Fitattun malamai 27 'yan wasu kasashen da Saudiyya ta ba shaidar zama ƴan kasar

saudi citizens

Asalin hoton, Alarabiya

A cikin watan Nuwamban 2021 ne wani abin da ba a saba gani ba Saudiyya ta ba wasu mutum 27 shaida zama ƴan ƙasar saboda gudunmuwar da suka bayar a fannoni da daban-daban.

Mutanen da aka ba sun ƙunshi fitattun mutane a fagen ilimi da kiwon lafiya da kuma harkokin addini, kamar yadda jaridar Arab news ta ruwaito.

Wannan na daga cikin sabbin manufofin Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman ƙarƙashin shirinsa na Vision 2030.

Kafar talabijin ta Al-Arabiya ta wallafa sunayen jerin mutanen da suka zama ƴan ƙasar Saudiyya, cikinsu har da malamin shi'a ɗan ƙasar Lebanon Mohammed al Hussien mai sassaucin ra'ayi.

Ga dai jerin sunayen malaman da bayanai a kansu kamar yadda kafar yada labaran intanet ta Alarabiya ta wallafa:

Radwan Nayef al-Sayed

Radwan al-Sayed ɗan Labanon ne kuma marubuci, sannan tsohon babban edita na mujallar al-Ijtihad ta mako-mako.

Shi ne babban jami'in kula da dakin tara bayanai na Makkah al-Mukarramah, kuma ya yi karatun digirinsa a Tsangayar Ilimin Addinai a Jami'ar al-Azhar da kuma digirin-digirgir a Jami'ar Tübingen ta Jamus.

Mustafa Ceric

Mustafa Ceric fitaccen malami ne ɗan asalin kasar Bosnia ne.

Ya taɓa riƙe muƙamin babban alkalin Bosnia da Herzegovina daga shekarar 1999 zuwa 2012, inda ya dinga assasa fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai da kuma shiga da addinin Musulunci cikin al'ummomin Turai.

Ceric ya yi karatunsa a Jami'ar al-Azhar a Alkahira sannan ya yi digirin-digirgir a Jami;ar Chicago a Amurka.

Hussein Daoudi

Daoudi shi ne shugaban Kwamitin Dangantaka na Scandinavia kuma mamba ne a kwamitin koliu ta kungiyar Musulmai ta Duniya.

Ya sha sukar tsattsauran ra'ayi a bayyane da kuma yaɗa aƙidar fahimtar juna a tsakanin addinai.

Malamin yana daya daga cikin fitattun mutanen da suka sanya kannu kan bayanan Makkah al-Mukarramah na 2020 da aka ƙaddamar don yaƙi da tsattsauran ra'ayi a tsakanin Musulmai.

Bayanai sun ce Daoudi ɗan Sweden ne.

Mohammed Nimr al-Sammak

Al-Sammak na daya daga cikin fitattun Larabawa masu tsinkaye a fanninsa.

Ya riƙe muƙamin Sakatare Janar na Kwamitin Sasantawa na Musulunci da Kiristanci, kuma mamba ne na kwamitin koli ta kungiyar Musulmai ta duniya.

Shi ma yana da cikin manyan jami'an kwamitin tattara bayanai na Makkah al-Mukarramah.

Abdullah Saleh Abdullah

Abdullah fitaccen masanin tarihi ne a Iraki wanda ya wallafa ayyuka da dama kan Saudiyya da ma sauran kasashen Larabawa na yankin Gulf.

Mohammed al-Husseini

A matsayinsa na Sakatare Janar na KWamitin Musulmai Larabawa na Labanon, al-Husseini ya kasance mai assasa sassaucin ra'ayin Musulunci.

Mohammed al-Husseini Malamin Shia ne da aka san shi da kokarin dakile siyasantar da Musulunci.

Emad Mohamed Teljeh

Teljeh ƙwararre ne kan cututtuka masu yaɗuwa da ya wallafa bincike fiye da 87.

Ya samu karramawa da dama a fannin lafiya kuma an ba shi shaidar ƙwarewa a Birtaniya da Amurka.

Farouk Owaida

Owaida ya yi aiki a matsayin shugaban sashen tiyatar zuciya a asibitin Saud al-Babtain a Dammam tun shekarar 2004.

Ya yi tiyatar zuciya fiye da 5,000 sannan ya wallafa fiye da bincike 20.

