Saliyo: 'Yadda na tsira a gobarar tankar mai amma kuma rayuwata ta tarwatse'

Iyalai da dangin mutanen da hatsarin gobarar tankar mai ya hallaka a Saliyo suna cikin kakabin yadda za su sake gina rayuwarsu bayan mummunan lamarin da ya jawo musu dumbin asara, kamar yadda wakiliyar BBC a Afirka ta Yamma Mayeni Jones ta ruwaito.
Da tsakar rana, jami'an lafiya cikin shiga ta kariya suke ta naɗe akwatunan gawa da tutar Saliyo. A jikin tutocin an rubuta "Allah Ya jiƙan ku."
Mutane sun taru suna kallonsu yayin da suke aikin ɗibar gawarwakin daga Asibitin Connaught da ke Freetown zuwa maƙabarta.
Wasu daga cikin ma'aikatan sun toshe hancinsu. Ana iya jin warin gawarwakin ya gauraye iskar da ake shaƙa.
Cikin waɗanda suka taru suna kallon yadda ake ɗibar gawarwakin, akwai wata mata da ɗan ɗan uwanta ya samu munanan ƙuna a hatsarin inda ta fashe da kuka.
"Wayyo Allahna, wayyo Allah!" ta yi ta maimaitawa, tana riƙe da hankici. tana goge fuskarta, jikinta na rawa kamar mazari saboda kaɗuwa.
Kama daga yakin basasa, da annobar Ebola ta 2014 da wasu bala'o'i masu kama da haka, 'yan Saliyo sun shiga ukubobi iri-iri.
Saliyo ce ta 182 daga cikin jerin kasashe 189 da Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai karancin cigaban al'umma ta fannin walwala da tattalin arziki, da kuma abin da ya shafi shekarun mutuwa da neman ilimi da kuma samun kudi.
Duk da cewa tana da arzikin ma'adanai shimfide, Saliyo na daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, kuma sai ga wannan bala'i ya fada mata.
"A tsawon rayuwata ta aikin likita, ban taba ganin bala'i irin wannan ba," in ji Dr Mustapha Kabbah, wani likita da ke asibitin Connaught, wanda kuma ke da kwarewar shekara 20 yana aiki.
Ya koma Saliyo ne daga Jamus tare da iyalinsa a shekarar 2018.
"Wannan babban abu ne. A ranar da naga abun nan na yi matukar kaduwa. Har yanzu ba mu iya gama fahimtar abin da ya faru ba."
'Mun gode Allah da ya tseratar da dan uwana'
A kan dakalin dakunan asibitin na yi magana da Victoria Fornah mai shekara 25, wadda daliba ce a kwalejin Fourah Bay da aka samar kusan shekara 200 da suka wuce.
Yayanta Ibrahim na cikin wadanda gobarar ta rutsa da su, a lokacin da yake dawowa gida ranar Juma'a da daddare.
Ta kafar intanet ta san cewa yana cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.
" Ina bacci 'yar uwata ta kirani ta ce min 'duba wayarki'. Ina budewa sai naga hoton yayana kwance a kasa duk wuta ta kona jikinshi."
Ibrahim ya kone a hannunsa da fuskarsa da kafafunsa. Amma Victoria ta ce yana samun sauki, "duk da raunukan da ya samu suna da yawa, mun gode wa Allah ya rayu."
A wurin da bala'in ya faru a Wellington da ke gabashin Freetown, ana jiyo kauri sama da awa 48 da faruwar lamarin.
Mazauna yankin da masu sana'o'i sun fara lissafin irin asarar da suka tafka.
Da dama sun kundume dukkan abin da suka mallaka don fara sana'a, ga shi kuma sun rasa komai a wannan gobara.
'Mun rasa komai- kudinmu duka ya kone'
Aisatu Sesay marainiya ce mai shekara 28 da ke karatu a wani karamin asibiti.
Ta bude wani karamin dakin shan magani ita da 'yar uwarta don samun karin kudi.
A watan Yuli sun rasa gidansu a wata gobara da wutar lantarki ta haddasa.
Sun zuba duk abin da suke da shi da tallafin da suka samu ga dakin shan maganin da suka bude. Yanzu ga shi sun rasa komai.
"Komai ya tafi, takarduna da na dakin maganin duk sun kone. Ban san ma me zan yi ba," in ji Ms Sesay.

Ta dawo daga aiki ne a lokacin da lamarin ya faru. Kuma a lokacin da ta yi yunkurin guduwa daga wutar mutane da ke gudu sun ture ta har sai da ta ji rauni.
" Da dama sun mutu ne saboda sun fadi kasa an tattaka su saboda ba za su iya tashi ba."
A yanzu ta damu da yadda rayuwa za ta kasance mata nan gaba.
A yanzu duka yan gidansu za su koma gidan marayu da zama a inda ta girma, don ba su da inda za su je.
" Abu ne mai matukar wahala mu iya bude wata sana'a yanzu saboda ba mu da isasshen kudi, amma a hankali za mu samu jari."
" Yayin jana'izar mamatan a ranar Litinin da daddare, Shugaba Julius Maada Bio ya jaddada alkawarin cewa za a binciki yadda lamarin ya faru don kauce wa sake faruwar irin haka a nan gaba.
To amma ga wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu, yadda rayuwa za ta kasance bayan wannan bala'i suke tunani kafin a yi maganar alkawarin kauce wa sake faruwar wani.













