Covid: Fasahar mutum-mutumin da ke hana ma'aikatan lafiya kamuwa da cutar korona a Abuja

Bayanan bidiyo, Daliban da suka kirkiri fasahar kange ma'aikatan lafiya daga kamuwa da korona.

Ku latsa wannan hoto na sama domin kallo:

Daliban makarantar Glisten International School da ke Abuja sun kirkiro wannan fasaha mai suna Mairobot bisa la'akari da yadda jami'an lafiya a Najeriya suka rinka kamuwa da cutar korona har ta kai su ga mutuwa, a zagayen annobar na farko.

A yanzu kuma da duniya ke shaida komen annobar a karo na biyu, daliban sun ce kirkira wannan fasaha ka iya takaita kamuwar jami'an na lafiya daga cutar mai kisa.

Wannan fasaha ta mutum-mutumi an yi ta ne da siffar wani akwakwu mai taya ta yadda zai yi zarya tsakanin marasa lafiya.

Mairobot na da kafa hudu sannan na amfani da na'urar daukar hoto a matsayin idanu da kuma na'urar aike sako ta Infrared wajen gwada zafin jikin marasa lafiya.

Ita wannan fasaha ta Mairobot na da matuki wanda shi ne idanunta.

Mai rahoto: Usman Minjibir

Mai daukar hoto: Abdul salam Usman Abdulkadir

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla