Badaƙalar Pandora: Yadda asirin Sarkin Jordan ya tonu na ɓoye kadarorin fan miliyan 70

King of Jordan
    • Marubuci, Daga tawagar da ke bibiyar labaran bakadaƙalar Pandora
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Panorama

A asirce Sarkin Jordan ya kashe sama da fam miliyan 70 (dala miliyan100) wajen mallakar wasu gidaje a Birtaniya da Amurka.

Wasu takardun sirri da aka fitar da su a asirce sun nuna yadda sarki Abdullah II bin Al-Hussein ya yi amfani da wasu kamfanoni na sirri ya sayi gidaje 15 tun bayan da ya hu mulki a 1999.

Gidajen sun hada da wasu da ya mallaka a Malibu da London da Ascot a Birtaniya.

Lauyoyin Sarkin sun ce ya yi amafani da dukiyarsa ne ta kashin-kansa ya sayi gidajen, a don haka babu wani abu da ya yi na saba wa doka don ya yi amfani da kamfanonin waje wurin sayen.

Jordan na samun tallafi sosai daga kasashen duniya da suka hada da Amurka da Birtaniya. Kuma gwamnatin Birtaniya na daga cikin wadanda suka fi ba Jordan taimakon kudi, inda ta ninka yawan kudin da take ba ta zuwa fam miliyan 650 a cikin shekara biyar a 2019.

Haka kuma ana daukar Sarki Abdullah a matsayin abokin kasashen Yammacin Duniya mai tsaka-tsakin ra'ayi a Gabas ta Tsakiya.

Sai dai yawan dukiyarsa ta gidje na ta karuwa daga tsakanin 2003 da 2017 yyin da ake zarginsa da jagorantr gwamnatin kama-karya a gida, inda har aka rika yin zanga-zanga a ƴan shekarun nan a lokacin da ake fama da matakan tsuke bakin aljihu da kara haraji.

Hukumomin kasar ta Jordan sun kadamar da wani shiri na a watan Yuni na 2020 kan kudin da ƴan kasar ke aikawa waje.

An ruwaito wani daga cikin masu sukar gwamnatin kasar yana cewa kusan Sarki Abdullah yana gudanar da mulkin kasar ne ta hanyar amfani da na'ura daga nesa - wani tsohon jami'in gwamnatin kasar ma ya bayyana wa Panorama cewa Sarkin yana yin kusan wata hudu zuwa shida a shekara a waje.

Wane ne Sarkin Jordan?

King and Queen of Jordan in 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, King Abdullah has been married to Queen Rania since 1993
  • An haife shi ranar 30 ga Janairu 1962, shi ne babban dan Sarki Hussein kuma matarsa Gimbiya Muna Al Hussein, haihuwar Birtaniya ce
  • Ya yi makaranta a Birtaniya inda ya halarci makarantar koyon aikin soji ta Royal Military Academy Sandhurst, da Amurka,
  • Ya yi aiki a rundunar sojin kasa ta Birtaniya da kuma ta kasar Jordan
  • Ya auri Sarauniya Rania a 1993
  • Ya goyi bayan shirin soji na kasashen ammacin Duniya na bayan hare-haren 11 ga Satumba
  • Ya aiwatar da shirye-shiryen zamanantar da harkokin tattalin arziki da zamantakewa a Jordan, amma kuma ya fuskanci suka kan tattalin arziki, inda matakan tsuke bakin aljihu da kara haraji suka jawo zanga-zanga a 2018
line

Bayanan mallakar gidajen na arkin na Jordan da aka tono suna kunshe ne a wasu sabbin takardu da aka samu wadanda aka yi wa lakabi da Pandora Papers.

Sun bayyana dalla-dalla ayyukan wasu kamfanoni da ke gudanar da harkokin kudi cikin sirri, da kuma tarin dukiyar boye ta wasu manyan mutane na kasashen duniya.

Shirin BBC Panorama da jaridar Guardian ta Birtaniya sun yi aiki tare da wasu kafofin yada labarai da suke hadin gwiwaa suka samu takardu sama da miliyn 12 daga kamfanoni 14 a British Virgin Islands da Belize da Panama da Hong Kong da Cyprus da Switzerland da wasu kasashen.

Haka kuma Sarki Abdullah ya sayi wasu gidaje a Georgetown, inda wani bangare ne na birnin Washington DC, da ke da tsada sosai tsakanin 2012 da 2014.

Zai iya kasancewa gidajen da ya saya na dala miliyan 16 na da alaka da dansa Yarima mai jiran gado, Hussein, wanda ke halartar Jami'ar Georgetown a lokacin.

'Wani ya yi fama da gaske wajen boye sawunsu'

Properties bought by the King of Jordan in Malibu

Wannan wani katafaren gida ne mai dakin kwana bakwai da ke cikin wasu gidaje masu tsadar gaske wadanda ke kan wani tsauni da ke kallon tekun Pacific a Point Dume da ke Malibu, a California.

Sir Anthony Hopkins da Julia Roberts da Simon Cowell da Gwyneth Paltrow da Barbra Streisand dukkanninsu sun zauna a yankin.

