Matar da ke ƙoƙarin gano sunayen ƴan Afirka 1,000 da suka nutse a teku

Asalin hoton, AP/Salvatore Cavalli
- Marubuci, Daga Linda Pressly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A ranar 18 ga watan Aprilun shekara ta 2015 ne 'yan gudun hijira da 'yan cirani fiye da 1,000 suka bar kasar Libya makare cikin wani kwale-kwalen kamun kifi a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai.
A cikin duhun dare kan tekun Bahar Rum ne kwale-kwalen ya nutse. Amma kuma ba a manta da wadanda suka nutse din ba - shekaru biyar da suka wuce wata tawaga wacce wata kwararriya a fannin binciken ƙwayoyin halittun gawa ke ta fafutikar aikin gano sunayensu.
"Akwai gawawwakin da ke bukatar a gano su, ka gano su - wannan shi ne daya daga cikin dokokin fannin binciken ƙwayoyin halittu,'' in ji Dr Cristina Cattaneo, farfesar kimiyyar ilmin ƙwayoyin halittun ɗan adam a Jami'ar Milan.
Abu mafi daukar hankalin Cattaneo shi ne saka wa mamaci suna. Wannan ba wani abu ba ne idan aka samu hadarin jirgin sama a kasashen Turai, ta ce.
Don haka me zai sa ya zama da bambanci da 'yan ci rani matafiya a kwale-kwale?
"Akwai allunan alamun sunayen gawawwaki a makabartun kasashen Turai dauke da alamar 'babu suna' da aka rubuta da harshen Italiyanci a gurbin suna, da kuma kwanan wata na mutuwa, shi kenan. Ina ga wannan abin bakin ciki ne. Babban cin mutunci ne da wani zai taba gani.''

Asalin hoton, Getty Images
Cattaneo da tawagarta sun bude wa mutane fiye da 350 da suka ɓace kundi, wanda 'yan uwansu suka yi amanna cewa me yiwuwa sun mutu ne a hadarin jirgin ruwa na 18 ga watan Afrilun shekarar 2015.
"Hakan na nufin iyalai 350 sun tunkari wasu hukumomi suna neman bayanai game da 'yan uwansu da suka mutu a hadarin.
Shekaru biyar sun wuce, kuma wadannan mutane har yanzu suna neman 'yan uwan nasu,'' ta ce.
Mutanen da suka hau wannan tsohon kwale-kwale a Libya sun fito daga kasashen Afirka da dama da suka hada da Senega da Mauritania da Najeriya da Ivory Coast da Saliyo da Mali, da Gambia da Somalia da Eritrea.
Akwai 'yan kasar Bangladesh ma a ciki. Daga bisani ne za a gurfanar da matukin kwale-kwalen dan kasar Tunisia tare da wani dan kasar Syria, kan aikata laifin fataucin mutane da kuma kisan kai a wata kotun kasar Italiya.

Bulaguron mai cike da hadari ya fara ne da asubahi a gabar tekun Garabulli da ke gabashin birnin Tripoli.
Wani kwale-kwalen kamun kifi mai tsawom mita 20, da aka yi wa fentin shudi ya yi tangal-tangal a kan igiyar ruwa.
A gefensa an yi rubutun Larabci aka saka "Allah ya yi Albarka ."
Tun da misalign karfe uku na dare Ibrahima Senghor yake ta jiran shiga kwale-kwalen.
Ya taso ne daga kasar Senegal zuwa wannan gabar teku a Libya tare da sauran matasan daga kauyensa, amma dandazon fasinjojin da ke fatan shiga kwale-kwalen ya raba shi da su.
"Muna cikin tawaga ta 10 mai dauke da mutum 100,'' ya tuna." Tawaga bakwai suka shiga. Ina cikin tawaga ta takwas.
"Karin wasu mutane sun iso a cikin wata babbar mota mai na'urar sanyi. Su ma sun shiga cikin kwale-kwalen. Muna iya ganin yadda ya makare, nan ne masu fataucin suka sanar da cewa kwale-kwalen ya cika. Na ce 'Hakan ba zai yiwu ba,' na dage ni ma sai na shiga.''
Amma kuma masu fasa-kwaurin ba su amince Ibrahima Senghor ya shiga ba. Ya biya kudi kwatankwacin dala 1,000 na kudin kasar, amma masu fataucin mutanen sun fi bai wa wadanda suka biya da dalar Amurka fifiko.
Abokan Ibrahima tuni suka riga suka shiga. An bar shi a bakin teku shi da wasu ragowar mutume 300, suna kallon kwale-kwalen na kama hanya.

