Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boko Haram: Tambayoyin da ƴan Najeriya ke son ƴan majalisa su yi wa Buhari kan tsaro
Ƴan Najeriya sun bayyana irin tambayoyin da ya kamata ƴan majalisa su yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari idan ya bayyana a gaban majalisar.
A makon da ya gabata ne majalisar wakilai ta gayyaci Buhari domin ya yi bayani kan ƙalubalen taɓarɓarewar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Sannan kuma shugaban ya yi mata bayani kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar.
Wannan na zuwa ne bayan mummunan harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai a ƙauyen Zabarmari, inda aka yi wa manoma yankan rago. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutum 110 aka kashe a harin, Boko Haram na cewa 78 ta kashe.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicinsa da kuma yin Allah-wadai da mummunan harin, yana cewa akwai rashin tunani a ciki.
Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa shugaba Buhari ya amince ya bayyana a gaban majasalisar domin amsa tambayoyi kan matsalolin tsaron Najeriya.
Wannan ya sa muka jefa tambaya ga masu bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta cewa: Wace tambaya ya kamata 'yan majalisa su yi wa Buhari idan ya bayyana a gabansu?
A shafin Twiitter kusan mutum 2,000 ne suka so saƙon yayin da kusan 300 suka yi tsokaci tare da bayyana tambayoyinsu.
Mafi yawan tambayoyin sun fi mayar da hankali kan dalilin shugaban na rashin sauke manyan hafsoshin sojin Najeriya.
Ga wasu daga cikin tambayoyin da ƴan Najeriya ke son majalisa ta yi wa Buhari daga Twitter.
@nafiu_barau ya yi tambayoyi guda uku kamar haka: 1. Me ya sa matsalar tsaro ke ta'azzara? 2. Me ya sa shugaban ya gaza sauke manyan hafsoshin sojoji? 3. Me aka amfana da shi da aka rufe iyakar kasar nan?
Tambayoyin @SirajoM54041952 su ne: Mi ya sa ka ƙi karbar shawarwarin Jama'a, akan sallamar manyan hafsoshin sojan Nigeria? Mi ya sa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara akan tsaro ba ya da tasiri a Gwamnatinka? Waɗanne matakai ka ke ɗauka don cika alƙawullan da ka dauka lokacin yekuwar neman zabe?
Shi ma @Ibrahim_salisuM ya yi tambayoyinsa kamar haka: Su tambaye shi me ya sa ake ta kashe mutane haka, amma gwamnatinsa ta gagara daukar mataki. Ko abun ya fi ƙarfinsa ne?
A facebook ma kusan mutum 500 sun yi tsokaci kan irin tambayoyin da suke son majalisa ta yi wa shugaban.
Babawo Mato Mai'adua ya yi tambayoyinsa kamar haka: Su tambaye shi akan halin da tabarbarewar tsaro ke ciki, wane mataki ya ɗauka akan kisan gillar da ake yima al-umma a arewacin kasar, Kuma wani mataki ya ɗauka akan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki, kuma ina batun bude kan iyakoki na kan tudu na kasar.
Gaddafee AL-hassan Umar ya ce: maganar da ya kamata su yi masa tawuce ta tsaro ne... muna mai rokonku da ku tsaya ku fahimtar da shi akan matsalar tsaro da muke fama da shi duk da mun san cewa ya san komai a wannan ta'addancin da ke faruwa a wagga kasa musamman arewacin NIGERIA.
Bayanan da majalisa ke son samu daga Shugaba Buhari
Honourable Satomi Ahmed, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin buƙatar gayyatar Buhari a majalisa, ya shaida wa BBC cewa an ɗauki wannan mataki ne ganin cewa an sha kiraye-kiraye ga shugaban kan neman sake fasalin harkokin tsaro amma shiru ake ji.
Satomi ya ce yanayin da ake ciki ya tabbatar da cewa dole ana neman gyara, amma majalisa ta rasa dalilan shugaban ƙasa don haka ta buƙaci ya bayyana a gabanta.
Majalisar ta ce dole shugaban ya fito ya yi bayani mai gamsarwa kan irin matakan da yake ɗauka da kuma dalilan gamsuwa da ayyukan hafsoshin tsaron ƙasar da ake gani ya kamata a sake zubinsu.
Sannan akwai kuma buƙatar sanin ina shugaban ya dosa, domin kashe-kashe da sace-sacen da ake gani sun wuce tunani.
"Majalisar ta ce talakawa sun bai wa Shugaba Buhari amana don haka ba za su amince su ci gaba da zaman ƴan amshin shata ba," in ji Satomi.
"Akwai gazawa a salon yaƙin da jami'an tsaron ke yi da matsalolin tsaro don haka za su so ji daga baƙin shugaban don sanin halin da ake ciki."
Yaushe Buhari zai bayyana gaban majalisa?
Duk da cewa majalisar ba ta bayyana ranar da take son Shugaba Buhari ya bayyana a gabanta ba, amma wasu rahotanni sun ce a makon da za a shiga ake sa ran shugaban zai je majalisar.
Rahotanni sun ambato shugaban masu rinjaye a majalisar Alhassan Ado Doguwa na cewa shugaban zai bayyana gaban majalisar wakilan a ranar Alhamis mai zuwa.
Tun da farko Hon Satomi, ya shaida wa BBC cewa ba da daɗewa ba ne za su karɓi baƙuncin shugaban saboda a cewarsa "dole mu tashi tsaye lura da cewa tura ta kai bango."