Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Emma Coronel Aispuro: Matar hamshakin mai safarar miyagun kwayoyi ta yi faduwar bakar tasa
- Marubuci, Daga Tara McKelvey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Emma Coronel Aispuro ta yi rayuwar jin dadi a birnin New York, tana more amfanin aurenta ga hamshakin mai safarar miyagun kwayoyi Guzman Loera, da ake yi wa lakabi da El Chapo. Daga bisani, an cafke ta aka garkame ta a gidan yari na jihar Virginia. Shin me ya faru ga sarauniyar kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta duniya?
Tagogin gidan yarin, Cibiyar Tsare Manya a Alexandria, an yanka su ne ta cikin ginin jan bulo, kuma a nan ne inda ake tsare da Emma Coronel Aispuro ita kadai a wani tsukakken daki.
A cikin dakin, in ji lauyar ta Mariel Colón Miro, tana karanta litattafan kagaggun labarai, don debe kewa.
Yanayin gidan yarin na da matukar banbanci da irin rayuwar da ta saba yi a da.
Watanni kadan da suka gabata, ta yi aniyar kaddamar da wani kamfanin zayyana tufafin kawa da ake kira El Chapo Guzman. (Ma'auratan na da wata alama da ken una matsayinsu a kasar Mexico, kana ita ma 'yar su ta yi fice a fannin ado da kayan kawa ta hanyar amfani da sunan shi.
A lokacin da na tattauna da ita a birnin New York yayin da ake yi wa mijinta shari'a a shekarar 2019, tana sanye da sarkoki da agogo mafi tsada.
Amma a farkon wannan shekarar, an cafke Coronel mai shekkaru 31 a filin saukar jiragen saman a kasa da kas ana jihar Virginia kuma aka tuhume ta da taimaka wa mijinta, hamshakin mai fataucin miyagun kwayoyi wajen shugabantar sananniyar kungiyar Sinaloa ta masu tu'ammali da fataucin miyagun kwayoyin.
Yanzu haka Guzman mai shekaru 64, na zaman daurin rai-da-rai a gidan yarin Colorado.
Jami'an hukumar binciken masu aikata manyan laifuka ta Amurka FBI sun ce an hada baki da Coronel wajen rarraba hodar ibilis kana ta taimaka wajen shirya yadda mijinta ya tsere daga gidan kurkukun kasar Mexico a shekarar 2015.
Labarinta wanda ya shafe ta ne ita kadai, tare da batun mijinta mai cin amana, da wata budurwarsa da kuma kamafanin aikata muggan laifuka.
Duk da haka ta yi karin haske kan sirrikan duniyar kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi, da kuma matan da ke tare da su.
Ba a tsayar da ranar da za a gudanar da sauraron karar ba. Muddin aka same ta da aikata laifi, za ta fuskanci zaman daurin rai-da-rai a gidan yari
Idan aka ajiye batun samun ta da aikata laifi ko kuma akasin haka, masu sharhi da suka gudanar da bincike kan duniyar fataucin miyagun kwayoyi sun bayyana cewa Coronel ta taka rawar da ba a saba gani ba a gare ta.
'Yar kasuwa ce, mai hudda ta jama'a, kuma mai lura da komai wajen taimaka wajen sa ido kan duk wanda ya kamata ya yi hudda da mijinta a lokacin da yake rike da kungiyar masu fataucin miyagun kwayoyin.
A al'adance, ana kallon matan masu fataucin miyagun kwayoyi a matsayin kawai ''masu gamsarwa a fannin jima'a'' a kan wadanda ''ba su da wata sana'a'', in ji Cecilia Farfán-Méndez, wata malama a jihar California a San Diego.
Coronel ta fita daban: "Ta nuna cewa mata za su iya rike babban matsayi.''
Nuna karfin mulki a cikin kungiyar abu ne mai hadari.
Derek Maltz, wani tsohon jami'a ne mai lura da bangaren hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Amurka, ya ce: " Idan dai kana cikin harar, daman ko ya zamana a kama ka ne, ko kuma a kashe ka.''
Coronel ta nuna jarumta, da shirinta na bude kamfanin zayyana tufafin kayan kawa, amma kuma hukumomin binciken na kokarin rufewa.
Kamar yadda Maltz ta bayyana:" Duniya na kokarin juya mata baya, komai nata na ja baya.''
Sace-sacen jama'a da kisan kai
Coronel na cin wani ganyen lettuce da aka yanka, a Kotun Tarayya ta Gunduma da ke birnin Brooklyn, lokacin sauraron karar mijinta.
Tana zaune tare da kawayenta a wurin cin abinci, suna hirar barkwanci a kan iyaye mata, da kuma yadda za su shawo kansu.
"Tana da kyawawan hali,'' in ji Miro, lauyarta. "Emma da na sani - tana cikin kuzari, ga murmushi a koda yaushe.''
Coronel, 'yar duka kasashen Mexico da Amurka, ta hadu da Guzman lokacin tana da shekaru 17, kuma ba da jimawa ba suka yi aure. Suna da 'yaya biyu, Maria Joaquina da Emali.
