Zamantakewa: Shin an zo zamanin da maƙwabta ke tsoron juna ne?

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashina tara, shirin ya yi duba ne kanyadda zamantakewar maƙwabtaka ta lalace a wannan zamanin, ba kamar a baya ba lokacin.

Maƙwabtaka ta zama abin da ta zama a cikin al'ummarmu a yau. A da mun taso mun ga iyayenmu sun zama tamkar ƴan uwa da maƙwabtansu.

Kansu a haɗe, ana zumunci. Idan biki ake a gidan maƙwabta sau tari ma sai bikin kacakom ya koma gidajen sauran maƙwabtan.

Tare yara suke zuwa makaranta, su ci abinci tare, wato ciyayya, su yi wasanni tare.

Maƙwabci na da izinin hukunta ɗan maƙwabcinsa daidai gwargwado a inda yaron ya yi ba daidai ba, sannan yana ƙoƙarin nuna soyayya da tausayi ga ƴaƴan maƙwabcinsa tamkar nasa ƴaƴan.

A misali ni a tasowata a unguwanni biyun farko da mahaifana suka zauna, shekara kusan 30 da suka gabata, amma har yanzu akwai zumunci mai ƙarfi tsakaninmu da maƙwabtan duk da cewa mun bar unguwannin.

Na kan tuna lokuta masu ɗadi na zamanin ƙuruciya, inda muke cin abinci tare da ƴaƴan maƙwabtanmu, daga wannan gidan sai mu je gida na gaba a zuba mana, kuma duk a tire ɗaya muke ci.

A ƙauyuka kuwa a da, har aikin gayya na noma ko girbi a kan taru a yi wa maƙwabci idan ba shi da lafiya, ko kuma idan duka ƴaƴansa mata ne ba zama sai a je a taya shi.

A gaskiya a yanzu ba na ganin irin wannan zumuncin. Yau an wayi gari wai mutum na iya zaman shekara guda cur a unguwarsa bai san su waye maƙwabtansa ba.

Lamarin ya yi muni ta ɓangaren maza da mata duka.

Ta kai ta kawo yanzu har ƙarar maƙwabciya sai ka ga mata na kai wa a zaurukan sada zumunta, suna neman wai a ba su shawara kan wani rashin kirki da maƙwabciya tai musu.

Caa su kuma mabiya dandalin sai a fara ai da ni ce wallahi ba zan yarda ba, kaɗan ne za a ga suna ba da shawarar yin sulhu.

Wasu na baya da za ku so ku karanta

To me ya jawo hakan ne, kuma ta yaya za mu gyara?

Wasu na ganin yanzu zamani ne ya sauya ta yadda rayuwar ta zama kowa tasa ta fisshe shi. Mutane suna ganin za su iya rayuwa ba tare da sa hannun kowa ba.

Wasu kuma gudun gulma da gutsuri tsoma ce take hana su sakar jiki da maƙwabtansu. Sun gwammace su kammale kansu a gidajensu, ba tare da shiga shirgin kowa ba.

Amma wasu na ganin tsabar kwaikwayon rayuwar Turawa ce kawai da ta yi mana katutu, abin da ya sa mu'amalar ta sauya.

Sheikh Nuru Khalid limamin masallacin Apo da aka fi sani da Digital Imam ya ce abu uku ne suka lalata zamantakewar maƙwabtaka a zamanin nan.

Na farko tattalin arziki, inda ya ce babu abin da mutane ba sa yi a zamanin saboda kuɗi don cutar da maƙwabta.

Na biyu ya ce mutane na lalata saƙon addini wajen ɓata zamantakewar addini.

Na uku kuwa ya ce zamananci na ɗaukar baƙin al'adu da mutane suka yi ya lalata zamantakewar addini.

Malam ya ce ya kamata kowa ya fahimci cewa maƙwabcinka shi ne mutum na fao da yake buƙatar agajinka a duk lokacin da wata matsala ta taso maka.

Ita kuma Malama Fatima Tasallah Nabulusi Baƙo (MFR) ta ce maƙwabci wani abu ne mai girma da Allah da Manzonsa SAW suka yi magana a kansa.

Tace dole ka kiyaye haƙƙoƙin maƙwabci na gudun cutar da su ko zalintarsu ko da kuwa da magana ne.

Ƙarin wasu da za ku so

Bayan jin ta bakin wadannan ƙwararru, yanzu kuma ga wasu ƴan abubuwa da za ku riƙe don kyautata wannan zamantakewa ta maƙwabtaka.

Yana da kyau ku dinga bibiyar halin da maƙwabtanku ke ciki, amma kar ku zurfafa shisshigewa duba da cewa wannan zamanin wataƙila wasu taka tsantsan suke don tsira da mutuncinsu.

Amma dai a yanayi na rashin lafiya da jaje da taya murna, kar a bar ku a baya, ku tabbatar kun sauke waɗannan manyan hakkokin.

Ku guji yin gulmar makwabtanku musamman a wajen wasu makwabtan, ranar da ƙwai zai fashe fa za a samu gagarumar matsala, kuma mutunci zai zube.

Ki dinga ɗan tuna cewa wataƙila maƙwabciyata wance fa da take da cikin nan yau ta ɗan tashi da kwadayin abincin gidan maƙwabta, kun da san ciki da tsirface-tsirface.

Dan kira ta ki ji, nebo yau dambun shinkafa na yi ko a zubo miki ne.

Wadannan ƙananan abubuwan na kyautatawa ki sani cewa ba ƙaramin tsayawa a rai suke ba.

Don Allah wannan izzar da jin cewa zaman bariki dan kowa yai ta kansa a ɗan rage. Ranar fa da wani babban al'amari ya sameka kafin kowa ya zo kanka sai maƙwabci ya zo.

A mako mai zuwa za mu bude babin tarbiyya a zamanin nan.