DR Congo: Yadda ake rarraba kayan allurar riga-kafin cutar ƙyanda

Mulalu Lwesso walks down a country road

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

Cikin shekaru biyu da suka gabata, Jamhuriyyar Dimkoraɗiyyar Congo ta yi fama da annobar cutar ƙyanda mafi muni a duniya, wacce ta kashe fiye da yara 7,000.

Ministan lafiya ya ce annobar ta wuce, amma ƙwararru sun ce ganin yadda ba a samun riga-kafi sosai da bai haura kashi 60 cikin 100 ba, to nan kusa za a iya samun ɓarkewar wata annobar.

Ƴar jarida Sara Assarssonda da mai ɗaukar hoto Johannes Tegner sun gana da ma'aikatan lafiyar da ke yin doguwar tafiya don rarraba muhimman kayayyakin riga-kafin:

Mulalu Lwesso sits on a wooden bench with his coolbox next to him

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

Duk da cewa ba za ka ga alamar datti a jikin takalmansa ba, Mulalu Lwesso kan yi tafiyar sa'a shida akai-akai don rarraba magungunan alluran riga-kafi a yankunan karkara.

''Na fara karatun aikin jinya amma rashin kuɗi ya hana ni kammala karatuna - a yanzu na kan taimaka ne a duk lokacin da ake buƙatar hakan.

''Tafiya ce mai nisa ga shi na fara tsufa. Duk wata sai na bi hanyar nan tun shekarar 1987,'' a cewarsa.

Mutumin mai shekara 62 ya kan yi irin wannan tafiyar daga wani asibiti a garin Mwenga - yana share zufa, ɗauke da jakar kular magungunan rataye a kan kafaɗarsa, ya ɗauki hanyar koma wa ƙauyensa da allurai da magungunan riga-kafin.

Lorries try to negotiate a muddy country road

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

Sauran hanyoyin kai kayayyakin na iya jawo tarnaƙi. Manyan motoci kan maƙale tsawon kwanaki, ko ma makwanni, idan aka yi ruwan sama mai ƙarfi da ya sa hanyoyin suka cika da taɓo.

Jamhuriyyar Dimkoraɗiyyar Congo, ƙasar da girmanta ya kai kashi biyu bisa ukun Yammacin Turai, na da hanyoyi masu kyau ne kawai na tsawon kilomita 2,000.

Magungunan riga-kafi kuwa zafi kan yi musu illa har ƙarfinsu ya ragu.

A carton containing a measles vaccine imported from India

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

A Indiya ake yin waɗannan magunguna sannan akai su babban birnin kasuwanci na DRC wato Goma, a kwale-kwale ta hanyar sanya su a wata ma'ajiyar sanyaya abubuwa a babban asibiti na Bukavu.

Mutumin da ke kula da rarraba allurar a yankin Kudancin Kivu Oscar Mutama ya ce, ''Yanayin sanyi a nan ya kai tsakanin 6 zuwa 7 ma'aunin salshiyas, amma mukan samu wutar lantarki ne kawai na ƴan wasu sa'o'i a rana.

''Idan kuwa aka ɗauke wuta na tsawon lokaci, to ba za mu iya ba da tabbacin cewa alluran za su kasance da ingancinsu ba.

''Kwanan nan muka samar da sabbin hanyoyin yin rijistar magungunan da suka lalace, amma ba mu da hanyoyin da za mu bi don tabbatar da binciken ingancinsu sosai.''

Mr Lwesso and his colleagues push a vehicle to get it started

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

A zangon gaba na bulaguron kuɗin man motar ya ƙare, inda ala tilas Mista Lwesso ya saɓa jakar kular magungunan ya kama hanyar kai su inda za a je da ƙafa a tafiyar kilomita 30 - bayan da tawagar suka ƙiyasta cewa ɗaukar babur ko tasi zai yi tsada sosai.

Tsarin lafiya a DRC ya taɓarɓare saboda rashin kayayyaki, sannan kuma yankin gabashin ƙasar na fama da rikice-rikicen masu tayar da ƙayar baya da halin ni ƴasu da mutane ke ciki, sannan talauci ya yi wa mutane dabaibayi.

Nine-month-old Zawidi with her mother Tantine Katangalo

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

Zaiwidi ƴar wata tara ta yi sa'a za a yi mata tata allurar riga-kafin ta farko a wannan karon.

An yi wa dukkan yayyenta alluran riga-kafin kamuwa da cututtuka irin su shan inna da ƙyanda da sarƙe haƙora da kuma hangun.

Sai dai duk da haka ɗaya daga cikinsu ya kamu da cutar ƙyanda a lokacin da annobarta ta ɓarke a baya-bayan nan.

''Bai yi ciwo sosai ba, amma na damu ƙwarai da rashin lafiyar tasa,'' a cewar mahaifiyarsa Tantine Katangalo.

Ta ɗauki Zaiwidi ta yi tafiyar kusan sa'a biyu don zuwa cibiyar lafiya. Da yake mutane suna zaune ne a wurare daban-daban a tsaunuka, sannan kuma ba su da zaɓin abin hawa, nisan tafiyar da iyaye kan yi ya zama wata babbar hoɓɓasa, a cewar shugaban kula da magunguna Arsène Mubuto.

