Afghanistan: Matan ƙasar na fargabar rashin sauyawar ƴan Taliban

Mulkin Taliban na tsawon shekara 20 an ga cin zarafin mata kamar sare kai da jifa da tursasa musu sa burka. Bayan da aka daƙile ƴan bindigar, mata a Afghanistan sun samu ci gaba- wasu sun zama ministoci da magajin gari da alƙalai da ƴan sanda. Sai dai yanzu suna matuƙar fuskantar rashin tabbas.

'Ana buƙatar sadaukarwa'

Wata ƴar jarida mace na zaune da wani babban jami'i suna tattaunawa ba wani babban labari ba ne a mafi yawan ɓangarorin duniya.

Amma duba da yadda Taliban ta yi ƙaurin suna wajen hana mata walwala, da yawa sun yi mamaki lokacin da ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar, Mawlawi Abdulhaq Hemad ya amince wata ƴar jarida ta tattauna da shi a kafar Tolo News, Bechesta Arghand.

Tattaunawar ta ranar Talata ta saɓa wa wata al'ada: shi ne karo na farko da wani shugaban Taliban ya yi irin haka a tashar Talabijin. Amma duk da waɗannan sauye-sauye, hankalin Arghand bai tashi ba.

"Sun ce, 'ba mu da wata matsala da matan Afghanistan. Muna goyon bayan aikinsu'... Amma ina jin tsoro,"ta shaida wa BBC.

Ta ce yanayi ya sauya a wurin aikinta a Kabul kuma birnin ma ya sauya. Ba ta iya tattaunawa da bakinta kan matsalolin da ke ƙasar. Tana takatsantsan.

"Bayan wata ɗaya ko biyu ƴan Taliban za su sa mana dokoki. Ina tunanin ba za su bar mu muyi abin da muke so ba. Zai yi wuya su bari mu ci gashin kansmu.

"Yanzu, sun nuna kamar babu damuwa amma dole mu yi takatsantsan. Ina takatsantsan."

A ƙarshen shekarun 1990 da farkon shekarun 2000, ƙungiyar ta jagoranci Afghanistan ƙarƙashin tsarin Shari'ar Musulunci kuma suka haramta amfani da talabijin da waƙoƙi da zuwa silma. A shekarun da suka biyo bayan hamɓarar da mulkinsu, an kafa gwamman gidajen talabijin da gidajen rediyo sama da 170.

Dawowar Taliban mulki ke da wuya, wasu tashoshin Talabijin suka daina sa mata masu gabatar da shirye-shirye kuma suka sauya shirye-shiryensu na siyasa zuwa na addinin Musulunci.

Da suka ga ƙungiyar ba ta ce komai ba, tashoshi da dama sun koma yar gidan jiya.

A wani taron manema labarai kwanan nan, ƙungiyar Taliban - wadda a yanzu ke mulkin mutum miliyan 39 - ta ce za su bai wa mata damar yin aiki da zuwa makaranta "bisa tsarin addinin Musulunci".

Amma a wurare da dama mayaƙan sun hana mata zuwa aiki. Wasu matan sun shaida wa BBC cewa sun janye jiki ne saboda tsoro.

Arghand ta koma aiki ne saboda tana ganin ya dace a ce tana aikin a wannan lokaci mai muhimmanci.

"Na gaya wa kaina cewa ki je... wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga mata a Afghanistan."

A hanyarta ta zuwa ofis mayaƙan Taliban sun tsayar da ita sannan suka tambayeta abin da ya sa take tafe ita kaɗai ba tare da muharrami ba kamar yadda Shari'a ta tanada.

"Muna cikin yanayi marar kyau. Mun san cewa wannan ba abu ne mai kyau ba ga mata a Afghanistan. Dole sai mun yi fafutuka kuma mun yi sadaukarwa ga waɗanda za su zo a bayanmu."

'Ba kamar wancan mulkin nasu ba ne'

Wata likitar mata da ke da asibitinta mai zaman kansa kuma take da asibiti a Kabul ta shaida wa BBC cewa rikicin siyasar bai shafi aikinta ba.

"Na zo aiki bayan kwanaki uku. Komai na tafiya kamar yadda aka saba," a cewar likitan da ba ta so a bayyana sunanta.

Ta ce ƴan Taliban sun sanar da cewa likitoci mata na iya ci gaba da aiki a asibitoci.

Likitar ta ce a wasu wuraren ƴan Taliban na bukatar mutane su koma bakin aiki amma saboda yanayin tsoro da ake ciki, da yawa ba sa zuwa.

"Likitoci da ungozomomi da yawa ba su zo asibiti ba saboda suna tsoro kuma ba su gamsu da sanarawr Taliban ɗin ba."

A ƙauyuka da dama na Afganistan, babu cibiyoyin lafiya.

kasar ta ɗauki matakan inganta yawan malaman jinya da ungozomomi don rage yawan matan da ke mutuwa yayin haihuwa. Hukumar Ƙidaya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce duka mata masu juna biyu da masu jego "na da ƴancin samun kulawa da su da jariransu".

A halin yanzu, likitar matan a Kabul tana da hasashe mai kyau. A hanyarta ta zuwa asibiti ta ga mutane ƙalilan a kan tituna kuma shaguna da yawa sun kasance a rufe amma Taliban ba su tsayar da ita don duba kayanta ba.

"Ba kamar wancan karon ba. Yanzu abubuwansu da sauki idan aka haɗa da wancan mulkin nasu ba."