Asalin hoton, Ibrahima Senghor
Kwale-kwalen ya kama hanya. Amma daga bisani ya sake juyowa. Matukin ya sanar da cewa kwale-kwalen ya cika fiye da ƙima. Mai fasa-kwaurin mutanen ya umarce shi da ya fita - ya ce muddin matukin bai fita ba zai kashe shi nan take.
Mai fataucin mutanen ya fito da bindigarsa ya yi harbi a sama. Har sai da misalin karfe 10 da safe ne sannan muka rika hango kwale-kwalen daga nesa.''
Abdirisaq - daya daga cikin 'yan kasar Somalia 24 ne da ke cikin kwale-kwalen da ya tunkari tekun kasashen waje. Bayan da suka matsu su bar kasar Libya, shi da abokansa sun kutsa da karfi daf da tashin kwale-kwalen.
"Hankalina ya kwanta saboda zan bar yakin basasar kasar Libya a baya,'' ya tuna abin da ya ce a lokacin.
Bayan hambare gwamnatin Muammar Gaddafi a shekara ta 2015, Mulki a kasar Libya ya kasance cike da hadari.
'Yan cirani sun kasance cikin hadarin yiwuwar a sace su - ana yawan yin garkuwa da su cikin wani mummunan yanayi, kana ana tilasta musu biyan kudade masu yawa kafin a sake su.
Abdirisaq bai yi tunanin ko wannan kwale-kwale na da ingancin bi ta kan tekun ba - ya dai san cewa ya zabi hanyar sayar da rai ne.
"Ban damu da batun kariya ba,'' ya ce. ''Na san dai ko a mutu ko a yi rai ne - ko mu isa kasashen Turai ko kuma mu nutse.''
Yayin da suke tunkarar babban teku, Abdirisaq ya fara barci. Da yamma kamar kimanin kilomita 100 da tafiya kan tekun amma har yanzu kusa da Libya fiye da kasashen Italiya ko Malta, kwale-kwalen ya fara yoyo. Matukin ya fara kiran neman taimako.
Kungiyar Tarayyar Turai ta fara gudanar da aikin ceto, don haka wani katon jirgin ruwa mai launin baki 'King Jacob' ya fara isowa wurin da misalin karfe 11 na dare.
Ya kunna fitilunsa. Wannan gagarabadon 'King Jacob' ya kashe inginsa ya fara aikin ceto, kuma wannan kwale-kwalen da ke makare da jama'a ya yi kokarin matsawa kusa.
Kwale-kwalen da ke tangal-tangal saboda wasu fasinjojin da ke ciki sun tsorata sun dawo suna zaune a gefensa kusa da King Jacob.
''Daga nan babu zato - matukin ya tuka kusa da shi, daga nan ne kwale-kwalenmu ya tunkuyi babban jirgin ruwan,'' in ji Abdirisaq.
"Mun yi karo da jirgin ruwan fiye da sau daya. Daga nan muka gogi gefensa. Bayan haka, ba mu iya tsayawa a kan ruwan ba sai muka kife.''

