Covid-19: Hanyoyi bakwai da za a bi domin yin bikin Kirsimeti lafiya a lokacin annoba

Friends toasting while wearing facemasks and keeping a safe distance from each other

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Annobar za ta mayar da bikin Kirsimeti wani yanayi na daban ga mutane da dama
    • Marubuci, Daga Laís Alegretti da Paula Adamo Idoeta
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil

Annobar cutar korona na shirin mayar da bukukuwan Kirsimetin bana zuwa wani yanayi na daban.

Bikin al'ada wanda mutane da dama ke haɗuwa da iyalai masu shekaru mabambanta shi ma wani lamari ne da za a yaɗa cutar korona wacce kawo yanzu ta yi ajalin kimanin mutum miliyan daya da rabi a faɗin duniya.

Ga mutane da dama, hanya ɗaya da za su tabbatar da ba su yaɗa cutar ba ita ce kar a yi bukukuwa a waje ɗaya a tare.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayar da shawarar cewa mutane su yi amfani da fasaha su ga junansu ta bidiyo bana.

People wearing Christmas hats and opening presents online

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, WHO ta bayar da shawarar mutane su gana da juna ta intanet

Amma ga mutanen da za su haɗu da wasu mutanen daban waɗanda ba tare suke zaune ba, akwai wasu matakai da za su iya ɗauka waɗanda za su taimaka wajen taƙaita haɗarin yaduwar cutar, kamar yadda likitoci suka nuna.

1. A mayar da bikin Kirsimeti ƙwarya-ƙwarya kuma taƙaitacce

Rage yawan mutane, sannan abu mai muhimmanci rage cakuɗuwar mutanen gida ɗaya da na wasu gidajen lokacin bukukuwan zai rage yawan mutanen da za su kamu da korona.

Haka kuma, gajarta lokacin da mutanen za su shafe tare, zai taƙaita haɗarin watsuwar cutar ta korona.

Kamar yadda firaiministan Birtantiya Boris Johnson ya fada: "Karamin bikin Kirsimeti zai kasance mara hadari, sannan takaitaccen bikin kirsimeti shi ne Kirsimeti mara hadari."

"Lokaci ne da za a hadu da iyalai kadan. Kar a hadu da 'yan uwa da yawa, da mutanen da suka wuce 10", a cewar Dakta Juliana Lapa, wata ƙwararriya kan cututtuka masu yaduwa a Jami'ar Brasilia a Brazil.

Takaitacciyar ziyara da bayar da tazara da sanya ƙyallen rufe fuska za su taimaka sosai ga duka ɓangarorin da ke son haɗuwa, a cewarta.

matakan kariya daga cutar korona a lokacin kirsimeti

Wani abokin aikinta, Dakta Estevão Urbano ya jaddada cewa mutane masu shekaru da masu cututtuka, kamar masu fama da matsalar kiba, da ciwon suga da hawan jini da matsalar huhu - ya kamata su nisanci shiga taro.

"Su ne mutanen da ya kamata a killace kuma suke bukatar kulawa a wannan lokaci, amma ya ma kamata su yi taka tsan-tsan fiye da kowa," a cewarsa.

2. Zama a waje mai iska

Ko da iska mara yawa ma tana tafiyar da ƙwayar cutar da ke dauke da korona.

Don haka, lambuna da rumfuna da ma baranda masu faɗi su ne wuraren da suka fi dacewa a gudanar da bukukuwa.

Idan za ku yi taro a cikin ɗaki, to a bar ƙofofi da tagogi a buɗe.

A cewar cibiyar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Amurka, wata dabara mai tasiri ita ce amfani da fankar taga, wacce aka ajiye ta a taga cikin aminci, ta yadda za ta ringa zuƙe iskar cikin ɗaki zuwa waje.

