Yadda juyin mulkin Mali ya shafi yaƙi da ta'addanci

Islamist fighters in Gao, Mali - 2012

Asalin hoton, AFP

Wata guda bayan da aka yi juyin mulki a Mali, shugabannin soji sun tsaya kai da fata don ci gaba da yaƙar 'yan ta'adda amma hakan ba zai faru ba har sai an cimma yarjejeniyar maido da martabar dimokraɗiyya kamar yadda wani mai sharhi a yankin Afrika ta Yamma Paul Melly ya rubuta.

Har yanzu ba a kai ga batun yin zaɓe ba makwanni bayan da sojoji suka ƙwace mulki a Bamako lamarin da ya tilasta wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita yin murabus, duk da cewa an ayyana tsohon ministan tsaro Ban Ndaw a matsayin shugaban riƙo.

Sojojin na fatan gamsar da mambobin ƙungiyar Ecowas su amince da ƙudirinsu bayan tattaunawar da aka yi a ƙarshen mako domin sake ba wa 'yan hamayya masu shakku tabbaci.

Amma sojojin da suka hamɓarar da mulkin a Mali sun aike wani saƙo ga ƙasashen duniya da suka jibge dubban sojojinsu domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tsawon shekaru abin da ya sa Arewacin Mali ke ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'adda yayin da yankunan tsakiya ke fama da rikicin ƙabilanci.

Kanar Manjo Ismael Wagué, mai magana da yawun sojojin da suka yi juyin mulki ya dage cewa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Mali da sojojin yaƙi da ta'addanci na Faransa da kuma sojojin ƙasashen yankin Sahel da kuma dakaru na musamman daga Turai dukkansu na "ƙawance ne don maido da zaman lafiya".

A man in a crowd shouts as he holds a sign that reads, "France get out" during a protest against French and UN forces based in Mali - Bamako, 10 January 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a farkon shekarar nan sun nemi sojojin Faransa su yi ƙaura daga Mali

Cikin shekara guda da ta gabata akwai alamomi da ke nuna cewa wasu 'yan Mali na nuna rashin jin daɗinsu kan kasancewar sojojin Faransa a ƙasar duk kuwa da rawar da suke takawa a matsayin muhimman ƙawaye ga sojojin ƙasar.

Amma Kanar Manjo Wagué ya yi baya-baya ga batun nuna son rai.

Ya fayyace cewa sabbin shugabbanin sojojin Mali sun mai da hankali wajen yin aiki da sojojin ƙasashen waje - kamar yadda suke fatan tabbatar da yarjejeniyar Ecowas ga ƙudirinsu na siyasa.

2px presentational grey line

Duk da cewa wata yarjejeniyar ƙarshe da aka cimma da Ecowas kan batun miƙa mulki na neman gagara, har yanzu akwai barazana daga 'yan ta'adda.

Sojoji za su ci gaba da yaƙi da ta'addanci a Arewacin ƙasar - sannan ya kasance atisaye mai haɗarin gaske; an kashe ƙarin sojojin Faransa biyu a wani harin bam kusa da yankin Taoudenni ranar 5 ga watan Satumba, kuma wannan shi ne hari na baya-bayan nan da ya yi sanadin mutuwar Faransawa 45 sannan lamarin ya shafi da yawa daga sojin 'yan Mali da na Majalisar Ɗinkin Duniya tun 2011.

Sojojin Mali za su fuskanci koma-baya

Yayin da ake kashe dakaru da dama, akwai manyan hare-hare da aka kai inda dubban mutane suka mutu a kwanton-ɓaunar da aka yi musu.

Hari na farko - Kisan gillar da aka yi a Aguelhok cikin watan Janairun 2012, lokacin da 'yan ta'adda da mayaƙan Tuareg suka kashe kusan mutum 100 bayan sun ƙwace iko da wani sansani - ya taimaka wajen rura wutar rashin jituwa a tsakanin masu mukami da kuma sojojin da suka yi juyin mulki a Maris ɗin shekarar.

Sama da shekara bakwai da suka wuce kuma duk da shirin Tarayyar Turai na ci gaba da aike sojoji tare da sake ƙarfafa musu gwiwa da ba su horo, har yanzu sojojin na fuskantar rashin nasara.

2px presentational grey line

Wannan lokacin musamman a hannun ƙungiyar IS reshen Greater Sahara da ake kira (ISGS), wadda ke iƙirarin mubaya'a ga ƙungiyar Gabas ta Tsakiya.

A shekarar da ta gabata, a ranar 30 ga Satumba da 1 ga Oktoba, kusan sojoji 85 ne suka mutu lokacin da ISGS ta mamaye sansaninsu da ke Boulikessi a kan iyakar Burkina Faso.

Sannan a ranar 1 ga watan Nuwambar 2019, ƙarin mutum 49 aka kashe a wani hari da ISGS ta kai kan wani sansani a Indélimane da ke kusa da iyaka da Nijar a gabashin ƙasar mai nisa.

Map of the Sahel countries: Mauritania, Mali, Niger, Burkina Faso and Chad

Rashin horo da ƙarancin makamai na daga cikin abubuwan da suka janyo koma-bayan.

Amma akwai ƙarin fargaba kan rashin jagoranci na gari ta fuskar siyasa daga tsohon Shugaba Keita a Bamako da kuma batun cewa gwamnati ta yi sake wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015 da 'yan a-waren Tuareg da ke arewacin ƙasar.