Abdirisaq - kwararre wajen iya ninkaya - ya samu kansa a karkashin kwale-kwalen a kasan ruwa.
Lokacin da aka jefar da mu cikin teku, mutane na ta rike ni. Kayana duk sun yayyage yayin da nake kokarin kubutar da kaina,'' ya ce.
Lokacin da ya samu ya yo sama, an samu hatsaniya.
"Na rika jin ana ta ihu da kuwwa. Mutane na ta kokarin kamo ni, don haka na yi kokari na yi iyo na fice daga cikin taron mutanen - Na galabaita sosai. Na yi kokarin bin bayan babban jirgin ruwan. A daidai lokacin da na soma yanke kauna ne, sai kawai suka jefo min majanyin ceto."
Bayan galabaitar da ya yi, Abdirisaq ya daure da kyar ya hau kan tsanin da ke makale a jikin, yana daga cikin mutane 28 da suka tsira.
Da sanyin asubahin Lahadi, Guiseppe Pomilla - wani likitan sa-kai ya iso cikin duhu daga Sicily a cikin jirgin gabar tekun Italiya.
"Akwai wani tsit da aka yi - babu abin da ke motsi,'' ya tuna.
Har sai bayan da Pomilla ya hau karamin kwale-kwalen, da ya kawo shi kusa da saman ruwa, nan ne ya rika cin karo da gawawwakin da suka taso sama.
"Akwai gawawwaki da yawa da suke yawo a kan igiyar ruwa.''
Shi da abokin aikinsa sun rika kamo wadanda ke yawo a saman ruwan don su ga ko akwai masu sauran numfashi.
Daga nan ne suka ji wani ihu. Tare da taimakon hasken fitila, sun iya gano wani mutum inda suka janyo shi cikin jirgin ruwan.
"Cike yake da farin ciki - ya kasa yin shiru. Ya tambaya ko shi ni dan kasar Italiya ne, ya kuma ce daga yau zai fara kaunar kasar Italiya har abada.''
Pomilla ya taimaka wajen ceto karin wani dan cirani guda a wannan dare.
"Mun dauka ma ya mutu. Idanuwansa a bude kuma ba ya iya motsi. Daga nan sai ya kama hannuna.''
"Wadannan mutane biyu da muka ceto… Ina ta mamakin watakila akwai sauran wani mai rai - wani wanda da ya kasa yin ihu ko kuma motsi da ba mu iya kai wa ga su ba.''

Asalin hoton, Getty Images
A lokacin da aka bayar da rahoton cewa mutane 800 ne a cikin kwale-kwalen kamun kifin da ya yi hadari a shekara ta 2015, adadin yawan 'yan gudun hijirar da 'yan cirani da suka rasa rayukansu har yanzu na haifar da damuwa.
Gwamnatocin kasashen Turai sun yi wata ganawar gaggawa. Firai ministan Italiya Matteo Renzi, ya ce za su bukaci lalubo kwale-kwalen da ya kife, don samo gawawwakin a yi musu jana'iza.
Daga bisani an bugo wa Dr Cristina Cattaneo waya daga ofishin kwamishiniya mai lura da harkokin mutanen da suka bace.
"An kwaso gawawwaki 249 a kusa da kwale-kwalen. Kuma mun yi aiki a kan wannan har sai bayan shekara guda, lokacin da firai ministanmu ya yanke shawarar janye kwale-kwalen,'' ta ce.
An kafa wata hukuma - wannan shi ne karon farko da aka taba janyo kwale-kwalen 'yan cirani daga zurfin kasan tekun Bahar Rum.
An yi amfani da butum-mutumi wajen gano kwale-kwalen a cikin zurfin mita 370 na teku. Sojojin ruwa masu ninkaya na Italiya sun ajiye babban furen kallo a kan kwale-kwalen, kafin a dago shi ta hanyar amfani da kugiya ta musamman.

Asalin hoton, Italian Navy


Asalin hoton, Italian Navy
A ranar 27 ga watan Yunin shekara ta 2016, ya bullo ta saman tekun Bahar Rum.
Wannan fasaha ta lakume kudi kimanin euro miliyan tara da rabi (9.5) kwatankwacin fam miliyan dari takwas da dari shida (£8.6m).
An kai kwale-kwalen sansanin sojin Melilli a kan tsibirin Sicily, inda dakarun sa-kai masu aikin kwana-kwana da kwararru a fannin binciken kwayoyin halitta da jikin dan adam ke jira.
"Na tuna yin tafiya a gabar teku tare da wasu karnuka, ina kallo ta gefen idona ana janyo kwale-kwalen 'yan cirani,'' ta ce.
"Kwale-kwalen namu karami ne. Kuma saboda janyo shin da aka yi, yana da manyan huda biyu a gefe inda sojojin ruwan suka toshe don kada wani abu ya fado daga ciki.… wani lokaci ne mai ban al'ajabi.''