An sayi gidan ne a kan dala miliyan 33 da rabi a 2014 ta hanyar amfani da kamfanin Nabisco Holdings SA, wanda kamfani ne a British Virgin Islands (BVI) - a lokacin ba gidan da aka taba saya da ya kai shi tsada.

Kamfanoni biyu daban-daban na British Virgin Islands suka sayi gidajen, bangare-bangare a 2015 da 2017, inda jumullar kudin ta kai fam miliyan 68 - sai aka hade dukkanin ukun suka zama gida daya babba.

Takardun na Pandora sun bayyana cewa dukkanin kamfanonin uku na daga wadanda suka wakilci kamfanin lauyoyi na Panama, kuma sarkin na Jordan ne ya mallake su a boye.

Wani mai yad labarai ta intanet wanda ba ya bayyana sunansa, wanda kuma yake rubutu a kan saye da sayar da gidajen fitattun mutane a California a lokacin ya rubuta cewa: "Wani ya sha matukar wahala sosai wajen gano sawunsu a nan. Kwarai, hamshakn attajirai yawanci ba sa so a gane su. Amma wannan cinikin na boye abu ne da ba mu taba gani ba."

'Ka san waye'

Sarkin Jordan ya iya boye gidajen da ya mallaka ne saboda ya yi amfani da kamfanonin kasashen waje wurin cinikin.

Mutanen da suka hada wa Sarkin kamfanonin sun yi da gaske wajen boye Sarkin, inda suka bayyana shi wata takarda ta maganar cikikin ta tsakaninsu a matsayin " Ka san waye".

Akwai kuma bayanai da ke nuna cewa duk wani kokari na tabbatar da gaskiya da baje abu a faifai kan harkokin kudade ka iya gamuwa da matsaloli ko wahala.

Gwamnatin British Virgin Islands ta aiwatar da wata doka 2017, inda ta tilasta wa dukkanin masu kamfanoni a tsiburan su bayyana wadanda suka mallake su a wata rijista da ke hannun gwamnati.

To amma har bayan wata takwas da fara aiwatar da wannan doka wasu kamfanonin da ke da alaka da Sarki Abdullah ba su mika bayanansu ba ga hukumomin.

Haka kuma kusan ba a bayyana Sarkin a matsayin wani babban mutum da ke da wani muhimman matsayi ba, wanda hakan wani sharadi ne a kan kamfanoni kan dokokin yaki da cin hanci da rashawa.

Annelle Sheline, mai fashin baki a Gabas ta Tsakiya ta nuna cewa labarin zai iya yin tasiri a Jordan.

Ta gaya wa Panorama: "Abu ne mai matukar wahala ga yawancin ƴan Jordan su iya rayuwa ta baina-baina, da kuma samun aiki mai kyau. Ta bayyana cewa sarkinsu yana zurare wasu makudan kudade zuwa waje a wannan lokacin? To lalle wannan abu ne da zai yi muni matuka."

Lauyoyin Sarki Abdullah sun ce bayanan gidajen nasa ba cikakku ba ne.

Sun ce an sayi dukkanin gidajensa na waje ne da dukiyarsa ta kashin-kansa, wadda kuma yake amfani da dukiyar wajen bayar da kudaden gudanar da ayyuka ga ƴan kasar ta Jordan.

Suka kara da cewa ba wai an yi amfani dagidajen na waje ba ne wajen boye dukiyar Sarkin, kuma abu ne daman da fitattun manyan mutane da kamfanoni su mallaki kadarori ta hanyar irin wadanan kamfanoni na waje domin dalilai na sirri da kuma tsaro

Suka ce kwararru ne suke tafiyar da harkokin kadarorin domin tbbatar da ana tafiyar da su yadda ya kamata bisa dokokin da suka shafe su".

A ina kadarorin ɓoye na sarkin suke?

Ba kawai a Malibu, ba ne sarkin ya sayi gidaje a asirce. Akwai takwas a London da kudu maso gabashin Ingila kamar yada takardun na sirri na Pandora da aka tono suka nuna.

Sun hada da gidaje shida a wasu tituna masu tsada na birnin London a Kensington da Belgravia.

Akwai kuma wasu biyu a Ascot da Surrey. Haka kuma ya sayi gidaje hudu a Georgetown, Washington DC.

Pandora Papers banner

Takardun na Pandora da aka fitar da su ta sirri sun kunshi takardu da fayil-fayil kusan miliyan 12 da ke tona dukiya da kadarori na boye na shugabannin duniya, da ƴan siyasa da attajirai.

Wata gamayyar 'yan jaridar duniya masu binciken kwakwaf ne a Washington DC ta samu bayanan, inda kuma ta jagoranci daya daga cikin manyan binciken kwakwaf na duniya

Sama da ƴan jarida 600 daga kasashe 117 suka duba takardun na kadarorin boye na wasu daga cikin manyan mutane mafiya karfin fadi a ji a duniya.

BBC Panorama da jaridar Guardian ne suka jagoranci binciken a Birtaniya.