Afghanistan: Shin kasar za ta zama matattarar 'yan ta'adda a karkashin mulkin Taliban?

Taliban forces patrol in Kabul, Afghanistan, August 16, 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Taliban ta sake kwace mulki - shin ungulu za ta koma gidanta na tsamiya?
    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan harkokin tsaro

A yankuna masu cike da tsaunuka na lardin Kunar da ke Afghanistan da kuma zaurukan sada zumunta na masu ikirarin jihadi ana ta yin murna game da abin da magoya bayan al-Qaeda suke kallo a matsayin "wata nasara mai cike da tarihi" da kungiyar Taliban ta samu.

Yadda aka wulakanta dakarun da suka kori Taliban da al-Qaeda na dan wani lokaci shekaru 20 da suka gabata ya zama wani abin karfafa gwiwa ga masu ikirarin jihadi a fadin duniya da ke kyamar kasashen Yamma.

Yanzu an samu yankunan da za su iya zama maboyar kungiyoyin masu ikirarin jihadi, musamman mayakan kungiyar Islamic State (IS) wadda take neman mafakar mayakanta bayan an kawar da su daga wuraren da suka kafa daularsu a Iraqi da Syria.

Janar-janar na sojin kasashen Yamma da 'yan siyasa suna yin gargadi cewa komawar kungiyar al-Qaeda kasar Afghanistan abu ne da "babu makawa" sai ya faru.

Da yake jawabi bayan taron gaggawa, Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya yi gargadin ga kasashen Yamma cewa akwai bukatar su hada gwiwa domin hana Afghanistan komawa matattarar kungiyoyin 'yan ta'addan duniya.

Kuma ranar Litinin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar "ya yi dukkan abin da ya kamata wajen ganin ya dakile barazanar da kungiyoyin 'yan ta'addan duniya ke yi a Afghanistan".

Shin kwace ikon da Taliban ta yi a Afghanistan zai sa kungiyar al-Qaeda ta sake kafa sansanoninta da kuma kaddamar da hare-hare kan kasashen Yamma da sauransu, daga can?

Mai yiwuwa hakan ba zai faru ba.

Neman goyon baya da kuma amincewa

Lokaci na karshe da Taliban ta mulki dukkan kasar shi ne daga shekarar 1996-2001, kuma a wancan lokacin Afghanistan kasa da ba ta da mafadi.

Kasashe uku ne kacal suka amince da ita, wato Saudiyya, Pakistan da Hadadddiyar Daular Larabawa.

Baya ga takurawa 'yan kasarta, kungiyar Taliban ta bayar da mafaka ga kungiyar al-Qaeda ta Osama Bin Laden wadda ta kaddamar da hare-haren 9/11 a Amurka a 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 3,000.

An kiyasta cewa mutum 20,000 daga fadin duniya sun samu horo a sansanonin al-Qaeda, inda suka koyi dabaru da kuma kirkiro abin da ake kira "jami'ar ta'addanci" a yayin da suka barbazu suka koma kasashensu.

Har yanzu 'yan Taliban suna kallona kansu a matsayin wadanda suka cancanci su zama shugabannin kasar da ake kira "the Islamic Emirate of Afghanistan" - duk da yake ba a zabe su a kan wani mukami ba kuma suna so kasashen duniya su amince da su.

Tuni suka nuna cewa sun kwaci mulki ne domin dawo da doka da oda, bayan gwamnatocin cin hanci da barna da kuma fadan cikin gidan da suka rika faruwa cikin shekaru 20 da suka wuce.

Lokacin zaman tattaunawar sulhun da bai yi nasara ba a Doha, an bayyana wa masu shiga tsakanin daga bangaren Taliban cewa ba za a amince da gwamnatinsu ba sai sun yanke hulda da kungiyar al-Qaeda.

Taliban ta ce tuni ta raba kanta da al-Qaeda. Kuma a taron manema labaran da suka gudanar ranar Talata a karon farko bayan kwace mulki, kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid ya ce ba za su bayar da mafaka ga masu ikirarin jihadi ba.

Sai dai wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na baya bayan nan ya nuna cewa ba ta yanke huldar da ke tsakaninsu ba, domin kuwa akwai dangantaka ta kabilanci da auratayya tsakanin kungiyoyin biyu.

Lokacin da Taliban ta kwace ikon kasar a baya bayan nan, an samu rahotanni da dama da suka ga "mayakan kasashen waje" wadanda ba su da alaka da Afghanistan.

Sannan kuma a bayyane yake cewa akwai bambanci tsakanin masu matsakaicin ra'ayi wadanda su ne 'yan gaba-gaba na Taliban- masu shiga tsakani da masu magana da yawun kungiyar - da kuma masu aikata munanan ayyuka wadanda su ne suke kusa da jama'a.

Ranar 12 ga watan Agusta, a yayin da Taliban take ci gaba da mamaye kasar zuwa babban birninta, ofishin jakadancin Amurka da ke Kabul ya wallafa sakon Tuwita da ke cewa: "Sanarwar da Taliban ta fitar a Doha ba ta yi daidai da abubuwan da suke aikatawa a yankunan Badakhshan, Ghazni, Helmand da Kandahar ba. duk wani yunkuri na karbar mulki ta hanyar tarzoma da sanya tsoro a zukatan jama'a da yaki zai sa kasashen duniya su ware kasar."

Kasashen Yamma za su yi jan aiki wajen kawar da masu ikirarin jihadi

Babban burin Taliban shi ne yin mulkin Afghanistan bisa fahimtarta game da shari'ar Musulunci.

Sai dai sauran kungiyoyin da ke ikirarin jihadi irin su al-Qaeda da IS suna da nasu bukatun na daban. Mai yiwuwa a idan sabuwar gwamnatin Taliban ta hana su motsi, akwai wasu yankuna a kasar da za su bar su su yi abin da suke so ba tare da an sani ba.

Dr Sajjan Gohel daga Gidauniyar Asia Pacific yana sa ran adadin mayakan al-Qaeda 200 zuwa 500 zai karu a lardin Kunar.

Osama bin Laden

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyar al-Qaeda ta Osama bin Laden ta tsara da kuma kaddamar da hare-haren 9/11 daga Afghanistan

"Mamayar da Taliban ta yi wa lardin Kunar tana da matukar muhimmanci a gare ta saboda yana da tsaunuka masu wuyar shiga da kuma dazuka masu sarkakiya. Tuni al-Qaeda take da mazauni a yankin wanda za ta so ta fadada."

Idan hakan ya faru, zai yi matukar wahala ga kaashen Yamma su tunkare ta.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, sun dogara ne da bayanan da suke samu daga hukumar leken asirin Afghanistan, tare da taimakon tawagar Amurka da Birtaniya da dakaru na musamman na kasar Afghanistan.

Yanzu duk wannan ta kare, lamarin da zai sa Afghanistan ta zama mai matukar wahalar sha'ani ga masu leken asiri.