Afghanistan: Ina duka 'yan gudun hijira za su tafi bayan Taliban ta karbe iko?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, The Visual Journalism Team
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Dubban mutane ne ke ta fadi tashin ganin sun tsere daga Afghanistan bayan da Taliban ta karbe iko da kasar, kimanin shekara 20 bayan da sojojin kawancen da Amurka ke jagoranta ya hanbarar da mulkinsu.
Adadin mutanen da ke yunkurin guduwar na zuwa ne daidai lokacin da mutum miliyan 2.2 suke gudun hijira a kasashen dake makwabtaka, miliyan 3.5 kuma suka rasa gidajensu suka kuma makale a kan iyakar kasar sakamakon rikicin siyasar da ya firgita kasar.
'Yan Afghanistan nawa ne ke guduwa?
A yanzu dai, babu takamaimai adadin mutanen.
Taliban sun karbe iko da duka iyakokin kasa na Afghanistan da kasashen da suke makwabta da su, kuma mayakan sun ce ba sa son 'yan kasar su fice zuwa makwabta. Rahotanni na cewa 'yan kasuwa ne kawai da wadanda ke da shaidar tafiya ake bari su tsallaka.
"Mafi yawan 'yan Afghanistan ba a barin su bar kasar ta hanyoyin da aka saba," kamar yadda kakakin shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ya bayyana a ranar Juma'a. "Ya zuwa yanzu mutanen da suka fi zama cikin hadari ba su da hanyar barin kasar nan."
Amma wasu da yawa na ta kokarin ficewa daga kasar ta hanyoyi daban-daban.
Da dama daga cikin in kasar sun haure zuwa Pakistan jim kadan bayan da Taliban ta karbe iko, yayin da ake bayar da rahoton sama da 1,500 na daban sun tsallaka zuwa Uzbekistan kuma duka suna zaune a tantunan da aka kafa kusa da kan iyaka.
A Kabul, dubban mutane ne suke ta nufar filin jirgin kasar, kuma shi kadai ne ke aiki a fadin kasar baki daya, a wani yunkuri da ake yi na neman ficewa daga kasar.
Mutum nawa ne suka tsere daga gidajensu?
Wannan abin da ke faruwa a Afghanistan wani bangare ne na mummunan tarihin da kasar ta yi ta fama da shi sama da shekaru.
Tun gabanin Taliban ta kara kwace iko, sama da mutum 550,000 rikici ya tilastawa barin muhallansu a wannan shekarar in ji UNHCR.
Wanda hakan yana nufin a hasashen da aka yi akwai 'yan Afghanistan kimanin miliyan 3.5 da suke gudun hijira a cikin kasar.
A wannan shekarar, kasar ta yi fama da matsanancin fari da karancin abinci a mafi yawan sassanta. Wani rahoto da shirin abinci na MDD ya fitar a watan Yunin da ya gabata ya ce mutum miliyan 14 na fama da matsananciyar yunwa, kwatankwacin sama da kashi uku cikin na mutanen kasar kenan.
Ina 'yan gudun hijirar Afghanistan ke tafiya?
A bara kasashen Pakistan da Iran da ke makwabtaka da Afghanistan sun ga tururwar ;yan gudun hijira da masu neman mafaka.
Kimanin milyan 1.5 ne suka shiga Pakistan a 2020, yayin da Iran ta karbi sama da 780,00 in ji UNHCR.
Jamus ce ta uku wadda ta karbi sama da mutum 180,000 ita kuma Turkiyya ta amshi kusan 130,000.
Babu masu neman mafaka a Iran, duka wadanda suke kasar suna da katin shiga Iran, kuma hakan yana basu damar samun tsarinsu na kiwon lafiya da na ilimi.
Me kasashen duniya ke yi domin taimaka wa?
Yayin da wasu kasashe suka yi tayin bai wa 'yan Afghanistan mafaka, wasu kuwa sun yi mirsisi sun nuna ba za su iya ba.
Iran
Iran ta kafa tantuna ga 'yan gudun hijrar a wasu larduna uku daga cikin wadanda suka yi iyaka da Afghanistan. Sai dai wasu manyan jami'an Iran sun ce duk dan Afghanistan din da ya sake ya tsallaka "sharadi guda da ta shimfida za ta mayar da shi inda ya fito". MDD ta ce Iran ta karbi 'yan gudun hijira da suka kai miliyan 3.5 ya zuwa yanzu.
Pakistan
A watan Yuni Firaiministan Pakistan Imran Khan ya ce kasarsa za ta rufe iyakarta da Afghanistan da zarar Taliban sun karbe iko. Amma duk da haka rahotanni sun ce da yawa sun samu tsallakawa Pakistan bayan gano cewa a kwai iyaka daya da take a bude.
