Princess Latifa: Ƴar sarkin Dubai ta ce tana cikin ƙunci saboda tsare ta da mahaifinta ya yi har shekara 3

Asalin hoton, Princess Latifa
- Marubuci, Daga BBC Panorama
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporting team
'Yar sarkin Dubai wacce ta yi kokarin guduwa daga kasar a shekarar 2018 daga baya ta aike da sakonnin bidiyo na sirri ga abokai inda suke zargin mahaifinta da boye ta, abin da ya sa take tsoron ,akomar rayuwarta.
A cikin wasu hotuna da BBC Panorama ta samu, Gimbiya Latifa Al Maktoum ta ce jami'an tsaro sun ba ta wani magani yayin da take kokarin guduwa ta jirgin ruwa, sannan suka mayar da ita inda take tsare.
Abokanta sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta shigo ciki.
Dubai da Hadaddiyar Daular Larabawa a baya sun ce tana cikin aminci cikin kulawar danginta.
Tsohuwar wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan 'yancin kare hakkin dan adam, Mary Robinson, wacce ta bayyana Latifa a matsayin budurwa mai wuyar sha'ani bayan haduwa da ita a 2018, ta ce danginta sun yi mata wayo ".
Tsohon Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'Yancin Dan Adam kuma shugaban kasar Ireland ya bi sahun kiraye-kirayen da ake yi na kasa da kasa don gano halin da Latifa take ciki da kuma inda take.
"Na ci gaba da kasancewa cikin matukar damuwa game da Latifa. don haka ina ganin ya kamata a binciki wannan lamari ," inji ta.
Mahaifin Latifa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, daya ne daga cikin shugabannin kasashe masu arziki a duniya, mai mulkin Dubai kuma mataimakin shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
An nadi bidiyon tsawon watanni, a wata karamar waya da aka bawa gimbiyar a asirce kimanin shekara guda bayan kama ta da kuma komawa Dubai.
Ta nadi bidiyon ne a makewayi, domin nan ne kadai inda take da kofar da za ta iya rufewa.
A cikin sakonnin, ta yi bayanin yadda:
- • Ta yi rigima da sojojin da suka kamo ta daga jirgin ruwan, "suna ta hargowa da faɗa" tana cizon hannun ɗaya daga cikinsu har sai da ya tsala ihu.
- • Bayan an mata wata allura sai ta rasa inda take, aka sa ta a wani jirgi, bata farka ba sai da ta sauka a Dubai
- • An tsare ta ita kadai ba tare da samun damar taimakon likita ko na shari'a ba, a wani wuri rufe da tagogi da kofofi, kuma 'yan sanda ke tsare da ita

Wata kawarta ta bawa sashen binciken ƙwaƙaf na BBC Panoma labarin kama Latifa, tare da wata yar uwarta Marcus Essabri da wani mai fafutuka David Haigh, wadanda dukkansu ke fafutukar ganin an sake ta.
Sun ce sun dauki wannan mataki na sakin bayanan ne saboda sun damu da lafiyarta.
Sune kuma suka gana da Latida a inda ake tsare da ita a Dubai, bisa kulawa yan sandan dake gadinta.
A karan kanta, Panaroma ta yi bincike, kuma ta gano ind ake tsare da Latifa.

Sheikh Mohammed ya gina katafaren birni mai matukar kyau, amma masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce ba a jure adawa, sannan tsarin shari'a na nuna wariya ga mata.
Yana da wurare masu yawa na tseren dawakai, sannan lokaci lokaci yakan je tarukan sarakai inda aka ɗauke shi hoto tare da Sarauniya Elizabeth II.

