Cocoa zai maye gurbin man fetur wurin samar da lantarki a Ivory Coast

A woman at a cocoa exhibit

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Gitonga Njeru
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC

Matsawar kai mai sha'awar cin cakuleti ne, to akwai yiwuwar ka ci wanda ya aka sarrafa daga kokon da ya fito daga Ivory Coast.

Ƙasar wadda ke Kudancin Afrika ita ce ta fi kowace ƙasa a duniya fitar da koko. Hasali ma kashi 40 na ƙwayar koko a duniya daga can ya fito.

Shi ne babban abin da ke samar wa Ivory Coast kuɗin shiga, kuma ya samar wa sama da mutun miliyan shida aiki.

Amma a maimakon kai shi waje don samun kuɗi, a yanzu Ivory Coast ta yanke shawarar amfani da wani kaso na kokon don samar da wutar lantarki ga ƙasarta.

A maimakon fitar da shi ƙasashen waje ana sarrafa shi zuwa cakuleti da abin sha, gwamnati za ta ware wani kaso don moriyar al'umma ta hanyar amfani da shi don samar da makamashi.

Tuni an gudanar da gwaji wanda ya nuna cewa za a iya samun nasara wurin samar da lantarki ga miliyoyin gidaje.

An shirya samar da tashoshi da za su riƙa samar da wutar lantarkin ta amfani da koko.

''Wannan tasha kaɗai za ta iya samar da lantarki ga kusan mutun miliyan biyu, a cewar Yapi Ogou, babban darakta ne a kamfanin makamashi na Société des Energies Nouvelles da yanzu haka ke aikin gina tashoshin.

Ƙaruwar koko

Tashar ta Divo biomass za ta zama tasha mafi girma a Yammacin Afrika da za ta samu taimako daga ƙungiyar cinakayya da ci gaba ta Amurka.

Kuma an shirta kammala ta a farkon shekarar 2023. Kazalika za ta riƙa samar da tsakanin megawat 46 zuwa 70 na wutar lantarki a duk shekara a cewar Ogou.

Wani ci gaba da za a samu shi ne tashoshin shi ne za a rage gurɓacewar yanayi wanda ke samuwa a dalilin amfani da sauran hanyoyin samar da lantarki.

Workers sorting cocoa beans

Asalin hoton, Getty Images

Ivory Coast na samar da kashi 70 na lantarkinta ne daga gas, to amma a yanzu burinta shi ne ta rika samar da kashi 42 na lantarkin daga koko daga nan zuwa 2030.

Tana fatan hakan zai rage gurɓacewar yanayi da aƙalla kashi 28 cikin 100.

An ƙiyasta cewa shirin zai laƙume kusan dala miliyan 224 da za a gina tashoshi tara da su a fadin ƙasar.

An kuma tsara cewa za a gina tashoshin a inda ake samar da koko don sauƙin samar da shi tare da samar da tarin ayyukan yi da kudin shiga ga dubbai.

Franciah na daga cikinsu, don ta mallaki kadada 14 ta koko a kusa da tashar Divo.

Ta shafe shekaru tana tunanin yin watsi da noman koko gaba ɗaya.

Ba ita kaɗai ba, manoma da dama a baya sun yi watsi da noman koko zuwa na ayaba da sauran kayan gona da suka fi noman shi riba.

Franciah ta bayyana irin alherin da ta samu da noman koko.

''Ta hanyar noman koko na ke biya wa ƴa'ƴana makaranta duk da cewa a yanzu ribar da muke samu ta ragu.''

A yanzu ta ce tana maraba da shirin gina tashoshin samar da lantarki ta amfani da koko, lura da tarin amfanin da ke ciki.

''Yadda na ke bazawara yanzu don mijina ya rasu shekaru 18 da suka wuce, da wannan shiri zan ƙara samun kuɗin yi wa ƴa'ƴana lalura har ma na ajiye ɗan wani abu.''

Baya ga buɗe sabuwar tashar, gwamnatin Ivory Coast ta shirya samar da wata ƙungiyar taimakon kai-da-kai ga manoman koko.

Manoman za su amfana ta hanyar adana ɗan wani abu na kudin da suke samu, wanda hakan zai ba su damar samun bashi don yi wa iyalansu lalura ko kuma buɗe wata sana'a daban.

A hand holding cocoa beans

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An shirya samar da tashoshi da za su riƙa samar da wutar lantarkin ta amfani da koko.

Ba Ivory Coast ba ce ƙasa ta farko a duniya da ta yi tunanin amfani da ɓawon koko ta wata hanyar ci gaba ba.

Yanzu haka Ghana na amfani da ɓawon koko wurin samar da hasken lantarki da bai taka kara ya karya ba.

Masu bincike a jami'ar Nottingham da ke Burtaniya sun samar da inji na hasken lantarki da ke amfani da ɓawon koko.

A yanzu shirin na Ivory Coast na fatan samar da hasken lantarki ga miliyoyi, a ƙasar da dama kashi 50 ne kawai suka mallaki wutar lantarkin.