Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mai ɗaukar hoton da ke fito da kyawun mutanen da ba a damawa da su a cikin al'umma
- Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Wata mai sana'ar gyaran gashi da ta koma sana'ar daukar hoto, da kuma ta ce ayyukanta sun sauya tunaninta game da manufar kyawu, ta dauki kayatattun hotunan mutanen da ake nuna wa wariya a cikin al'umma.
Ta ce ta zabi wannan aiki da kuma irin wadannan mutane da masu daukar hoto ba su cika damuwa da su ba ne saboda ta fito da irin baiwa da kyawun da Allah ya yi musu.
Ta shaida wa BBC cewa: "Mata na zuwa wurina (a matsayina na mai gyaran gashi) saboda suna son su kara kyau, kuma ina taimaka musu,"
"Amma na sani kwarai da gaske cewa kyakkyawar kama na tattare da asali, a wani lokaci boye wasu muhimman abubuwa na jin kwarin gwiwar kai ko wanene.
Daukar hotunan wadanda aka ware
Silvia ta fara aiki a matsayin mai gyaran gashi a kasar Italiya lokacin tana da shekara 17. Kamar sauran mutane, da farko ta dauki sana'ar daukar hoto a matsayin wani nishadi kawai amma daga baya ta zama abin da take matukar kauna.
Lokacin da ta yi bulaguro zuwa kudancin kasar Ethiopia a shekarar 2010, ta tattara bayanai game da kabilu daban-daban na yankin kwarin kogin Omo, kuma ta fahimci cewa 'yan kasashen yammacin duniya masu yawon bude ido na daukar wurin tamkar "wurin ajiyar namun daji amma na mutane".
Ta ce zuwa Afirka ya koya mata ta nemi sanin abubuwa game da mutane kafin ta fara daukar hotunansu.
"Bai kamata masu daukar hoto su rika daukar hoton wadanda suka yi amfani da su a wajen samun wata lambar yabo kan daukar kayatattun hotuna ba, ba tare da sanin wani abu game da su ba.," in ji ta.
Babban aikin Silvia na farko wajen duba abubuwan da suka kamata ta yi da tattara bayanai, sun fara ne a shekarar 2017 kuma ya kai ta har kasar India.
Ta samu karfin gwiwar zuwa can bayan ganin wani hoton wata mata zabiya a shafin sada zumunta a birnin Mumbai kana ta samu labari game da halin nuna wariya da kyama da ake nuna wa irin wadannan mutane (zabiya), da ke sa fata da idanu su rasa sinadaran launi da kuma kwari.
Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, akwai daruruwan mutane zabiya da aka kai wa hari ko kuma aka hallaka a yankin Kudu da Saharar Afirka.
A kasar India, da aka bayyana cewa irin wannan yanayi ya shafi mutane kusan 200,000, ba a cika samun tsangwama da nuna wariya ba, amma kuma mata zabiya na cikin fargabar rasa mijin aure har abada.
Bayan da ta dauki hotunan wasu zabiya 'yan gida guda su uku, Silvia ta kara fadada aikinta - da aka yi wa lakabi da ''Fata'' - kuma ta gana da wata mata a Agra wacce ta Allah Ya tarfa wa garinta nono bayan harin da aka kai mata da sinadarin asid, da akasarin matan da aka kai wa irin wannan hari don kawai sun ki amincewa a yi lalata da su ne.
"Soniya, mace ta farko da aka fara kai wa harin nasinadarin asid da na hadu da ita, mai sana'ar kwalliya ce. Mun tattauna da ita sosai game da ayyukanmu, a cikin natsuwa," in ji Silvia, mai shekaru 45.
"Kafin in hadu da ita, na cika da damuwa saboda ba na son na sa ta rika jin babu dadi, amma a gaskiya tana da saukin kai kuma ta fuskanci abin da ta sa a gaba kuma sai na ga duk tunaninmu daya ne. Burinmu, na lura, duk daya ne - mu wayar da kan jama'a (game da abubuwan da muke fuskanta)."
Silvia ta hada ayyuka biyu, daukar hoton wacce ta rayu bayan watsa mata sinadarin asid, da kuma wacce take zabiya wuri guda.
"Tunanina shi ne na isar da sako kan al'amuran da suka shafi zamantakewa ta hanyar nuna wagegen gibi inda duka abubuwan biyu, dalilin nuna wariya a kansu shi ne fata.
