Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zamantakewa: Waɗanne sharuɗa aka ɗora wa namiji kafin ya auri mace fiye da ɗaya?
Wannan makon shirin maimaici ne, amma za mu kawo muku sabo a mako mai zuwa:
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da zai dinga lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na huɗun, shirin ya yi duba ne kan rayuwar namiji mai mace fiye da ɗaya, da irin adalcin da ya kamata ya shimfiɗa a tsakanin iyalansa da yadda zai kyautata zamantakewarsa da su don a samu kwanciyar hankali.
Maigida a kowane lokaci shi ne jagora kuma ƙashin bayan gina iyalinsa da ɗora su a kan turba mai kyau.
Shi Allah Ya ɗora wa nauyin aurowa da kuma kula da abin da ya aura ɗin.
A addinin Musulunci an ba shi damar auren fiye da mace ɗaya, amma ba a bar shi haka ba sai da aka saka masa dokoki da iyakoki, don haka ne ma wasu malaman ke ganin auren mace fiye da ɗaya ba na kowane namiji ba ne.
Mata da dama a wasu lokutan da suke su biyu ko uku ko huɗu a wajen mazajensu, kan yi ƙorafin cewa rashin adalcin da wasu mazan ke nunawa shi ke kawo rarrabuwar kawuna da rashin zaman lafiya.
Akwai gidajen da tsabar tsananin kishin da ake yi sai ka rasa gane ko son mijin ne ya jawo hakan ko kuwa ma dai ba sa son sa ne.
Wasu gidajen kuma salon yadda masu gidan ke tafiyar da shi zai sa ka dinga tunanin anya wannan mijin ba shi ne silar matsalar gidan ba?
To ko ma dai mene ne akwai hanyoyin da za a iya bi a inganta zamantakewa a gidan mai mata biyu, ko uku ko huɗu, kamar yadda masana da ƙwararru suka ce.
Daga cikin wadanda shirin Zamantakewa ya yi hira da su a wannan mako akwai Farfesa Ibrahim Maqry babban limami a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Sannan sai Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, malama a Jami'ar Al-Qalam ta jihar katsina da kuma wani malami masanin halayyar ɗan adam da Dr Hadi Musa, malami a fannin halayyar ɗan adam a Jami'ar Maitama Sule ta Kano.
Wasu na baya da za ku so ku karanta
Sheikh Maqry ya ce mataki na farko na shimfiɗa zamantakewa mai kyau a gidan da ake da mace fiye da ɗaya shi ne namiji ya fara duba tukuna ma ko yana da wadatar da zai iya riƙe matan ta hanyar raba musu wajen zama.
"Kamata ya yi a ce idan za ka auri mace fiye da ɗaya, to ka tanadar wa kowacce gida isasshe wanda zai ɗauke ta ita da iyalanta.
"Kar ka haɗa su, idan ma a gida ɗaya ne to kowacce a ware mata ɓangarenta daban, hatta da kicin da hanyar wucewa ta zama daban, a cewar malam.
Ya nanata cewa: "Dole a dinga samun matsala idan ana haɗe a waje ɗaya tun da a wasu lokutan zuciya ba ta da ƙashi, lokacin da zai nuna alamar ya fi karkata ga wata ma ba zai sani ba.
"Hakan kuma yana iya tunzura zuciyar ɗayar har zamantakewa ta taɓarɓare," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Tambayoyi huɗu da ya kamata ya yi wa kansa kafin ƙara aure
Dr Hadi kuwa cewa ya yi ya kamata namiji ya san cewa a tun lokacin da ka fara neman aure, akwai abubuwan da ya kamata ka kiyaye su.
Ya ce duk namijin da yake son ƙara aure to ya kamata ya yi la'akari da wasu tambayoyi masu muhimmanci guda huɗu.
"Tambaya ta farko ita ce, yana buƙatar auren ma? Don mutane da yawa kan ƙara aure ne kawai don sun ji ana cewa za ka iya ƙara aure, ba tare da ya san yana da buƙata ba ko a'a.
"Tambaya ta biyu ita ce, mene ne dalilin da ya sa yake da buƙatar ƙara aure? Matarsa ce ta ba ta haihuwa yake son ya auri wacce za ta haihu? Ko ayyuka ne suka yi mata yawa bata sauke wasu nauye-nauyen?
"Tambaya ta gaba, wace irin mace ce ta dace da waɗannan buƙatun?
"A ƙarshe dole idan ya samu wacce yake so to ya fara da nuna mata muhimmancin matarsa ta gida da cewa tana da ƙima da daraja, kuma ba don ya gaji da ita zai ƙaro ba," a cewar Dr Hadi.
Ya kuma yana da kyau miji ya tattashi uwargida da ba ta baki da nuna mata cewa ba don ya gaji da ita ne zai ƙara aure ba.
Sannan ya ce ita ma uwargida sai ya ja kunneta da cewa kar ta wulaƙanta amarya ko bayar da ƙofar da za ta jawo wa kanta wulaƙanci.
Hajiya Bilkisu Yusuf Ali ta ce kar ka bai wa wata fifiko mai yawa fiye da ɗayar, sannan kar ko da zuciyarka ta fi son ɗaya to kar ka bari duk su biyun ka gane.
"Domin idan wacce ka fi so ɗin ta gane to za ta yi amfani da damar wajen wulaƙanta ɗayar, idan kuma wacce son ta ba shi da yawa a zuciyarka ne to za ta dinga jin ita bora ce ta kasa zama lafiya da dayar," in ji Hajiya Bilkisu.
Wasu muhimman batutuwa da za a kula da su
- Kar ka je kana aibata matarka a gaban wacce kake shirin ƙarowa
- Kar ka zama mai kawo wa uwargida hirar amaryarka
- Idan ka shiga gida, duk abin da zai jawo fitina kamar waya da amarya, ka daure ka guje shi
- Ka ga wadannan kananan abubuwan, kar ka raina su wallahi suke tunzura mata wasu lokutan
- Idan gida daya za ka hada su, ka tabbatar ka kiyaye muhimman sharuddan zaman tare
- Kar ka dinga fifita daya a gaban daya, ka zama adali a kowane fanni
- Kar ka yarda ka zama munafukin mata, kuma kar ka bari karfar baka ta rude ka
- Dole ka iya takunka sosai
- Kar ka zama munfukin mata
- Ka zama tsayayyen maigida, jajircacce, wanda zai dinga wanzar da adalci a duk harkokinsa
- A ƙarshe ki zama mai basirar gano karfar baka, wato kisisina irin ta wasu matan. Don wata kan zauna ta kalallame ka da zance ta haɗa wa abokiyar zamanta tuggu, kai kuma ka hau ka zauna ba tare da bincike ba.
Mako na gaba shirin zamantakewa zai bude babin surukuta ne, domin shi ma fannin ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwarmu ta yau da kullum.