Abin da ya sa wasu a Najeriya ke kulle ƴan uwansu masu taɓin hankali tsawon shekaru

- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo da Salihu Adamu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Batun samun mutane da ake ɗaure su tsawon shekaru da aka yi ta samu a baya-bayan nan a Najeriya ya sa ƴan ƙasar sun kaɗu matuƙa, sannan ya bayyana halin ko in kula da wasu iyayen ke nuna wa ƴaƴansu da kuma rashin tanadi mai kyau kan sha'anin lafiyar ƙwaƙwalwa.
An gano wasu mutane da ake zaton suna da taɓin hankali da aka ɗaure su cikin mari, sannan aka bar su a waje ɗaya tsawon shekaru inda a nan suke ci da sha da yin najasarsu.
A wani lamarin da aka gani, akwai wani mutum mai shekara 32 da iyayensa suka ɗaure shi a ƙalla tsawon shekara bakwai a garejin motoci a jihar kano da ke arewa maso gabshin Najeriya.
Sannan an samu rahotannin yadda ake azabtar da yaran da ke ƙarƙashin kulawar matan uba ko dangi.
A wani lamari na baya-baya da ya faru a watan Satumba, an kama matar mahaifin wani yaro ɗan shekara bakwai bayan da ta kusan kashe shi a Kano, birnin da ya fi kowanne girma a arewacin Najeriya.
Har yanzu ba a gurfanar da matar uban ba kuma ba ta ce komai kan zargin ba.
Yaron da aka ɗaure a turken awaki
Duk da cewa ana samun al'amura na cin zarafi a ko ina faɗin Najeriya, a baya-bayan nan an fi samun matsalolin a arewacin Najeriya, tun bayan samun labarin wani yaro ɗan shekara 11 wanda aka ɗaure a turken dabbobi a jihar Kebbi, yayin da ubansa da matan uban da a yanzu aka gurfanar da su a kotu suke zaune a cikin gida suna jin daɗi abinsu.
Mutane sun harzuƙa kan hoton da ke nuna yaron zaune tsulum cikin kaji da dabbobi da talo-talo ba daɗin gani.

"Bayan shari'ar a Kebbi, mun fara samun bayanan sirri," in ji Haruna Ayagi, shugaban ƙungiyar kare hakkin dan adam ta HRN, ƙungiya mai zaman kanta da ta shiga cikin ceton mutum 12, bakwai daga cikinsu yara ƙanana, a watan Agusta kaɗai, a jihar Kano.
Mista Ayagi ya ƙara da cewa "Abin da muka lura shi ne, yaran da aka ci zarafinsu, ba su zauna tare da iyayensu mata bane."
A babban birnin tarayya Abuja, an samu nasarar ceto wasu yara biyu daga bayan gida, inda ake zargin matar mahaifinsu tana kulle su a kullum har sai ta dawo daga aiki.
'Ana dukan su, an ƙona su kuma an bar su da yunwa'
Wasu hotunan yaran da aka yi wa mummunan rauni sun yi kama da hotuna daga fim ɗin Nollywood, inda ake nuna yadda halayen muguwar matar uba suka zama gama gari a tsakanin mafi yawan 'yan Najeriya, ko da yake tabbas akwai iyaye mata da yawa masu halin kirki da ke kula da ƴaƴan da ba nasu ba.

A wani lamari da ya faru a Kano, ana zargin wata matar uba ta lakaɗa wa wata 'yar mijinta mai shekara bakwai duka da ƙonata, sannan ta hana ta abinci, a cewar hukumomi.
Yarinyar da wasu sauran yaran da aka ceto a Kano, yanzu haka suna gidajen kula na gwamnati, suna karɓar magani da shawarwari, yayin da aka kama wasu daga cikin iyayen da masu riƙon, amma har yanzu ba a gurfanar da su a gaban kotu ba.
Wata dokar tarayya ta 2003 wacce ke kare 'yancin yara ta bai wa jihar ƴancin ƙwace duk wani yaro da ake zargin cewa an yi watsi ko kuma ana musguna musu.
Amma har yanzu jihohin arewa 11 ciki har da Kano ba su zartar da wannan doka ba, musamman saboda adawa da ayyana yaro a matsayin duk wanda bai kai shekara 18 ba, wanda hakan ke nufin haramta auren wuri ga yara da ake yi a yankin.
Wasu Musulmai sun yi imani da cewa da zarar yarinya ko yaro sun balaga, to sun manyanta kuma suna iya yin aure.
Wannan taƙaddama ta hana zartar da dokar a jihohi 11, hakan ya sa ya zama da wahala ga jihar ta sa baki a cikin wani lamari da ake zargi na rashin adalci ko rashin kulawa.

