Zamantakewa: Sarƙaƙiyar da ke cikin zamantakewar iyayen riƙo da ƴaƴan riƙo

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashina takwas, shirin ya yi duba ne kan Sarƙaƙiyar da ke cikin zamantakewar iyayen riƙo da ƴaƴan riƙo.

Daga cikin al'amuran zamantakewa masu matukar sarkakiya akwai batun riƙon 'ya'ya.

A idanun al'umma a mafi yawan lokuta iyayen riƙo ba sa tsira daga zarge-zarge da tuhume-tuhume, haka su ma 'ya'yan riƙon.

Wasu Allah Ya kan ɗora musu nauyin riƙon ko dai 'ya'yan 'yan uwa marayu da ma waɗanda iyayensu ke rayen ko 'ya'yan miji ko 'ya'yan dangi ko na abokan arziki, kai wani lokacin ma har 'ya'yan da babu dangantakar jini.

Sai dai za a yi ta jin gutsuri tsoma, wance na cin zalin su wane, tana dukansu tana hana su abinci da sauran matsaloli.

A wasu yanayin kuma sai a samu ma cewar matsalar daga uban riƙon take ba uwar riƙon ba.

Sau da yawa za a ga mutum na nuna bambanci tsakanin 'ya'yansa da na ƴan uwansa uwa ɗaya uba daya, wataƙila saboda kawai ƙasa ta rufe idon nasu mahaifan.

Mun sha ganin yadda a gidaje da dama ake nuna bambanci ƙarara tsakanin ƴaƴan da ake riƙo da ƴan gidan, tun daga yanayin abincinsu zuwa sutura da ma makarantun da suke halarta.

A wasu gidaje ana ƙoƙari sosai wajen ƙin bambanta ƴan gida da ƴan riƙo ta fannin abinci da sutura da makarantu, sai dai duk da haka sai a ga cewa iyayen riƙon ba su tsira daga zargin yin ba daidai ba.

Wasu iayyen riƙon kuma da gangan suke nuna bambanci, yayin da wasu zuciya ɗaya ce ta sa suke wasu abubuwa, kamar ƙoƙarin gyara tarbiyyar yaran.

Hajiya Hadiza Lamara wata uwar riƙo ce a Bauchi da ta ce min ta riƙe yara da dama, kuma ita a yanayinta mai ƙoƙarin ɗabbaka tarbiyya ce ga yara.

"Ina daɗan zafi ta wajen tarbiyyar yara, har kuwa a kan ƴaƴana, don haka sai a dinga ganin kamar mugunta nake yi wa ƴaƴan riƙo.

"Ba a lura da cewa ko ƴaƴan cikina haka nake musu. Gaskiya mutane wani lokacin ba sa adalci wajen fassara yadda wasu ke tafiyar da al'amuransu," in ji ta.

A wasu lokutan kuma ƴaƴan riƙon ne ke zama ƴan kansu, a goya su a musu 10 ta arziki amma daga sun samu duniya a gaba sai su zama dan kaza ci ka goge baki.

Sau tari ma tun kafin ɗan riƙo ya girma ya zama wani abu sai a ga ba ya kallon alherin iyayen riƙonsa.

Wasu duk inda suka zauna sai zagi da kushe duk wani ƙoƙari da ake yi musu, ko kuma a samu wasu su dinga zuga su.

"Su kuma sai ka ga suna ɗaukar zugar suna yi wa iyayen riƙonsu tijara," in ji Hajiya Hadiza.

To wai ta yaya za a rage a kalla ko ba a daina duka ba wasu matsaloli na batun riko a wannan al'umma tamu?

Na farko dai abu ne mai wahala a ce dole sai iyayen riƙo sun daidata soyayyar ƴaƴansu da ƴaƴan riƙo, abu ne kamar na mai mace fiye da ɗaya.

Ba lallai yawan soyayar da yake yi musu ta zama ɗaya ba, amma gara ya bar hakan a zuciyarsa.

To haka lamarin ƴaƴan riƙo da iyayen riƙo yake, ba lallai su so ƴan riƙo daidai yadda suke son ƴaƴansu a zuciya ba, amma idan da dattako to za su bar komai a ransu su jaddada adalci a zamantakewarsu da su.

Wannan zai samo musu wata ƙima ta musamman a idon ƴaƴan riƙon nan da ma nasu ƴaƴan da sauran al'umma.

Idan har sun san duk abin da suke wa ƴaƴan riƙon don Allah ne har zuciyarsu, kamar misali wajen ɗabbaƙa tarbiyya, to su toshe kunnensu daga duk abin da za a ce su ci gaba da ƙoƙarinsu.

Su kuwa ƴaƴan riƙo kar su bayar da ƙofar da za a dinga zuga su don juyawa iyayen riƙonsu baya, su gane cewa laheri danƙo ne.

Iyayen da ake riƙon ƴaƴansu a wani wajen su ma sai sun kawar da kai daga wasu ƙananan ƙorafe-ƙorafe tare da sa ƴaƴansu kan hanya na yadda za su zauna da mariƙansu lafiya.

Batun duka da zagi da cin mutunci wannan duk ya kamata a ce ba sa cikin tsarin riƙon da za ka yi wa ɗan wani.

Masu iya magana kan ce ɗa na kowa ne, bawa sai mai shi.

Ƙarin wasu da za ku so