Amurka ta sake zurfafa bincike kan asalin korona

..

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomin tattara bayanan sirrin Amurka sun bayyana cewa duk da yake ba lallai ne su gano yadda korona ta samo asali ba, amma sun tabbatar da cewa ba a ƙirƙiro cutar bane don cutar da bil adama kamar yadda ake ta raɗe-raɗi.

A wani ƙarin bayani da aka samu kan asalin cutar, ofishin darakta janar na hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ya ce kusan dukkanin hujjojin da aka tattara a halin yanzu ba hujjoji bane gamsassu.

Kamar yadda Shugaban Amurka Joe Biden ya buƙata, wannan wani bincike ne da kuma neman ƙarin bayani wanda hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta yi kan salsala da asalin korona.

Masu bincike da masana sun cimma matsaya kan wasu abubuwa biyu inda tunaninsu da fahimtarsu ta zo ɗaya kan batun cutar, inda a farko duka suka taru suka yi ammanar cewa ko dai cutar ta yaɗu ne daga dabba zuwa bil adama ko kuma ta sulalo ne daƙin gwaji ta yaɗu.

Sai dai dukansu sun kasa cimma matsaya kan ko ta wace hanya ce za a yi wa cewa ta fi yiwuwar zama gaskiyar zance dangane da wannan hasashen biyu.

Masu tattara bayanan sirri sun tsayu ne kan cewa ba wani mahaluƙin da ya zauna a ɗakin gwaje-gwaje ya ƙirƙiro wannan cuta kuma ba daga ƙwayoyin hallita aka samar da ita ba.

Haka a iya bincikensu, sun ce babu wani tabbaci kan zargin da ake yi wa masu bincike a wani daƙin gwaje-gwaje da ke birnin Wuhan na China kan cewa suna da hannu dumu-dumu a wajen yaɗuwar cutar.

Amma jami'an Amurka sun ce akwai yiwuwar su koma su ci gaba da bincike domin samun ƙarin haske kan wasu abubuwan da har yanzu suke cikin duhu musamman idan an sake samun wasu hujjojin.