"Dukan su biyu sun rika jin suna da muhimmanci, da kyau da kuma ban sha'awa. Sun damu su san dalilan da suka saka nake son na nuna su."
'Fasaha magani ce'
Silvia ta koma India domin ta cigaba da gudanar da ayyukanta, har ila yau ta dauki hotunan mutane a kasar Iraqi, da Afghanistan da kuma Japan.
Ta damu matuka game da halin kuncin da mutane suka shiga a birnin Bhopal na tsakiyar kasar India, wanda ya ja hankulan kasashen duniya a watan Disambar shekarar 1984 lokacin da tan 400 na sinadarin iska mai guba ta 'methyl isocyanate' ta balle ta fira daga masana'antar 'Union Carbied' mai sarrafa maganin kwari.
Gwamnatin kasar India ta ce mutane 3,500 ne suka mutu a cikin kwanaki kadan da aukuwar bala'in, kana fiye da mutane 15,000 a cikin shekaru bayan hakan, duk da cewa masu fafutika sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 25,000.
Sun ce matsalolin da suka biyo baya sun ci gaba zuwa haihuwar 'yaya da rashin lafiya mai barazanar kisa da wuri, kamar irinsu Samir, da ya kamu da cutar da ta shafi kwakwalwa, da ba ya iya magana ko kuma motsi.
Yana da shekara 18 lokacin da Silvia ta dauki hotonsa kuma ta ce haduwa da shi ta taimaka mata wajen fahimtar girman bala'in.
Ta yi amanna cewa hakan ya kara wa aikinta martaba, amma shi ma ya ba shi wani abu.
"Bayan da na kammala aikin daukar hoton Samiri, sai na fara kuka," a cewatsa. "Fasaha magani ce ga masu fasaha, ga wadanda aka yi aikin fasahar da su, da kuma wadanda za su kalla.
"Na san na bai wa Samir wata rana ta daban, da kuma jin wani sauki."
'Bai ji tsoro ba'
Sauran mutanen da ta hadu da su a kan hanyar tafiye-tafiyenta sun ci gaba da kara wa Silvia kwarin gwiwa.
A kasar Afghanistan wacce yaki ya daidaita, ta dauki hotunan wasu kabilu makiyaya da ke rayuwa cikin lumana a kan hanyarsu ta fatauci da ke kai wa kusa da kan iyakar kasashen Tajikistan da China.
A kasar Japan, ta cika da mamaki matuka game nuna juriya da karfin hali na Koichi Omae, wanda duk da cewa ya rasa kafarsa da hagu a hadarin mota lokacin yana da shekara 23, amma ya koyi sana'ar rawa, kuma ya yi rawa a bikin gasar wasan motsa jiki na nakasasu a birnin Rio.
A kasar Iraqi, inda halayyar nuna kiyayya ga 'yan luwadi ke ci gaba da faruwa, ta kauce wa gargadi da damuwar masu yi wa 'yan yawon bude ido jagora, kuma ta je dandalin shakatawar da ta san 'yan luwadi ke yawan zuwa, inda ta shawo kan daya daga cikinsu ya amince ya zo ya tsaya ta dauki hotonsa a asirce washegari.
"Na ga mutumin da ya dace, kuma na fara magana da shi, ina dariya na kuma samu amincewarsa. Ya yi dar-dari da ni daga farko, amma kuma ba ya jin tsoron game da ko shi wane ne.''
Tun bayan da annobar korona ta hana tafiye-tafiyen kasashen duniya, Silvia na shafe lokacinta tana daukar hotunan kanta da kanta a gidanta da ke Bergamo.
Amma kuma tana shirin fara wani aikin nata - kan muhimmancin da muke bai wa gashinmu.
Tana ci gaba da tuntubar mutanenta kana tana sanar da su game da lokacin da kuma inda ta ke baje kolin ayyukanta, ko a wuraren bikin nunin kayayyaki ko kuma a shafin intanet, da kuma irin martanin da ta kan samu.
Ta ce: "Idan na yi magana game da ayyukana a fadin kasar Italiya a tarukan al'adun gargajiya ko kuma bikin baje kolin hotuna, a kodayaushe ba kan bayar da labarin da ke tattare da hotunan kana in fada musu sunayen mutanen da nake nun awa.
"Ita ce hanyar da nake bi wajen taimaka musu da kuma wayar da kuma fadakarwa game da matsalolin da suke fuskanta."