Coronavirus: Sabbin dokokin da wasu jihohin Najeriya suka saka

Asalin hoton, @GOVKADUNA
A yayin da wasu sassan Najeriya da dama suka fara shirya wa abin da hasashensu ya gano na sake samun hauhawar annobar cutar korona a karo na biyu, BBC ta yi duba kan sabbin matakan da jihohi daban-daban ke dauka da kuma yadda hakan zai shafi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
A ƙalla hukumomin manyan jihohi biyar ne suka sanar da sabbin matakan yaƙi da cutar korona.
Tun da fari, ministan lafiya na kasar Dakta Osagie Ehanire, ya ce ya bayar da umarnin a sake buɗe cibiyoyin killace mutane da na kula da masu cutar waɗanda aka rufe su a baya saboda rashin masu kamuwa da cutar sosai.
Ya yi hakan ne saboda amannar da gwamnatin ƙasar ta yi na samun kanta a yanayin da cutar ke hauhawa duba da yadda ake samun masu kamuwa da ita sosai da kuma waɗanda suke rasa ransu.
Kamar yadda yake faruwa a wasu ƙasashen, hauhawar cutar ta sa ana sake daukar matakan kulle - haka ma Najeriyar ke shirin komawa kan wancan tsari.
A ranar 21 ga watan Disamba, hukumar da ke daƙile cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta ce mutum 78,434 ne jumullar waɗanda suka kamu da cutar idan aka kwatanta da 66,228 wata guda daidai da ya wuce, wato ranar 21 ga Nuwamba.
Dr Ehanire ya gargaɗi 'yan Najeriya da cewa tun da riga-kafi bai kai ga zowa ba to ya kamata mutane su yi taka tsantsan wajen ganin cewa ba su yaɗa cutar ba kuma ba su kwasa ba a yayin bukukuwan Kirsimeti.
Tuni dai wasu jihohin suKa fitar da matakai a daidai lokacin da ake shirin bukukuwan Kirsimeti domin hana yaɗuwar cutar korona a yayin da take sake hauhuwa.
Bari mu ga yadda hakan zai shafi 'yan kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Legas (18 ga Disamba)
Daga ranar 21 ga Disamba, ma'aikatan gwamnati daga mataki na 13 zuwa kasa za su fara aiki daga gida har tsawon mako biyu (ban da ma'aikatan gaggawa da masu agaji)
Wuraren ibada ba za su wuce sa'a biyu suna bauta ba sannan masu ibadar ba za su wuce mutum 50 ba.
An haramta tarukan kalankuwa da liyafa har sai Baba ta gani.
Dukkan makarantu za su kasance a kulle har sai yadda hali ya yi.
Abuja - Birnin Tarayya (21 ga Disamba)
Dole dukkan wuraren shaƙatawa su bi dokokin da gwamnati ta sanya musu
Dole a dinga duba yanayin zafin jikin dukkan ma'aikata da abokan hulɗa a wuraren aiki da wuraren kasuwanci
Dukkan wuraren aiki da na kasuwanci dole su tanadi wurin wanke hannu da ruwa da sabulu da man sanitaiza
Dukkan dokokin da aka sanya wa wuraren ibadah a ranar 4 ga watan Yunin 2020 za su ci gaba da aiki kuma dole mutane su kiyaye su.
Anambra (16 ga Disamba)
An hana taruwar mutane da yawa a waje guda kamar biki ko jana'iza ko taron kungiyoyin al'umma
Za a horas da kananan hukumomin jihar 21 da shugabanninsu kan barazanar yaɗuwar cutar
Imo (21 Disamba)
Dole a rufe sakatariyar jiha daga ranar 21 ga watan Disamban 2020
Dukkan ma'aikatan gwamnati za su dakatar da aiki sai manyan sakatarori da masu muƙaman siyasa kawai.
Babu wani taro kowane iri ne idan har mahalartan suka wuce 100 kuma dole a bi dokar nesa-nesa da juna.
Kaduna (20 ga Disamba)
Saka takunkumi ya zama wajibi ga duk mai son fita daga gida
An haramta taron jama'a da yawa
Daga 21 na watan Disamba dukkan ma'aikatan gwamnati daga mataki na 14 zuwa ƙasa za su fara aiki daga gida
Wuraren ibada ba za su dinga wuce sa'a ɗaya ba, kuma kar mutanen su yi yawa
Motocin haya za su dinga daukar mutum biyu ne kwai a kowane layin kujeru sannan ba za dinga cika motar ba
Za a bar shagunan sayayya da na aski da na gyaran gashin mata a buɗe amma dole masu zuwa su dinga sanya takunkumi
Za a bar otel-otel a buɗe amma mashaya da wuraren cin abincinsu ba za su dinga aiki ba sai dai su dinga kai wa abokan hulɗa abin da suke so har daki
Gidajen abinci za su kasance a bude amma mutane ba za su dinga con abinci a ciki ba sai dai su dinga saya su tafi da shi gida
Wuraren yin bukukuwa da taruka da mashayu da gidajen rawa da wuraren motsa jiki duk za a rufe su sai yadda hali ya yi.
Makarantu za su kasance a rufe sai yadda hali ya yi.