Tantine Katangalo carries her daughter down a country road

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

Mayaƙan sa kai sun tursasa wa dubun-dubatar mutane barin gidajensu a cikin shekarun da suka gabata.

''Muna kiransu da mayaƙan da ke kai kawo,'' a cewar Dr Mubuto. ''Idan akwai tashin hankali a wani yanki, dole mutane su koma wani ƙauyen mai maƙwabtaka kafin daga bisani su koma nasu.''

Duk da wannan yanayi da ake ciki, ya ce an cimma abubuwa da yawa a ƙasar: ''A lokacin da muka fara gano cutar ƙyanda a 2019, mun yi saurin ɗaukar mataki na yi wa kowa riga-kafi. Kuma kamar an yi nasara.''

Presentational grey line

Mece ce ƙyanda?

Ƙyanda ƙwayar cuta ce da da farko take jawo mura da yoyon hanci da atishawa da zazzaɓi.

Daga bisani sai ƙuraje su feso a fuska da illahirin jikin mutum.

Mafi yawan mutane kan warke, amma ƙyanda na iya jawo naƙasa ta dindindin ga mutum. Ta kan iya kisa musamman idan ta jawo cutar numoniya a huhu ko idan ta kumbura ƙwaƙwalwa.

An yi ƙiyasin cewa mutum 110,000 na mutuwa sakamakon ƙyanda a faɗin duniya duk shekara.

Presentational grey line
Parents queues with their children outside Iganda health centre

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

"Yawancin iyaye kan zaɓi zuwa nan da ƴaƴansu duk da cewa suna da nisa,'' a cewar malamin aikin jinya Doms Mushimgwa a cibiyar lafiya ta Iganda da ke wajen garin Mwenga.

''Babu batun bujirewa riga-kafi.''

A woman looks a syringe containing a vaccine

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

''A wasu yankunan, kusan rabin yara ba sa samu a yi musu riga-kafi kwata-kwata,'' a cewar Jorge Caravotta, wani ƙwararre kan lafiya a Asusun Kula da Yara Na Majalisar Ɗinkin Duniya, Unicef.

''A lokacin ɓarkewar annobar cutar Ebola, mun ga raguwar bayar da riga-kafi da kashi 25 cikin 100, abin da ya jawo ɓarkewar annobar cutar ƙyanda a baki ɗayan ƙasar.''

Kuma kamar yadda shugaban likitan asibitin yankin Dr Mubuto ya faɗa: ''Ko da wata rana za mu cimma hakan 100 bisa 100, wasu alluran riga-kafin tuni sun lalace a yayin da suka isa asibitin.''

A patient is weighed

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

Fiye da yara 7,000 ƴan ƙasa da shekara biyar ne suka mutu tun bayan ɓarkewa annobar cutar ƙyanda ta baya-bayan nan a shekarar 2018, a cewar ma'aikatar lafiya ta DRC.

Tamowa na sanya yara cikin babban haɗari, ta kuma sa ya zama wahala ga riga-kafin wajen yin aiki a jikinsu, in ji Jorge Caravotta na Unicef.

''Wata matsalar kuma ita ce wasu alluran riga-kafin ba sa daɗewa sai su lalace kuma ana buƙatar su da yawa.

''Babban ƙalubale ne a gamsar da iyaye cewa riga-kafiin sun ne hanyoyi mafi kyau na kare kamuwa daga cututtuka, a yayin da a lokaci guda kuma su kan ga yara sun kamu da cutar duk da cewa an yi musu riga-kafin.

A infant sits in a hospital ward with her mother.

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

''Mafi yawan yaran da muke bai wa magani za ka ga suna fama da tamowa mai tsanani,'' a cewar Aline Nabintu, wata likita a Babban Asibitin Mwenga.

''Mu kan ba su kunun gyaɗa wanda ke taimaka musu sosai. Sai kuma mu ɗan taimaka musu kaɗan mu tura su gida.

''Sai kuma ka ga yaran dai da muka duba sun sake dawowa don a sake duba su. Gaskiya abin da matuƙar wahala da ɗaga hankali.''

Nurse Doms Mushimgwa at the clinic

Asalin hoton, Johannes Tegner/BBC

A yayin da ya kammala ba da jerin alluran, malamin aikin jinya Mushimgwa ya kulle ɓangaren haihuwa na abibitin da yake aiki. Ya nuna ƴan kayan aiki kaɗan din da suke wajen kamar su zare da abin auna bugun ƙirji. An aika masu haihuwa da ke da matsala zuwa asibitin Mwenga.

Amma ba kowace mace ce take tsira ba don ana yawan samun mace-macen mata masu haihuwa.

Duk da cewa mutuwar ƙananan yara ta ragu sosai da rabi a a DRC sun farkon shekarun 1990, kashi 8.5 cikin 100 na yaran har yanzu ba sa kai wa shekaru biyar da haihuwa.

''Riga-kafi ita ce babbar inshorar rai. Idan yara suka kamu da cuta, iyaye da dama ba sa iya biyan kuɗin asibiti,'' a cewar Mr Mushimgwa.

"Amma yana da muhimmanci a kawo riga-kafin nan da wuri don su yi aiki yadda ya kamata. Idan ba haka ba za a samu matsala.''

Dukkan hotuna suna da haƙƙin mallaka.