Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zabuka kasar Rasha: Abu biyar da ya kamata ku sani kan zabukan Rasha
- Marubuci, Daga Kateryna Khinkulova
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
Rasha za ta fara gudanar da zabukan 'yan majalisa da kananan zabukanta daga ranar Juma'a 17 zuwa 19 ga watan Satumbar nan da muke ciki.
Shugaba Vladimir Putin ya ce, wannan 'wani lokaci ne mai hamimmanci ga rayuwar mutanen Rasha da kasar baki daya".
Amma me yasa wannan zaben ke da mahimmanci?
Domin samun damar fahimtar hakan ga wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani.
1. Wa za a zaɓa, wanene me yin zaɓen?
An kusa lashe duka kujerun majalisar Rasha 450 da ke majalisar dokokin kasar wadda ake kira State Duma.
Rasha na da duka majalisar dokoki da kuma shugaban kasa.
Shugaban kasar ne ke da cikakken iko kan abin da ya shafi siyasa da tattalin arziki da ci gaban kasar, amma ita majalisa ce da ikon samar da sabbin dokoki.
Rasha kasa ce da ke bin tsarin federaliyya tana da jihohi ko yankuna 85. Akwai 'yan majalisar dokoki na jiha kamar yadda ake kiransu, kuma suna taka muhimmiyar rawa a wajen ci gaban yankin, ta yadda suke da iko kan abin da za a rika kashe wa da abubuwan da suka shafi rayuwar mutane ta yau da kullum kai tsaye.
Shi yasa wadanda ake zaba a matsayin 'yan majalisar tarayya suke zama kamar ba su da amfani ga rayuwar mutane. A wannan karon wasu bangarorin kasar za su gudanar da zabukansu - ko dai na kansiloli ko kuma na 'yan majalisu 39 daga cikin yankuna 85 ko kuma gwamnonin yankuna tara ko jihohi.
Rasha da tsarin kada kuri daba-daban - rabin 'yan majalisar Duma ana zabarsu a karkashin jam'iyya sauran kuma wadanda aka fara zaba ne ke zabarsu.
Akwai sama da mutane miliyan 108 da suka yi rijistar zabe a Rasha.
Akwai kuma 'yan kasar sama da miliyan biyu da za su yi zabe daga kasashen waje. Akwai rumfunan zabe sama da 95,000 da za a gudanar da zabukan ciki.
2. Saboda me ake kwashe kwana uku ana zaben?
A yadda aka saba, ana gudanar da kada kuri'ar zabe a Rasha ne a ranar Lahadi kuma yakan haura rana guda ana yi.
Tun bayan bullar annobar korona da kuma dokar ba da tazara saboda cutar aka tsawaita ranakun zaben zuwa sama da kwanaki uku saboda tabbatar da ba da tazara.
A wannan sabon tsarin za a fara kada kuri'ar a ranar Juma'a 17 ga watan Satumbar da muke ciki zuwa 19 ga watan.
A wasu yankunan na Rasha mutane za su iya kada kuri'unsu ta intanet ta shafin hukumar zaben kasar.
3. Wanene ke da ruwa da tsaki a ciki?
Akwai gwamman jam'iyyun siyasa da suka shiga zaben yayin da daruruwan 'yan takara za su fafata da juna.
Mafi yawan su 'yan babbar jam'iyya ne wadda ta ke lashe mafi yawan zabukan da ake gudanarwa.
Wannan gangamin ya fito ne daga 'yan takarar jam'iyyar adawa wadanda aka hana shiga cikin zabukan.
Hukumomin Rasha sun ce an haramta musu shiga zabukan ne saboda gudanar da binciken manyan laifuka da ake yi a kansu.
Cikin wadanda aka haramta wa har da 'yan takarar da aka zaba a baya a kananan hukumomi da kuma wadanda ba a taba zaba ba.
Shugaba Putin da kan sa ba zai shiga zaben ba - tun da shi ma ba za a zabe shi a matsayin dan majalisa ba sai dai ya je ya kada kuri'a.
4. Mene ne "smart voting" kuma wace rawa Google ke takawa a kansa?
A 2018, babban dan adawar Rasah Alexei Navalny da magoya bayansa suka zo da tsarin kada kuri'a da ake kira "smart voting" wanda suke ganin hakan zai iya takaita karfin iko da jam'iyya mai mulki da shi.
Sun samar da wata manhajar da za su rika shawartar masu kada kuri'a wanda za su zaba,
Navalny ya ce wannan tsari zai tabbatar da magudin da ake zargin jam'iyya mai mulki ke yi wanda 'yan adawa ke zargi.
A farkon wannan watan ne ranar 6 ga Satumba, hukumar da ke sa ido kan kafofin watsa labaran Rasha ta rufe shafin intanet din smart voting, in da ta ce ana amfani da tsarin wurin gudanar da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.
5.Yaushe za a sa ran samun sakamakon zaben?
Ya danganta da yankin da aka yi zaben.
A wasu yankunan kuwa za a fara samun sakamakon a ranar Litinin 20 ga watan Satumbar amma a wasu zai fi haka jimawa saboda yawan al'umma.
Akwai kuma damar soke wasu zabunkan gwamnoni da za a yi a yankuna ko kuma jihohin kasar.