Asalin hoton, PA Media
Amma ya gamu da suka mai tsanani kan Gimbiya Latifa da kuma kishiyar mahaifiyarta Gimbiya Haya Bint Al Hussain, wacce ta gudu zuwa Landan a shekarar 2019 tare da 'ya'yanta biyu.
Tserewa a jirgin ruwa.
Latifa, mai shekaru 35 yanzu, ta fara kokarin guduwa tana da shekaru 16 amma sai bayan da ta tuntubi dan kasuwar nan na Faransa Herve Jaubert a shekarar 2011.
An shirya tserewar ne tare da taimakon Ms Jauhiainen.
A ranar 24 ga watan Fabrairun 2018, Latifa da Jauhiainen sun ɗauki kwale-kwalen da za su iya cuwa-cuwa da zuwa jirgin ruwan kasa da kasa, inda Mr Jaubert ke jira a cikin jirgin ruwan da ke da tutar Amurka.
Amma bayan kwana takwas, daga Indiya, sai kwamandojin dakarun Hadaddiyar Daular Larabawa suka shiga jirgin ruwan.
Ms Jauhiainen ta ce gurneti da hayaki ne suka tilasta mata da Latifa ficewa daga cikin gidan wankan da ke kasan bene, a nan ne aka rike su da bindiga.
An dawo da Latifa zuwa Dubai, kuma ba a sake jin duriyarta ba har yanzu.
Ms Jauhiainen da ma'aikatan da ke cikin jirgin sun sami 'yanci bayan sun kwashe makonni biyu a tsare a Dubai.
Gwamnatin India ba ta taba cewa komai game da rawar da taka wajen kama su ba.

Asalin hoton, Princess Latifa
Kafin yunƙurin tserewar ta na 2018, Latifa ta ɗauki wani bidiyo wanda aka saka a YouTube bayan an kama ta.
Ta ce, "Idan kuna kallon wannan bidiyon, ba abu mai kyau ba ne, ko dai na mutu ko kuma ina cikin mummunan yanayi."
Wannan shi ne ya tayar da hankalin duniya sosai tare da yin kira da a sake ta.
Hadaddiyar Daular Larabawa ta fuskanci matsin lamba domin bayar da bayanan halin da take ciki, kuma an shirya ganawa da Ms Robinson.
Ganawa da Robinson
Ta tashi zuwa Dubai a watan Disambar 2018 bisa bukatar kawarta, Gimbiya Haya, don cin abincin rana inda Latifa ma ta kasance.
Robinson ta fada wa Panorama ita da Gimbiya Haya an gabatar musu da bayanai dalla-dalla game da rashin lafiyar Latifa, yanayin da ba ta da shi.
Ta ce ba ta tambayi Latifa game da halin da take ciki ba saboda ba ta son "kara mata yawan tashin hankali"
Kwana tara bayan cin abincin rana, ma'aikatar harkokin waje ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta buga hotunan Ms Robinson tare da Latifa, wanda ta ce ya tabbatar da cewa gimbiyar tana cikin koshin lafiya.
Ms Robinson ta ce: "An yaudare ni musamman lokacin da hotunan suka fito a bainar jama'a.
Hakan ya ba ni mamaki matuka ... Na yi matukar mamaki."
A shekarar 2019, an bayyana tashin hankalin da ke tsakanin dangin mai mulki a Dubai a gaban Babbar Kotun Ingila bayan da daya daga cikin matan shehun, Princess Haya, ta gudu zuwa Burtaniya tare da 'ya'yanta biyu tare da neman umarnin kariya.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar da ta gabata, Babbar Kotun ta fitar da jerin hukunce-hukuncen bincike na gaskiya wanda ta ce Sheikh Mohammed ya ba da umarnin tare da kitsa yadda za a dawo da Latifa da karfi a 2002 da 2018, gami da sace ta da aka yi daga Burtaniya ba bisa doka ba a shekarar 2000 ta kanwarta Gimbiya Shamsa.
Abokan Latifa sun yi fatan cewa hukuncin da kotun ta yi a watan Maris din shekarar da ta wuce na cewa Sheikh Mohammed ba mai gaskiya bane, na iya taimakawa.
Ta ce ta yi tunani sosai game da sakin sakonnin bidiyon a yanzu, amma ta kara da cewa: "Ina jin cewa za ta so mu tsaya mata, kuma kada mu karaya."