Asalin hoton, Italian Navy
Cikin kwanaki 12 da aka shafe, an umarci masu aikin kwana-kwana 348 daga ko ina a fadin kasar Italiya da su ciro gawawwakin mutanen da suka makale a cikin kwale-kwalen mai launin shudi.
"Ka yi tunanin yadda dandamalin ya cika da gawawwaki,'' Cattaneo na tunawa - gawawwakin da ba a iya gane fuskokinsu, bayan shafe shekara guda a karkashin teku.
Suna kama da 'yar tsanar da aka saka wa tufafi. Akwai wasu gawawwaki biyar ko shida wasu kan wasu.
Kuma na tuna da yadda na dauki abin a raina cewa ban taba ganin - ban taba tunanin - abu irin wannan ba."
Wannan wani sabon wuri ne ga su kan su jami'an kwana-kwanan. Cattaneo ta ba su dokoki na musamman.
"Su yi taka tsan-tsan su ga abubuwan da ke hade wuri guda. Misali, idan akwai kai da gangar jiki, su duba idan akwai wata fata ko jijiya da ta hada su, ka da a bar komai. Muna magana kan gawawwakin da suka rube."

Asalin hoton, Italian Fire Brigade
Aiki ne mai cin rai. Sanye da cikakkun kayan aiki da rigunan kariya, ga kuma yanayin sanyin bakin teku a tsibirin na lokacin bazarar a Sicily ya kai ma'aunin 40C, yanayin ya tsananta.
Ma'aikatan kwana-kwanan suna aiki ne na mintoci 20 ko wannensu, kuma masana halayyar dan adam kan yi musu huduba a kowace yamma.
Haka kuma, Cattaneo da 'yan tawagarta na gudanar da aikin bincike ne kan gawawwakin.
"Wadannan gawawwaki da dauke da duka takardunsu dinke a jikin tufafinsu. Don haka sai mun yi taka tsan-tsan wajen yankar yanka gefen tufafin, saboda a nan ne za a samu takardun, katin shaida, wasiku, da wasikun soyayya - akwai takardar shaidar jarrabawa ta wani yaro mai shekara 14.
"Kuma ina iya tunawa daya daga cikin gawawwakin - wannan mai shekara 18 ya daure wani tsumma a jikin rigarsa wanda ciki akwai wani abu mai kama da kasa."
Abinda ke ciki kenan.

"Wannan ya tayar min da hankali, saboda abin da na saba yi kenan ni ma…na girma a kasar Canada, amma na kan zo kasar Italiya lokacin bazara.
"Kuma a kowace shekara idan na koma, na kan cika aljihuna da ganyaye daga kasar da nake kauna wato Italiya. Wannan ya yi daidai da irin nawa tunanin."
Binciken ya gano wani abu mai sarkakiya.
"Mun gano wani karamin hakori na karamin yaro amma kuma babu kasusuwan yaron, da hakan ya nuna cewa akwai akalla yaro guda a cikin kwale-kwalen. Amma wadanda suka tsira sun yi magana kan matan da suka zo a cikin babbar mota dauke da wadannan kananan yara, wadannan jarirai.
"Amma babu wasu kaya da suka nuna shaidar wadannan mata. Don haka a yanzu kwale-kwalen kenan na dauke da matasa, kananan yara da kuma maza manya."
Akwai bayanai masu cin karo da juna game da cewa akwai mata da kananan yara cikin kwale-kwalen.
Ibrahima Senghor, da bai shiga ba, amma an bar shi a gabar teku ya ce ya gan su. Amma Abdirisaq, dan kasar Somalia da ya kubuta daga hadarin kwale-kwalen, bai iya tuna ganin wasu mata a ciki ba.