A lokacin sauraron karar mijinta, Coronel kan zauna a zauren kotun a koda kullum.
"Sarauniyar Sinaloa," in ji Le Cour Grandmaison, wani mai sharhi kan al'amuran da suka shafi tsaro da ke zaune a birnin Paris- kuma wanda ya dade a kasar Mexico yana bincike a kan kungiyoyi masu fataucin miyagun kwayoyi.
Sanye da jan jan-baki da kuma lu'u-lu'u da matsattsen wandon jeans, ta yi nuni da sanannen hoton "buchona", wata mata da ta shahara wajen soyayyar hamshakin mai sha da aikata laifukan da suka danganci safarar miyagun kwayoyi.
Jami'ar George Mason da ke Guadalupe Correa-Cabrera ta gudanar da bincike a Sinaloa, kasar Mexico, inda kungiyar El Chapo ke gudanar da harkokinta.
Ta fassarar ma'anar buchona da: "Su kan sanya tufafi masu tsada, da rike kananan jakunkunan kawa na Louis Vuitton.
An yi kari ne a kan komai, kuma ta kasance tamkar wancan hoton. Duk dai game da kamani da tiyatar sauya kamanni.''
Daya daga cikin fitattun surorinta, in ji One Correa-Cabrera, shi ne ''kwankwasonta'', wanda ta bayyana a matsayin ''ƙirar kalangu''.
Guzman ya yi amfani da tashin hankali wajen cigaba da jagorantar haramtacciyar kasuwar miyagun kwayoyi tare da amfana da ita, da azurta matarsa da danginsa.
Mutane fiye da 300,000 ne aka kashe a kasar Mexico sun daga shekarar 2006, shekarar da gwamnati ta ƙaddamar da yaƙi da ƙungiyoyin masu fataucin miyagun kwayoyi
Wadanda abin ya rutsa da su sun hada da abokan gabar Guzman, har ma da makusantansa.
An gano gawar daya daga cikin masoyansa a cikin wata mota, kisan kan da aka bayyana cewa wata kungiyar dake suke gaba da shi ne suka aikata.
Sakamakon nuna goyon baya
Lucero Guadalupe Sanchez Lopez, wata tsohuwar farkar Guzman ta gabatar da mummunar shaida a kan shi a lokacin sauraron karar.
An cafke ta a cikin watan Yunin shekarar 2017 a kan aikata laifin tu'ammali da miyagun kwayoyi a kusa da kan iyakar kasashen Mexico da Amurka.
Ta amsa laifinta, kuma an fada mata cewa za ta fuskanci zaman gidan kurkuku na shekaru goma.
Sánchez, mai 'yaya biyu ta bai wa masu gabatar da kara hadin kai.
Sanye da shudiyar rigar fursunoni mai hade da wando, a zauren kotun, ta bayyana yadda mu'amalarsu ta ke da kuma aikinsa a matsayin jagoran kungiyar masu fataucin miyagun ƙwayoyi.
Tana yawan kiftawa cike da razaana. She had a nervous tic, and blinked often. Guzman dake zaune ba da nis aba, da alamu ya kagara, yana ta kallon wani agogon bango.
Coronel na zaune a layi na biyu. Tana jan dogon gashinta da yatsunta, kuma a wannan rana tana sanye da wata rigar jacket mai karan-muski, irin wacce mijinta ke sanye da ita.
Riguna iri daya da suka saka ya nuna karfin igiyar aurensu, in ji William Purpura, wanda shi ne lauyan Guzmán.
Coronel na son isar da sako ga Sánchez ta hanyar aka riga iri daya da ta mijinta a ranar da tsohuwar farkarsa da bayar da shaida a kan sa.
"Habaici ne ga farkar,'' in ji Purpura. "Taba cewa ne: 'Mijina ne."
Bayan bayar da bahasi a kotun, Sánchez ta sake komawa dakin da ake tsare da ita.
Ba da dadewa bayan nan ba, komai reshe ya juye da mujiya a tsakanin matan biyu. An saki Sánchez daha kurkuku yanzu ta samu 'yanci. Coronel na bayan kanta kuma ana tsare da ita ba tare da izinin bayar da beli ba.
Da dama sun kadu game da yadda Coronel ta nuna a lokacin sauraron karar, sun nuna rashin jin dadin su kan yadda ta kasance mai cigaba da goyon bayan mijinta.
Mai sharhi kan al'amuran tsaro Grandmaison ya ce: "Ana yi mata kallon sakarai."
Duk da acewa ba daga wurin Sánchez ba.
Lokacin da lauyanta Heather Shaner, ya shaida mata cewa Coronel na gidan yari, Sánchez bata nuna wata alamar wani jin dadi ba.
A maimakon haka, ta tuno da lauyanta: "Ta ji bakin cikin saboda, ta ce: ''Har ila yau wata uwa ce da zata kasance nesa sa 'yayanta.'"