Tajikistan
Babu takamaimai yawan mutanen da suka tsallaka Tajikistan, amma dai rahotanni na cewa daruruwan mutane ciki harda sojin Afghanistan sun tsallaka kasar a kwanan nan. A watan Yuli kasar Tajikistan ta ce za ta iya daukar 'yan gudun hijirar Afghanistan 100,000.
Uzbekistan
Kimanin mutum 1,500 ne aka ce sun tsallaka iyakar Uzbekistan da Afghanistan tare da kafa sansani. Rahotanni kuma na cewa Taliban na barin wadanda suke da cikakkiyar biza ne kawai suna tsallakawa.
UK
Tun tuni Burtaniya ta sanar da shirinta na karbar mutum 20,000 daga Afghanistan. Wani shirin gwamnatin Burtaniya zai bar yankasar Afghanistan 'yan Burtaniya 5,000 su zauna a kasar a shekarar farko, kuma za a fi mayar da hankali kan yara da mata da kuma wadanda ake ganin suna cikin barazanar Taliban.
Amurka
Shugaba Joe Biden ya ba da umarnin sakin kudi har dala miliyan 500 saboa "bukatun 'yan gudun hijira na musamman" da ka iya tasowaduba da halin da ake ciki a Afghanistan, ciki har da masu neman bizar 'yan ci rani ta musamman.
Sai dai Amurkan ba ta fadi adadin yawan 'yan gudun hijirar da za ta karba ba.
Canada
Canada ta ce za ta karbi 'yan gudun hijirar Afghanistan 20,000, inda za ta mayar da hankalj kan wadanda ke fuskantar barazanar Taliban, da sula hada da ma'aikatan gwamnati da shugabanni mata.
Australia
Australia ta ce za ta ba da damar daukar mutum 3,000 a shirinta na ba da bizar agaji ga 'yan Afghanistan din da suka tsere daga kasarsu.
Amma ta ce za a ba da bizar ne a oan tsarin da dama ake da shi na jin kai, kuma ba za a kara yawan mutanen da za a bai wa ba.
Tarayyar Turai
Jami'ai daga kasashen Turai da dama sun ce suna taka tsantsan wajen maimaita abin da ya faru a 2015 na tururuwar 'yan gudum hijira, inda shigar 'yan gudun hijira da dama ya jawo musu matsaloli a yankin Turan.
Jamus
Jamus ta nuna alamar cewa za ta karbi wasi 'yan Afghanistan, amma ba ta kayyade yawan ba.
Shugabar gwamnati Angela Merkel, wacce ta sha fama da suka a 2015 saboda bude wa 'yan gudun hijira kofa, ta ce gwamnatinta ta mai da hankali kan tabbatar da cewa 'yan gudun hijirar sun samu wajen zama na rufin asiri a kasashen da ke makwabtaka da Afghanistan.
Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce dole Turai ta kare kanta daga kwararar 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba daga Afghanistan.
Ya ce Faransa za ta kare wadanda ke cikin hadari, amma ya kara da cewa "Turai ba za ta iya daukar dukkan dawainiyar nan da ke tasowa ita kadai ba."
Austria
Austria ta ce ba za ta dauki 'yan gudun hijirar Afghanistan ko daya ba.
Ministam harkokin cikin gida na kasar ya tsaya kan matsayarsa ta ci gaba da mayar da 'yan Afghanistan masu neman mafaka ya kuma nemi a samar da cibiyoyin mayar da mutane a kasashen da ke makwabtaka da Afghanistan, a yanayin da mayar da su can kasar tasu zai yi wahala.
Switzerland
Switzerland ta cr ba za ta karbi 'yan gudun hijira masu yawa da ke tahowa kai tsaye daga Afghanistan ba.
Turkiyya
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki da Pakistan don daidaita al'amura a Afghanistan da kuma hana tururuwar 'yan gudun hijira da ke neman shiga Turkiyya.
Gwamnatin ta kuma fara gina katanga a kan iyakarta da Iran don hana 'yan gudun hijira shiga.
North Macedonia da Albania da kuma Kosovo
Kasashen North Macedonia da Albania sum ce za su karbu 'yan gudun hijira 450 da 300 na wucin gadi bisa bukatar da Amurka ta nuna.
Ana sa ran 'yan gudun hijirar za su zauna a xan har sai an samar musu da bizar Amurka ta 'yan gudun hijira.
Kosovo ma tana shirin samar da matsuguni na wucin gadi ga 'yan gudun hijirar da ke kan hanyar zuwa Amurka amma ba ta fafi yawansu ba.
Uganda
Uganda ta amince ta karbi 'yan gudun hijirar Afghanistan har 2,000.
Kasar waxce takr gabashin Afirka ta fi kowace kasa yawan 'yan gudun hijira a nahiyar - kuma ita ce ta uku a wannan fanni a fadin duniya.yya