Asalin hoton, Italian Navy
Masu fataucin mutane sun cika kowane wuri da tarin jama'a a cikin kwale-kwalen. An samu kwarangwal har a karkashinsa. Hatta wurin da ake ajiye Sarkar turken jirgin ma duk gawawwakin mutane ne.
Wasu gawawwakin da aka fitar daga cikin kwale-kwalen an binne su. Kana an kai ragowar 30,000 da suka rududduge zuwa dakin bincike na Milan.
"Ka yi tunanin a ce an saka kasusuwan ko wace gawa daga mutane 500 a cikin babban buhu kana a girgiza a sake juyewa,'' ta ce. '' Abin da muke ta faman yi kenan yanzu.''

Asalin hoton, Getty Images
Aikin tantance matattun ya saka Cattaneo cikin wani tunano mata wasu abubuwa.
"Ina kan hanya dauke da duwatsu da tsakuwowi kana ina neman kananan kasusuwa. A kowace kusurwa, na kan tuna na ga kashi, ashe dutse ne, haka abubuwan suka cigaba da faruwa.''
A ganin Cattaneo, saka wa wadanda suka bace suna na da muhimmanci saboda akwai mutanen da ya kamata a mutunta ransu, har ma da wadanda ke alhinin rabuwa da su.
"Dole a tantance wadanda suka mutu, ba don kawai a shawo kan matsalar aikata laifi ba, ko kuma mutunta wadanda suka mutu ba, amma don wani abu da ya kamata a yi don lafiyar wadanda ke raye,'' ta ce.
"Ina jin yana da sauki a yi tunanin cewa rashin sani ya fi sanin cewa ya ko ta mutu zama abin damuwa. Muddin ka riga ka san cewa sun mutu, sannan ne za ka fara jimami.''

Baya ga aikin binciken da Cattaneo ke yi, kwamitin bayar da agaji na kasa da kasa (ICRC) ya fara gudanar da binciken gano 'yanuwan wadanda suka mutu a hadarin kwale-kwalen na dare 18 ga watan Afrilun shekara ta 2015.
"Ba ma bukatar kawai jiran mutane su zo gare mu, amma mu za mu neme su, mu gano inda suke neman wani, kana mu tattara bayanai game da ko wannensu," in ji Dr Jose Pablo Baraybar, jami'in binciken halittun dan adama na hukumar ta ICRC, kana wani kwararre a fannin bincike kan wadanda suka bace a kasashen Srebrenica, Rwanda, da kuma kasarsa ta Peru.
Baraybar ya zagaya aiki a kasashen Mauritania da Senegal don ganawa da iyalan wadanda suka tabbatar cewa 'yanuwansu na cikin kwale-kwalen da ya nutse, suka debi kwayoyin halittarsu, suka kuma nadi bayanai daga gare su game da wadanda suka bace - da duk wani abu da zai taimaka wajen gano su.
Ya kuma gana da shaidu kamar su Ibrahima Senghor, wanda ya koma gida Senegal.
"A ko da yaushe za ka iya samun wani wanda ya shaida lamarin kuma ya kubuta,'' in ji Baraybar.
"Kana wadannan bayanai na da matukar muhimmanci wajen gano takamaimen sunayen fasinjojin. Yanzu mun samu sunaye kusan dari.
"Sai dai abin takaicin aikin akwai tafiyar hawainiya. Don haka, nasara ta farko ta nuna cewa adadin mutanen da ke cikin kwale-kwalen tsakanin 1,050 zuwa 1,100 ne."
A takaice za a iya cewa kashi 30 bisa dari fiye da adadin 800 da aka yi kiyasi sun bace a shekara ta 2015.

