Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NFHS: Da gaske mata sun fi maza yawa a Indiya?
- Marubuci, Daga Geeta Pandey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
Shin mata sun fi maza yawa a India?
Kididdigar cibiyar kula da iyali ta kasa ta fitar ta nuna cewa yayin da aka samu maza 1,000, to akan samu mata 1,020 a kasar, abin da ke nufin adadin mata ya haura na maza da 20 cikin dubu.
Sai dai kwararru na gargadin a yi taka tsantsan wajen sanar da kididdigar, saboda an yi kidayar ne a kan Indiyawa 630,000 cikin 'yan kasar sama da miliyan 300.
Sannan a tabbatar da an yi cikakken bayani kan adadin mata da mazan, ba kuma za a samu hakan ba har sai an gudanar da kidaya ta kasa baki daya.
"Ita kidaya za ta kirga daukacin 'yan kasar, hakan ne zai ba ta hoton ainihin abin da ake magana a kai," in ji daraktar asusun yawan jama'a na Indiya, Poonam Muttreja, a hirarta da BBC.
Sai dai adadin ya dauki hankali a cikin kasar, inda wasu ke ikirarin an mayar da hankali a kan wani bangare, tare da nuna fifiko ga maza.
Ma'aikatar lafiya ta ce wannan ne karon farko da aka taba bayar da kididdigar mata sun fi maza yawa a duniya. Wani jami'i ya alakanta hakan da matakan da gwamnati ta dauka na bai wa mata aikin yi.
Rahotannin kafafen yada labarai kuwa cewa suke wannan gagarumin ci gaba ne. Wani dan jarida ya rubuta cewa ''Indiya ta shiga kasashe masu ci gaba.''
Sai dai masu fafutuka sun ce adadin bai wani dadasu da kasa ba, sannan sun bayyana ikirarin na gwamnati da ba mai inganci ba.
"Sama da shekara 100, kidayar jama'a da ake yi a kasarmu ana nuna maza sun fi mata yawa a Indiya," in ji mai bincike kuma dan fafutuka Sabu George.
"Kamar yadda kidayar shekarar 2011 ta nuna, ana samun mata 940, yayin da ake da maza 1,000."
An dade ana kiran Indiya da sunan "kasar da mata ke bata" - kalmar da aka fara amfani da ita ga wanda ya zo na daya a gasar Nobel kan tattalin arziki Amartya Sen a shekarar 1990, lokacin da mata suka yi karanci fiye da maza. A lokacin ya nuna sama da mata miliyan 37 ne ba a san inda suke ba a kasar.
Son haifar da namiji a Indiya tsohuwar al'ada ce da aka dade ana amfani da ita, da kuma aka yi amanna da cewa da namiji shi ne ke gadon gidansu da kula da iyayensa a lokacin da girma ya hau kansu, yayin da 'ya'ya mata ke janyo wa iyayensu kashe kudi ta hanyar biyan sadaki, tare da komawa ga dangin mijin da suka aura.
Masu fafutuka na cewa dabi'ar nuna wariya ga mata, da kididdigar shekarar 1970, da miliyoyin cikin da mata suka din ga zubarwa saboda samun bayanin za su haifi 'ya'ya mata, ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan matan a Indiya.
A shekarar 1994 binciken kimiyya da ke nuna abin da mai ciki za ta haifa, ya nuna yadda aka samu karuwar zubda ciki, a kuma shekarar 2002 majalisa ta gabatar da kudurin dokar da ya hana yin binciken. Sai dai masu fafutuka na cewa har yanzu ana aikata hakan.
Masu sa ido kan yawan al'umma, sun ce inda ba a nunawa mata wariya da za a samu mata 952 ga mazaje 1,000 maimakon 929 da kididdigar ta nuna a baya-bayan nan. Mista George ya ce hakan na nufin akwai rarar mata 23 wato kashi 2 kenan tsakanin kididdigar ta yanzu da ta baya.
"Ta nuna har yanzu ana kashe miliyoyin 'ya'ya mata," in ji shi. "Idan an samu haihuwa miliyan 26 a Indiya a kowacce shekara, ya nuna an samu karuwar haihuwa sama da miliyan 130 shekaru biyar da suka wuce. Wannan abin kunya ne ga kasa, babu wani abin murna akai."
A baya, gwamnati ta amince matakan da ta dauka na rage zubar da dan tayin mata bai yi tasiri ba.
Tsohon Fira Ministan Indiya Manmohan Singh, ya bayyana matakin da abin kunya ga daukacin kasar da nuna tsabar rashin imani, tare da kiran daukar kwakkwaran mataki domin ceto 'ya'ya mata a Indiya. Jim kadan bayan nan a shekarar 2014, Fira Minsta Narendra Modi, ya roki Indiyawa su daina kashe 'ya'yansu mata. Shekara guda bayan nan, aka kaddamar da wani shiri da ke kira ga iyaye su kubutar da 'ya'yansu mata ta hanyar ilimantar da su.
Amma duk da matakin, sauyin da aka samu bai taka kara ya karya ba.
A shekarun bayan, mun kawo rahoton an tsinci wata jaririya sabuwar haihuwa da aka yasar a gefen titi, wata kuma an binne ta, wata kuma gefen rafi, da kusa da kwatami. Haka kuma rahotanni sun bayyana yadda ake samun karuwar asibitocin da ke tantance abin da mace za ta haifa tun jaririn ya na dan tayi.
"Ina ganin bincike ba shi da sahihanci. Babu ta yadda za a yi hakan ta faru. Ina tunanin kidaddigar kidayar, ko ma daga inda ta fito, ba ta nuna wani ci gaban da aka samu ba ta wannan fannin. Hasali ma zan yi mamaki idan aka ce abin bai kara raguwa ba,'' in ji shi.