Emad el-Din Najeh Ezzat Kanaan

Kanaan fitaccen mai tiyatar ƙwaƙwalwa ne da yake shugabantar sashen ƙwaƙwalwa na Asibitin King Faisal.

Mamba ne shi a hukumar likitocin kwakwalwa ta Jamus kuma darakta a sashen ƙwaƙwalwa a Jami'ar Al-Faisal University.

Khaled Hamwi

Hamwi ƙwararren likita ne a sashen dashen bangarorin jiki, kuma ya yi aiki a asibitin kwararru na King Faisal.

Ya yi aiki a matsayin babban darakta na dashen matsarmama a Asibitin Mayo da ke Amurka daga shekarar 2008 zuwa 2012.

Hamwi ya kuma wallafa littattafai da dama kan wannan batun.

Muhammad Ghayath Jamil

Jamil ma ƙwararre ne a fannin lafiya kuma shi ne shugaban sashen lafiya na tafi da gidanka a asibitin kwararru na King Faisal.

Walid Khaled Rashid

Rashid bababn likitan jini ne da dashen bargo a asibitin kwararru na King Faisal.

Mustafa Abdullah Saleh

Saleh ƙwararre ne a fannin lafiyar yara kuma ya wallafa maƙaloli na bincike fiye da 235.

Ansir Marah

Marah Farfesa ne a fannin man fetur da ma'adinai a Jami'ar King Fahd.

Ya taba sa ido a kan wani bincike tsakanin jami'arsa da Cibiyar Fasaha ta Massachusetts a Amurka da aka samar da makaloli fiye da 90.

Muhammad Abdulaziz Mustafa Habib

Shi ma farfesa ne a Jami'ar King Fahd , ya kuma wallafa makaloli fiye da 90.

Bikar Yilbas

Yalbas farfesa ne a na man fetur da ma'adinai a Jami'ar King Fahd.

Mohammed Abdel Karim Antar

Shi ma farfesa ne kuma ƙwararre a kan man fetur da ma'adinai a Jami'ar Fahd.

Ya wallafa makaloli na bincike fiye da 70.

Tawfiq Abdo Saleh Awad

Awad farfesa ne kan ilimin hada sinadarai a Jami'ar King Fahd.

Ya wallafa makaloli na bincike fiye da 340.

Ali Hussein Mogabeel

Mogabeel farfesa ne a Jami'ar King Fahd inda ya kware a fannin fasahar sadarwa.

Ya wallafa makaloli fiye da 40 na bincike.

Ezz El-Din Zerkin

Zerkin farfesa ne a Jami'ar King Fahd wanda ya ƙware a fannin fasahar sadarwa da basirar na'ura.

Ya wallafa fiye da makaloli 80 na bincike.

Samir Maked

Maked farfesa ne a Jami'ar King Fahd wanda ya ƙware a samar da abubuwa. Ya wallafa fiye da makaloli na bincike fiye da 70.

Ayman Helmy Salt

Salt farfesa ne a Jami'ar King Fahd inda ya ƙware a fannin komfuta.

Ya wallafa fiye da makaloli 40 na bincike.

Bassam al-Ali

Al-Ali farfesa ne a Jami'ar King Fahd da ya kware a fannin harhada sinadarai.

Ya wallafa fiye da makaloli na bincike 90.

Hadi Mohammed Aqoun

Aqoun injiniya ne da ya yi aiki a matsayin farfesa a jami'oi daban-daban a Amurka.

Ya taba karbar lambar yabo ta kamfanin Boeing, kuma ya taba karbar lambar yabo ta farfesa na shekara.

Yana daga cikin injiniyoyi da dama da suka yi wa kamfanin na ƙera jiragen sama aiki.

Salah al-Din Mahmoud Ahmed al-Katatni

Al-Katatni farfesa ne a Jami'ar King Fahd da ya ƙware a fannin man fetur - musamman kan rijoyoyin mai da haƙarsa.

Ya wallafa fiye da makaloli 77 na bincike.

Mohamed Ahmed Nasr el-Din Mahmoud

Mahmoud farfesa ne a Jami'ar King Fahd da ya ƙware a fannin man fetur.

Ya wallafa fiye da makaloli 130 na bincike.

Musa Qari Syed

An haifi Syed a Saudiyya ya kuma samu ƙwarewa da dama a Amurka a makarantu daban-daban har zuwa matakin digirin-digirgir.

Ya kuma taba zama shugaban kwalejin lafiya ta Jami'ar California a Los Angeles.