Omicron: Ta yaya ake gane sabon nau'in cutar korona mai firgita duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Philippa Roxby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan lafiya
An gano sabon nau'in kwayar cutar korona mai suna Omicron a karon farko a Birtaniya, bayan da masana kimiyya suka bayyana bullarta a kasar Afirka ta Kudu a matsayin mai hadarin gaske.
Wadanne irin gwaje-gwaje ake amfani da su wajen gano kwayar cutar ta Omicron?
Wasu kyallaye da ake dibar samfurin majina daga hancin wadanda ake yi wa gwajin kwayar cutar da akan aike zuwa dakin gwaje-gwaje don gudanar da bincike ne kan gano ko mutane sun kamu da cutar korona ko kuma akasin haka.
Daga binciken ne, wanda ya danganta da dakin gwajin da aka aike da samfurin, kwararrun kan iya gano ko shin ya yi kama da nau'in kwayar cutar Delta ko Omicron, ko kuma wani sabon nau'in ne ke haddasa cutar.
Daya bisa ukun dakunan binciken Birtaniya - amma da duka ba - suna da fasahar zamanin da ake bukata wajen iya gano nau'in kwayar cutar.
Gwajin majinar su ne wadanda za ka iya nema daga shafin yanar gizo na gwamnati za zarar ka fahimci alamun kamuwa da cutar, ko kuma ka nema daga kamfani mai zaman kan sa idan kana bukatar gwajin saboda bukatu da bulaguro.
Ta yaya zamu gane cewa kwayar cutar Omicron ta bulla a Birtaniya?
An aike da sakamakon binciken gwaje-gwajen da ka iya kasancewa sabon nau'in kwayar cutar ta Omicron ne zuwa dakin gwaji don gudanar da cikakken nazari kan kwayoyin gado na halitta, ta hanyar amfani da salo da ake kira jigilar hada kwayoyin halitta wuri guda.
Wannan ya tabbatar da cewa wasu sun kamu da sabon nau'in kwayar cutar.
Wannan bincike na dakin gwaje-gwaje kan abubuwan da kwayoyin halitta suka kunsa muhimmin abu ne wajen gano sabbin nau'ukan da kuma gano dabi'arsu.
Akwai yiwuwar samun karin wasu na'ukan da dama a Birtaniya, amma har yanzu aka kasa ganowa, saboda ya kan dauki tsawon makonni kafin a kammala irin wannan bincike.
Har yanzu Delta shi ne nau'in kwayar cutar korona da yafi mamaye ko ina , wanda ake samun sabbin mutanen da suka kamu kimanin 40,000 a Birtaniyar.
Shin gwaje-gwajen yi da kan ka a gida ana iya gano kwayar cutar Omicron?
Gwaje-gwajen da mutane kan iya yi a gida za su iya nuna maka wane irin nau'in kwayar cuta ka kamu da ita - amma kuma har yanzu ana tunanin za su iya nuna makai dan ka kamu ko kuma baka kamu da shi kansa sabon nau'in ƙwayar cutar korona ta Omicron.
Menene banbancin dake tsakanin kwayar cutar Omicron da sauran nau'ukan?
Sabon nau'in kwayar cutar Omicron na da yanayin rikida da dama da ba a taba shaidawa ba, kuma wasu da dama sun nuna haka.
A gwaje-gwajen da kwararru da dama suka sa hannu, Omicron na da abinda ake kira "S-gene dropout" (wanda kwayar cutar Delta, a lokuta da dam aba ta da shi), kuma wannan ya bayar da alamar cewa za ta iya kasancewa sabon nau'in kwayar cutar.
Amma ba duka masu "S-gene dropouts" ne za su iya kasancewa omicron ba - Ana bukatar cikakken bincike na jigilar hada kwayoyin halitta wuri guda don tabbatar da hakan.
Wace rawa jigilar hada kwayoyin halittu ke takawa?
Kusan kashi 20 bisa dari na samfurin majinar da ake diba daga wadanda suka kamu da kwayar cutar a Birtaniya a kowane mako ko kuma kusan mutanen da suka kamu kusan 60, ana aike su ne wajen gwajin jigilar hada kwayoyin halitta.
Ta hanyar yi wa abubuwan da kwayoyin halittar suka kunsa kallon tsaf, masana kimiyya za su iya tabbatar da ko wani ya kamu da kwayar cutar Omicron ko kuma ta Delta da ta riga ta bazu a kusan ko ina.
Wannan hanya za ta kawai samar da bayanai game da samufurin majinar da ake gudanar da bincike a kai - amma kuma a yayin amfani da wadannan sakamako, masana kimiyya za su iya kididdige yawan adadin wadanda suka kamu da kwayar cutar ko sabob nau'in ce.
Masana kimiyya a Birtaniya da Afirka ta Kudu na kan gaba-gaba a kan wannna sabuwar fasaha, da hakan ya sa aka gano akasarin sabbin nau'ukan kwayar cutar a wadannan kasashe. Amma hakan bay ana nufin cewa sun samo asali daga can ba ne.
Me muka sani game da kwayar cutar ta Omicron?
Kadan aka sani game da irin dabi'un sabon nau'in kwayar cutar, da kuma yanayin girman hadarin da ta ke da shi.
Misali, babu tabbaci kan ko tana yaduwa cikin sauri, ko tana saka mutane cikin tsananin ciwo fiye da sauran nau'ukan, ko kuma idan kariya daga ruwan rigakafi zai kasancewa kasa da yadda ake tsammani.
Amma a kan takarda akwai alamar damuwa, kuma don haka ne gwamnatoci ke daukar matakai cikin gaggawa, ko da zai kasance labari marar dadi.
Wadannene alamomin kamuwa da kwayar cutar Omicron?
Yanzu haka a Afirka ta Kudu mutane da dama da suka kamu da cutar matasa ne kuma alamun kamuwa da cutar ba su yi tsanani ba.
Akwai wasu shawarwari cewa sabon nau'in kwayar cutar ka iya haddasa alamu kadan daban da na Delta - da suka hada da ciwon jiki da gabobi, da kuma rashin jin dandano da kamshi ko wari - amma ya yi wuri a tabbatar da hakan.
A halin da ake ciki yanzu, Kungiyar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa babu wata shaidar da ta nuna cewa kwayar cutar ta Omicron na da banbanci da sauran nau'ukan kwayar cutar korona.
Hakan na nufin tari, da zazzabi da rashin jin kamshi ko wari, da dandano har yanzu alamu uku ne da suka kamata a duba.
Asibitoci a Afirka ta Kudu na shaida yadda ake samu matasan da suka kamu da alamun kamuwa da kwayar cutar masu zafi - amma da dama ba a yi musu allurar rigakafin korona ba ko kuma an yi musu kashin farko ne kawai.
Hakan ya nuna cewa yin rigakafin sau biyu na da muhimmanci wajen bayar da kariya daga kamuwa daga sabon nau'in kwayar cutar har ma da sauran nau'ukan.