Ibrahima Senghor ya bai wa kwamitin na ICRC ibayanai game da abokansa da suka bace daga yankinsu na Kothiary, a gabashin kasar Senegal.
"Akwai mutane uku da na sani, daya ma'aikacina ne. Tun bayan da muka bar gida kullum muna tare - mun shafe makonni a cikin hamada, muna tare har zuwa lokacin da muka isa gabar tekun Libya,'' ya tuna.
Ibrahima Senghor ya sayar da komai nasa - da suka hada da Saniya - saboda ya samu ya yi wannan bukaguro zuwa Turai.
A ranar 18 ga watan Afril una shekarar 2015 ya yi matukar bakin cikin cewa abokansa sun shiga kwale-kwalen ba tare da shi ba. Amma lokacin da ya samu labari game da hadarin ya yanke shawarar komawa kauyensu.
"Na zauna a gida har na tsawon watanni biyu ba tare da fita waje ba. Kowa ya zaci na haukace ne. Amma saboda da farko ban samu tafiya ba, sannan ba zan iya fita in yi ido hudu da 'yan uwan abokaina da suka nutse ba. Har yau idan muka kalli juna mukan fashe da kuka,'' ya ce.
Samun dangin wadanda suka bace a gidajensu na da wahalar gaske, amma Cristina Cattaneo na tunanin za a iya yin wani abu a Turai.
Ta yi amanna 'yan cirani da dama na da 'yanuwa da suka riga suka ketare tekun na Bahar Rum, ko suka bi ta hanyar kasa zuwa Paris, Berlin da kuma London.
Don haka tana ganin za a iya bude ofisoshi a fadin nahiyar inda wadanda ke neman wadanda suka bace - ba sai lallai dangin 'yan ciranin ba - za su iya zuwa.
Hakan zai iya bayar da damar tattara bayani daga masu bincike, kamar na kwayoyin halittu da nayanai hakora, daga abinda aka tattara daga iyalansu.
Cattaneo ta san cewa wannan zai yi aiki saboda an taba yi a baya. Bayan hadarin jiragen ruwa biyu dauke da 'yan cirani a tekun na Bahar Rum a shekarar 2013, an gayyaci iyalan wadanda suka bace zuwa biranen Rome da Milan don a yi musu tambayoyi da samun bayanai. Mutane fiye da 40 da suka bace ne aka gano.

Duk da cewa tafiya daga Arewacin Afirka da tsallake tekun Bahar Rum na da matukar hadari ga 'yan cirani a fadin duniya da aka yi kiyasin cewa an yi asarar kusan mutane 20,000 tun daga shekara ta 2014, halayyar kasashen Tura ikan 'yan cirani ta kara tsauri, kana kudaden tafiyar da ayyukanta sun kara zama da matukar wahalar fitarwa.
Cattaneo da tawagarta sun cigaba da gudanar da aikinsu na sa kai kan ragowar abinda suka samu daga gawawwakin da aka kwankwale daga cikin kwale-kwalen, amma aikin na su zai fi yin sauri idan suka samu tallafin kudi.

Asalin hoton, Getty Images
Abdirisaq, matashi dan kasar Somalia da ya rasa abokansa amma ya kubuta daga hadarin kwale-kwalen na ranar 18 ga watan Afrilun shekarar 2015, na kokarin gina sabuwar rayuwarsa a arewacin Turai.
"Wani lokaci na kan tuna abubuwan da suka faru. Na samu kaina - na gode Allah da na kubuta. Amma halin da na shiga a cikin kwale-kwalen abu ne da zan iya mantawa,'' ya ce.
Abdirisaq ya san cewa kwale-kwalen an janyo shi daga karkashin tekun. Amma bai san faman da Cattaneo da kwamitin na CRC suka yi ba na tantance sunayen duka mutanen dake ciki, har sai da BBC ta tuntube shi.
"Abin farin ciki ne ka san cewa akwai mutanen da ke kokarin gano yadda abokaina suka mutu a wannan rana,'' ya ce.
"Zai taimaka min in san cewa an gano gawawwakinsu. Zan taimaka wa likitoci wajen aikin da suke yin a gano abokaina.''
"Matattu na fada maka yadda suka rayu da kuma yadda suka mutu,'' in ji Cattaneo.
"Kuma yadda suka mutu na nuna maka yadda suka sayar da rayukansu, halin da suka shiga.
Ina ga yana da muhimmanci ka san wannan. Kuma idan ka shaida wannan, zai sauya tunanika har abada.''

Asalin hoton, Colin Freeman











