Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan abubuwa biyar da suke durkusar da darajar naira
Masana harkokin tattalin arziki a Najeriya sun bayyana cewa muddin kasar ba za ta yi kokarin shawo kan manyan matsalolin da ke haifar da faduwar darajar naira ba, za a ci gaba da fuskantar matsin tattalin arzikin da ya wuce wanda aka fuskanta a baya.
Faduwar darajar nairar musamman a kan dalar Amurka wacce aka fi amfani da ita wajen kasuwancin kasa da kasa a duniya na kara jefa 'yan Najeriyar cikin matsanacin hauhawar farashin kayayyaki a kasuwannin cikin gida.
A karshen watan Agustan shekarar 2021 ma darajar nairar ta yi sabuwar faduwar da ta dade ba ta yi ba, inda darajarta ta yi kasa da 527 a kan dalar a kasuwar bayan fage, kwanaki kadan bayan Babban Bankin ya hana kananan 'yan kasuwa yin hada-hadar canjin kudaden waje a kasar.
Babban Bankin ya haramta sayar da dala ga 'yan kasuwar canjin saboda zarginsu da bin hanyoyi na halatta kudin haram.
BBC tattauna da Dakta Mohammed Shamsuddeen wani masanin tattalin arziki a Najeriya game da abubuwan da ke saka darajar naira yawan faduwa, inda ya fara da bayyana cewa akwai abubuwa da dama da ya kamata a duba wadanda muddin ba a magance su ba za a ci gaba da fama da wannan matsala.
1. Dogaro da man fetur
Dakta Shamsuddeen ya bayyana cewa dogaro da man fetur da kasar ta dade tana yi ya kara sa darajar naira faduwa musamman idan aka danganta da dalar Amurka.
Masanin ya kuma ce ko shakka babu man fetur shi ne babbar hanyar da Najeriya ke samun kudaden shiga na kasar waje, don haka a duk lokacin da kasuwar man fetur ta yi kasa a duniya hakan na nufin Najeriya ba za ta samu kudaden kasashen waje ba kenan da za ta bayar a cikin kasa.
"Wannan tabbas zai janyo darajar naira ta fadi, domin za ka ga cewa akwai nairar da yawa a kasuwa yayin da ita kuma dalar ta yi karanci don haka sai ta yi tsada kenan a kasuwa."
"Muddin ba fadada hanyoyin samun kudaden shiga daga kasashen waje Najeriyar ta yi ba, za a yi ta fama da irin wannan matsalar a duk lokacin da kasuwar man fetur ta fadi a duniya," in ji Dakta Shamsuddeen.
2. Cin bashi daga kasashen waje
Batun yawan cin bashi daga kasashen waje na daga cikin abubuwan da masanin ya bayyana cewa na kara karya darajar nairar saboda irin sharuddan da ake gindaya wa kasashe ciki har da Najeriyar a duk lokacin da suka ciyo bashin.
"Musamman basussuka daga hukumomi wadanda aka gina su a kan tsari na jari hujja, a duk lokacin da aka ciyo bashi irin wadannan kungiyoyi daya daga cikin sharuddan da suke saka wa misali za su tilasta wa Najeriya ne ta rage darajar naira a gwamnatance ko kuma a yi kokarin hade farashin nairar a kasuwa da kuma a hukumance," ya ce.
Ya kara da cewa: "Kuma daga baya-bayan nan shi ne kusan babban abin da ya sa babban bankin kasa ya yi ta rage wa naira darajarta."
3. Yawan amfani da kayayyakin kasashen waje
Har ila yau wani batu da masanin ya fito da shi game da abubuwan da ke sa darajar naira ta karye shi ne dabi'ar yawan son amfani da kayyakin kasashen waje a tsakanin 'yan Najeriyar da su kansu mahukuntan kasar.
"Ya zama dabi'ar 'yan Najeriya da su kansu mahukuntan kasar a ko da yaushe sun fi kaunar sayen kayayyakin da aka sarfafawa a kasashen waje ko da kuwa ana yin irin sa a cikin gida ya zama kamar wani abu na yayi ko wayewa," Dakta Shamsuddeen ya bayyana.
Ya kuma ce haka ma ko a bangaren lafiya da ilimi ne sai ka ga mutum ba zai kai 'ya'yansa ko kuma shi kansa makarantu ko asibitocin da ake da su a cikin kasa ba idan yana da hali, komai kyawunsa kuwa.
"Za ka ga idan lalura ta samu sai dai a nemi kudaden waje a tafi wata kasar, haka ita ma gwamnati wajen bayar da kwangiloli ko sayen kayayyaki yawanci ta fi dogara da na kasashen waje, kamar ba ta yarda da kamfanoni da masana'antun kasar ba," in ji masanin.
Duk wadannan a cewar masanin, idan aka hada gaba daya da bukatu na yau da kullum na 'yan kasa ya zama cewar an dogara kusan kacokan da shigo da kayayyaki daga kasashen waje - ya sa bukatar kudin kasar wajen ta yi yawa kuma a duk lokacin da suka yi karanci dole su yi tsada wanda aka ke nufin dole darajar naira ta karye.
4. Magudin 'yan kasuwar canjin kudaden kasar waje
Ta wani gefen kuma 'yan kasuwar bayan fage ko kuma 'yan canji a cewar Dakta Shamsuddeen su ma suna da tasu gudumawar wajen karya darajar naira, inda su kan rika yin magudi wajen sayar da dalolin, duk kuwa da cewa a lokuta da dama su kan samu dalar ne da sauki daga gwamnati.
"Su kan rika boye ta su tura ta wata hanya da ba ta kamata ba, don kawai ta yi tsada su ci riba mai yawa ko su boye ta su haddasa karancinta da gangan.
"Saboda idan ta yi karanci dole farashinta zai tashi, kenan darajar naira ita kuma ta sake faduwa," ya ce.
5. Cin hanci da rashawa
Matsalar cin hanci da rashawa da ta yi katutu a Najeriya wanda masanin ya ce za ka ga jami'an gwamnati da masu hannu da shuni na yin kyauta da dala a cikin kasa, ko idan suna bikin 'yayansu, suna lika wa 'ya'yan nasu, da 'yan uwansu, da abokansu dalolin ko kuma wasu kudaden kasar waje.
"Wannan shi ake kira dolarisation na tattalin arziki - ma'ana ka dauko kudaden da ba na kasarku ba kana kashewa a cikin kasarku saboda ka nuna ka isa ko kuma saboda ka raina kudaden kasarku," Dakta Shamsuddeen ya bayyana.
Sannan kuma a cewarsa a duk dai a bangaren cin hanci da rashawa, abubuwan nan da ake bayarwa na kaso na kwangila yawanci kamfanonin da za su bayar da irin wannan kaso ga jami'an gwamnati da suka ba su kwangilar sai sun nemo dala saboda harkar kudi ce da ba za a yi ta asusun ajiyar banki ba.
"Saboda ita naira tun da darajarta ta karye, ba zai yiwu a yi amfani da ita ba saboda yawan da za ta yi - guda dari na bandir din dalar Amurka ya kai naira miliyan biyar kudin Najeriya," ya ce.
"Don haka wannan cin hanci da rashawa shi ma ya taimaka kwarai da gaske wajen kara yawan dalolin da ake bukata a cikin kasa, kana shugabannin siyasa sun fi 'yan kasuwa ajiyar dala a gidajensu da sauran wuraren da suke boye kudaden kasar waje."
Masanin ya kuma bayyana cewa muddin ana son a nemi mafita game da wannan matsala lallai sai an yi gyara ga al'amarin in ba haka ba za a yi ta fama.