Hakan zai taimaka wajen shigar da iska mai tsafta cikin dakin ta sauran tagogi da kofofi, ba tare da samar da iskar da ta cunkushe a dakin ba."

matakan kariya daga cutar korona a lokacin kirsimeti

3. Takunkumi da bayar da tazara

Kwararru sun ba da shawarar sanya kyallen rufe fuska a kowane lokaci, in ban da lokacin cin abinci ko shan wani abu.

Sun ce hakan na da muhimmancin ne tun da cutar korona tana yaɗuwa ne ta hanyar ƙwayoyin da ke yawo a iska idan muka yi tari ko dariya ko magana, sun kuma ba da shawarar a ringa rage sautin kida, ta yadda ba wanda zai bukaci daga murya idan zai yi magana kafin a ji me zai ce.

Babu daya daga cikin wadannan matakan na sama da zai maye gurbin ba da tazara tsakanın mutanen da ba a waje daya suke zaune ba.

matakan kariya daga cutar korona a lokacin kirsimeti

4. Kowa ya ci abinci shi kadai

Lokacin cin abinci zai ya zama mai haɗari sosai, tun da idan mutane suka hadu za su cire takunkumansu domin cin abinci.

Ya kamata su lura ka da su yi amfani da cokula da ludaya daya da kofunan shaye-shaye, sannan ƙwararru sun ba da shawarar a ringa cin abinci daban-daban, da ɗiban abinci daya bayan daya - iyali daya su ci su tashi sai wasu su zauna.

Idan akwai isassun dakuna da tebura, wannan ne lokacin da za a yi amfani da su.

Christmas dinner

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A guji yawan surutu yayin cin abinci a bikin Kirsimeti

"Yana da muhimmanci a dauki duk wanda bai sa kyallen fuska ba a matsayin wanda zai iya yada cutar, saboda mutane da ba sa nuna alama su kan iya daukar cutar ba tare da sun sani ba," a cewar Jaques Sztajnbok, mai kula da cibiyar ba da kulawa ta musamman a asibitin Emílio Ribas a Sao Paulo, Brazil.

5. A guji yin tafiye-tafiye

Ƙwararru kan cututtuka masu yaduwa sun amince cewa rashin tafiye-tafiye shi ne mafi alheri.

Amma idan har dole sai ka yi balaguro, tafiya a motar gida shi ne ya fi fiye da amfani da ababen hawa na haya inda za a hadu da ɗumbin mutane.

6. Idan kana da alamun cutar, zauna a gida

Idan ba ka killace kanka ba gabanin Kirsimeti, yi kokari a yi maka gwaji 'yan kwanaki kafin taron da kake shirin zuwa.

Sannan ka kula sosai da kanka dangane da alamun cutar Covid-19 da za ka iya nunawa.

An elderly man talks to his family via conference call

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dr Estevão Urbano ya ce: Yana da muhimmanci sosai ga mutanen da suka manyanta su fi ɗaukar matakan kariya

Yana da muhimmanci ka dauki dukkan alamun da matukar muhimmanci ko yaushe.

Mutane da dama za su ce, tari ne fa kawai, kawai 'yar mura ce da majina, to amma dole ne ka dauke su da muhimmanci ka kuma zauna a gida. Yanayin zai iya zama mai hadari sosai ga wasu," kamar yadda Dokta Juliana Lapa ta fada.

7. Kada ka yi sassauci da daukar matakai

Bayan shafe watanni ba a haɗu ba, mutane za su iya bukatar haduwa da juna don a ɗan sarara a shakata tare, to amma a nan akwai babban hadarin yin sassauci da matakan da aka dauka.

Musamman ma idan an hada da shan giya, kamar yadda ƙwararru suka yi gargadi.

Dokata Estevão Urbano ya ce sassauci wajen daukar matakai za su iya haifar da "yawan mace-mace" bayan kirsimeti.

"Hakan zai zama tamkar ka yi rashin nasara a wasa ne a lokacin karshe".

"Mun kusa samun riga-kafi" a cewarsa, "Muna bukatar yin aiki tukuru mu kuma lura sosai lokacin Kirsimeti."