Asalin hoton, Getty Images
Bugu da ƙari, auren mace fiye da ɗaya a arewa da kuma sauƙin mutuwar aure - inda kawai namiji cewa zai yi yi "Na sake ki" - ya sa yara da yawa ba sa rayuwa tare da iyayensu na asali wanda hakan ke sa su faɗa mugun hannu.
Imaobong Ladipo Sanusi, shugabar kungiyar Wotclef, wata ƙungiya da ke fafutukar kare hakkin mata da yara ta ce: "An samu daidaituwar rikici a kan waɗannan yara, galibi a matsayin aikata mugunta da rashin sanin hakkin dan adam."
Tana son a gudanar da gangamin fadakarwa game da abin da ya shafi "cin zarafin mutane da kuma fahimtar taswirar rahoto mai kyau".
Ƙyamar masu taɓin hankali
A kwanakin baya ne aka ceto wani matashi mai shekara 30 daga garejin mota na iyayensa a Kano, inda maƙwabta suka ce an kulle shi tsawon shekara bakwai bisa zarginsa da taɓin hankali, da ƙyar ya iya yin tafiya lokacin da aka same shi.

Asalin hoton, HRN
Kafafunsa sun karkace, sannan gwiwoyinsa ma sun yi sanyi sun kasance marasa ƙarfin da za su tallafa wa jikinsa mai tsananin rauni.
A wani lamarin da ya faru kuma a Kano, an ga wani mutum mai shekara 55 aka gano a kulle cikin ɗaki ba tare da kofa ko taga ba. Ɗaya daga cikin ƙafafunsa an haɗe ta da babban katako tare da sandar ƙarfe an ɗaure.
Danginsa sun kulle shi tsawon shekara 30 saboda yana da taɓin hankali, kuma an ɗauke shi zuwa babban asibitin Rogo. Wani likita a asibitin, Luis Nweke, ya ce ya sha wahala daga "halayyar rashin hankali da taɓin hankali".
Shekaru da yawa, Najeriya na gwagwarmaya don kula da masu taɓin hankali, saboda ƙyamar da ke tattare da da larurar.
A wasu al'ummomin, ana ɗaukar larurar taɓin hankali a matsayin abin kunya kuma ana kiran masu taɓin hankali da "mahaukata", waɗanda danginsu ke yanke alaƙa da su, ana tilasta musu yin yawo a kan tituna cikin yagaggun tufafi kuma suna cin abinci daga shara.

Asalin hoton, Getty Images
"Matsalar da ke faruwa a arewacin kasar na nuna abin da ke faruwa a Najeriya. Wannan batun na kulle mutane masu taɓin hankali wani lamari ne da ya yaɗu a duk faɗin kasar," kamar yadda shugaban kungiyar likitocin masu taɓin hankali, Dakta Taiwo Lateef ya shaida wa BBC.
Ba a samun cikakkun bayanai na yau da kullum kan yawan mutanen da ke buƙatar magani, amma a yayin da ake da likitocin kula da masu taɓin hankali 300 a ƙasar da ke da yawan mutum kusan miliyan 200, iyalai daga ɓangaren Musulmai da Kirista kan koma cibiyoyin warkarwa na gargajiya, da wuraren malamai.
"Saboda yawancin mutane suna ganin rashin taɓin hankali a matsayin matsala ta ruhaniya, suna neman taimako daga shugabannin ruhaniya da masu maganin gargajiya da fatan kawar da muguwar ruhun da ke da alhakin," in ji Dr Oluseun Ogunnubi, wani mai ba da shawara game da taɓin hankali.


Wani rahoto na 2013 da ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta fitar ya ce a kalla kashi 10 cikin 100 na al'ummar kasar sun samu matsalar tabin hankali. Kasa da kashi 10 cikin 100 na wannan adadin sun samu damar samun kulawar da suke bukata, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Kodayake rashin cibiyoyin kula da lafiyar kwakwalwa wani bangare ne na babbar matsala a tsakanin bangaren kiwon lafiya. Ganin cewa jihohi 15 cikin 36 na ƙasar ne kaɗai ke da cibiyoyin duba lafiyar kwakwalwa ya sa mutane ke da wahalar samun kulawa a karkara.
Amma ko a wuraren da ake da cibiyoyi ko kuma asibitoci na kula da masu taɓin hankali, kyamar da ke tattare da daukar masoya don kai su wuraren domin nema musu magani na hana iyalai da yawa yin hakan.
"Akasarin mutane ma ba sa son ana ganinsu suna shiga cibiyoyin da ake kula da masu taɓin hankali sakamakon tsangwama da ake yi wa masu larurar," in ji Dakta Lateef.
"Mutane na rayuwa cikin karyatawa saboda nuna kyama, ta yaya za a ce ina da tabin hankali, saboda ba su taba yarda da shi a matsayin wani nau'i na rashin lafiya ba?" Ya tambaya.
"Mutane da dama ba su so su yarda cewa suna da taɓin hankali, ta ya za a ce ina da taɓin hankali, saboda ba su taɓa yarda cewa taɓin hankalin wata larura bace".
Manuella Bonomi ce ta yi zane-zanen cikin wannan labarin