Jinkirin da aka yi wajen murƙushe mayaƙan da kuma raba iko da kuɗi zuwa ga matakin yanki ya haifar da yanayin takaici da ta'addanci zai ci gaba.

Wannan lamarin na iya zama wani babban abin da ya janyo juyin mulki na ranar 18 ga watan Agusta - waɗanda shugabanni ciki har da jami'ai da suka san irin mawuyacin da sojoji ke fuskanta a yankin arewacin ƙasar.

Sojojin Mali za su ci gaba da yaƙi da ta'addanci tare da sojojin ƙasashen waje - Sojin Faransa da sojin ƙasashen yankin Sahel da ake kira G5 (Mali da Mauritania da Burkina Faso da Nijar da Chadi), sojojin Tarayyar Turai na musamman da na Majalisar Ɗinkin Duniya Minusma.

Aikin dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya shi ne tabbatar da zaman lafiya a maimakon yaƙi da 'yan ta'adda - ganin yadda aka yi asarar soji 220 tun bayan da aka kaddamar da sojojin a 2013.

Ƙalubalen sojojin

Amma ƙalubalen da ke fuskantar sojojin na cikin ƙasar da na waje shi ne ƙoƙarin mai do da kwanciyar hankali a yankin Arewa da kuma tsakiyar Mali ba wai ya ta'allaƙa ne kan yaƙar ƙungiyoyin 'yan ta'adda ba ne kaɗai.

A soldier of the Malian army patrols the archaeological site of the Tomb of Askia in Gao - 10 March 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwanciyar hankali abu ne mai mahimmanci ga ci gaba a yankin arewa

Sojojin Faransa na Barkhane sun kai wasu jerin hare-hare kan 'yan ta'adda tare da kashe wasu fitattun kwamandoji irinsu Abdelmalek Droukdel, Jagoran Ƙungiyar al-Qaeda a yakin Sahara ranar 3 ga watan Yunin shekarar nan bayan da ya tsere zuwa Mali daga Arewacin Algeria.

Amma irin waɗannan hare-haren ba su hana rikicin 'yan ta'adda ba a yankin arewa daga kogin Neja kusa da Mauritania zuwa iyakar gabashin ƙasar da Nijar.

2px presentational grey line

Yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen Tuareg

  • Al'umomin Tuareg na yankin Arewa sun koka da yadda ake mayar da su saniyar-ware tun bayan samun 'yancin kai a 1960.
  • Mayaƙan IS sun ƙwace iko da 'yan awaren Tuareg a 2012 inda suka karɓe wasu birane.
  • An ƙwato yankin a 2013 tare da taimakon sojojin Faransa - sannan shekara biyu bayan nan, aka rattaba hannu kan wata yarjejeniya inda aka yi alƙawarin samar da ci gaba da rage ƙarfin ikon arewacin Mali.
  • Amma ba duka mayaƙan aka ci ƙarfinsu ba kamar yadda aka yi alƙawari sannan an samu jinkiri wajen miƙa mulki
  • Wannan ya janyo matsalar tsaro da ƙungiyoyin ta'addanci cin karensu ba babbaka.
2px presentational grey line

Sannan wasu daga cikin kwamandojin - kamar Abu Wali al-Sahrawi na Ƙungiyar ISGS - baƙi ne, da yawansu 'yan Mali ne.

Sun haɗa da Amadou Koufa, malamin da yake jagorantar Ƙungiyar Macina Liberation Front da ke ɗaukar manoma a matsayin ma'aikatanta ko kuma shugaban 'yan tawayen Tuareg a wani lokaci Ag Ghaly wanda ya jagoranci Ansar Dine da kuma gamayyar ƙungiyoyin sojoji da Jama'a Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin _JNIM).

Mayaƙan na ci gaba da yin ƙorafi kan al'umomin yankin kan samun damar yin kiwo ko tallafin gwamnati misali ko kuma cin zarafi daga sojoji.

Tallafin ƙasashen duniya

Dakaru kaɗai ba za su iya magance matsalar ba.

Samar da ci gaba da kuma inganta harkokin gwamnati na da matukar mahimmanci musamman a yankunan da gwamnati ta gaza sauke nauyin da yake kanta.

A French helicopter flying over Gao, Mali - 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojojin da suka yi juyin mulkin na son ci gaba da ƙawance da sojojin ƙasashen waje

Dole ne tsaro ya kasance yana ciki saboda idan ba tsaro, ba za a iya tabbatar da muhimman abubuwa kamar adalci da ilimi da kiwon lafiya ba.

Amma ci gaba yana buƙatar jagorancin siyasa da kuma tsarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Kuma shi ne yasa tattaunawar da ake a Bamako da kuma batun miƙa mulki da Ecowas za ta amince da shi - abin da zai 'yantar da Mali daga takunkumi da kuma buɗe ƙofar maido da tallafin ƙasashen waje - abu ne mai matuƙar muhimmanci.

Abin da sojojin CNSP ke so na tabbatar da haɗin kan sojoji da dakarun ƙasashen waje da tsaro ba tare da yarjejeniyar siyasa ba ba zai iya tabbatuwa ba.

Karin labarai da za ku so ku karanta: