Wadannan abubuwan da suka faru ne da suka haifar da karuwar kishin kasa da bukatun kasancewa masu jajircewa.

Me yasa hakan ke da muhimmanci a yanzu?

Damuwa a tsakanin kasar Russia, kokarin ganin ta taka rawarta ta kasancewa jagora da mai karfin fada a ji, da kasashen Tarayyar Soviet sun cigaba da wanzuwa.

Dangantaka tsakanin Moscow da kasashen yankin Baltic, da Georgia ta baya bayna nan - da kuma mummunan tasiri - Ukraine ta cigaba da tsara taswairar kasashen Turai da sauransu.

4. Gushewar hankali da tunani

An sanar da mutanen Tarayyar Soviet kasashen Yamma ''a gurbace suke'' kana mutanenta na fama da wahala da talauci da tabarbarewar rayuwa a karkashin gwamnatocin 'yan jari-hujja.

'Yan kasar Soviet na iya ganin cewa a kasashe da dama yanayin tsarin rayuwa da samun 'yancin cin gashin kai, da walwala da jin dadi ya zarta na wadanda ke cikin kasar.

Suna kuma iya fahimtar abinda hukumominsu suka yi kokarin boyewa a cikin shekaru da dama, ta hanyar haramta tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, da rufe hanyoyin tashoshin rediyo (kanar su BBC) da kuma sa ido da tantance duk wasu litattafai ko fina-finai a cikin Tarayyar Soviet.

An yaba wa Gorbachev wajen kawo karshen yakin cacar baka da dakatar da barazanar kai harin makaman nukiliya ta hanyar gyara dangantaka da kasashen Yamma, amma sakamakon hakan ya sa mutanen Soviet suka kara fahimtar yadda rayuwarsu ta ke cikin hali na talauci idan aka kwatanta da na wadanda ke sauran kasashe.

Gorbachev ya kara samun tagomashi a kasashen waje a yayin da ya rika fuskantar karin suka a cikin gida.

Me yasa yake da muhimmanci a yanzu?

Gwamnatin kasar Russia ta kasance mai juya yanayin sakonnin da ke fitowa daga kafafen yada labarai a bisa daidai da bukatunta.

Don kaucewa kwatanta ta da sauran kasashen duniya, akan gabatar da Russia a matsayin wata ta daban a fannin al'adu da tarihi - jaruma, mai kewaye da wadanda ba sa kaunarta.

Ana cigaba da amfani da cigabanta a fannin kimiyya da nasarori lokacin Yakin Duniya na Biyu da bunkasa al'adu a cikin labaran kafafan yada labarai don karkatar da tunanin kasar Rusiisa daga matsalolin yau da kullum.

5. Shugabanci

Gorbachev ya san cewa akwai bukatar tsaurara matakan kawo sauyi don dakatar da matsalar tabarbarewar tattalin arzikin Soviet da kuma karfafa guiwar jama'a, amma kuma tunaninsa game da yadda za a cimma wanna buri ya rasa cikakkiyar madafa.

Bayan da ya kawo karshen Yakin Cacar Baka, ya zama wani tauraro ga kasashen duniya, amma a cikin gida masu fafutikar kawo sauye-sauye da suke ganin ya kwace komai, da kuma masu ra'ayin mazana jiya sun yi ta sukar lamirinsa da cewa yana wuce gona da iri.

Masu ra'ayin mazan jiya sun yi yunkurin kaddamar da mummunan juyin mulki a watan Agustar shekarar 1991 don hambarar da Gorbachev daga kan karagar mulki.

Bayan kasa da kwanaki uku jagororin juyin mulkin da bai samu nasara ba sun yi yunkurin tserewa daga kasar, kana Mista Gorbachev ya sake dawowa mulki amma takaitacce.

Boris Yeltsin a kasar Russia da shugabannin al'umma a sauran yankunan Tarayyar Soviet sun wuce gaba.

Bayan 'yan watanni 'yan jamhuriyoyi da dana sun gudanar da kuri'ar raba gardama game da 'yancin cin gashin kai kuma zuwa watan Disamba aka san makomar babbar kasar.

Me ya sa haken ke da muhimmanci a yanzu?

Vladimir Putin daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a kan karagar mulki ne.

Daya daga cikin sirrikan dadewarsa shi ne saka kasar Russia a gaba fiye da komai.

A yayin da ake ta sukar lamirin Mikhail Gorbachev kan sadaukar da matsayin karfin ikon da dama na Tarayyar Soviet, kamar janyewar dakarun Soviet daga Gabashin Jamus, da fadan Vladimir Putin kan abin da ya yi amanna game da muradun kasar Russia ne.

Putin ya kasance jami'i ne a hukumar leken asiri ta KGB a kasar Gabashin Jamus a lokacin da Katangar Berlin ta fadi, kana ya shaida yadda tashin hankalin da janyewar Soviet ya haifar.

Bayan shekaru talatin, ya fito karara ya nuna adawa da nausawar kungiyar tsaro ta NATO kusa da kan iyakar kasar Russia, kana a shirye yake a goyi bayan haka da karfin soji, saboda abinda ke nuni da mamayar dakarun Russia a kusa da kasar Ukraine.