'Mata ba sa cikin ajandar'

Cikin kujeru 250 na majalisar dokokin Afghanistan, kashi 27 cikin ɗari na mata ne kuma a halin yanzu akwai mata ƴan majalisa 69.

Amma Taliban ba su da mata cikin jerin shugabanninsu kuma ba a sani ba idan za su sa mata a gwamnatin tasu.

"Ba mu san yadda ajandar tasu ta ke ba. Abin da ke damunmu shi ne ba sa taɓa magana kan mata," in ji wata yar majalisa, Farzhana Kochai.

Ta ce gwamnatin da babu mata a cikinta ba za a riƙa ganinta a matsayin wadda ta san abinda ta ke yi ba a idon duniya.

"Mu mata bai kamata a cire mu daga gwmanati ba. Ya kamata mu ci gaba da aiki kuma mu kasance a gwamnati da duk ma inda mu ke so."

'Ba ni da tabbas a kansu'

Abin da Taliban suka ce kan haƙƙoƙin mata da kuma abin da suke yi a zahiri sun sha bambam, a cewar wata malamar makaranta kuma mai fafutukar kare hakƙin Pashtana Durrani.

Ta shaida wa BBC cewa tana kira da a fayyace waɗanne haƙƙoƙin mata ne kungiyar ta Taliban ta amince da shi, wadda a baya ta tursasa wa mata sa burka sannan ta hana yara mata ƴan sama da shekara 10 zuwa makaranta.

Durrani ta ce ta ga ya dace ne ta yi magana duk da cewa tana tsoro.

"Dole ne in yi fafutuka a yau, don waɗanda za su zo a baya kada su fuskanci waɗannan matsalolin."

Durrani ta ce shugabancin Taliban ba ta fito ƙarara kan haƙƙoƙin mata ba amma mayaƙanta na ƙasa na nuna halayyar da aka sansu da ita a ƴan kwanakin nan.

"Yara mata a Herat, ba su iya zuwa jami'a ba: yara mata a Kandahar, an kore su gida an ce yara zama su zo a mdadinsu...

"Don haka... ƴan Taliban na neman halacci daga ƙasashe da dama, don a gansu a matsayin halattacciyar gwamantin Afghanistan amma kuma a lokaci guda me suke yi a zahiri?

"Ko dai ba su da iko da sojojinsu na ƙafa ko kuma suna matukar son halacci amma ba sa so su yi aikin. Waɗannan abubuwan biyu daban ne."

Haka kuma, Malama Durrani na buƙatar sanin abin da Taliban ke nufi idan suka ce "haƙƙoƙin mata".

"Suna nufin haƙƙin yin tafiya ko haƙƙin cakuɗuwa da sauran mutane, da haƙƙin siyasa ko kuwa haƙƙin yin zaɓe?" a cewarta.

Jamus ta ce za ta daina bai wa Afghanistan agaji idan ba a kare haƙƙin mata ba. Wasu masu sa ido na cewa Taliban za su bai wa mata ƴanci don shawo kan shugabannin duniya.

Durrani, wadda ta karɓi lambar yabo ta Malala Fund Education Champion saboda aikinta, tana ganin ƙarshenta sai dai mata sun yi karatu ta intanet idan Taliban ta hana yara mata zuwa makaranta.

Tana fargabar mayakan na iya sauya darussan makaranta.

"Yaran na iya ci gaba da karatu da manhajar da aka sani ko kuma karatun addini da ko wane ɗan Afghanistan ke amfani da shi?" a cewarta.

"Ba ni da tabbasa a kansu."

'Ƴanci kawai na ke so'

Wata ƴar kasuwa matashiya da ke zaune a babban birnin Afghanistan, wadda ke amfani da sunan bogi na Azada don kare kanta, ta ce ba ta yarda da alkawurran da Taliban ta yi ba.

"Azada na nufin mutumin da ke da ƴanci. Babu abin da nake so yanzu irin ƴanci. Shi ya sa na zaɓi wannan sunan."

Tana fargaba game da sabbin shugabannin kuma tana da bukata mai sauki:

"Ina son sabuwar gwamnati da za ta sa kowa da kowa a harka. Ina son Taliban, da ƙungiyoyi masu nuna turjiya da mutanen daga ko wane addini. Idan hakan ya faru za mu samu sabuwar kasa. Sannan za mu yi fatan ganin gaba mai kyau."

Amma ta fara ganin zahiri. Ta fara rasa ƴanci kasuwancinta saboda ta rufe shagonta kuma yayin da wasu da yawa ke tserewa daga ƙasar, Azada ta ce ba za ta iya ba.

Tunanin mulkin Taliban na dawo mata - ta ce sun nuna wa mata barazana kuma a yanzu ma ba ta tunanin za su sauya hali.

"Ba su sauya kayansu ba, gemunsu na nan, ya za a yi su sauya aƙidarsu? Ban yarda da irin waɗannan jita-jitar ba," a cewarta.

Ta yi hasashen cewa idan Taliban ta cire mata da wasu ƙabilu, za a sake fuskantar rikici.

"Za a yi yaƙi. Idan ba mu fafata ba, ba za mu rayu ba. Zan zama ɗaya daga cikinsu. Zan iya rasa rayuwata. Ba wani abu ba ne wannan. Dole in jajirce. Ba zan iya tserewa daga Afghanistan ba. Wanann ne kawai zaɓina."