Dabbobi na barazanar ƙarewa saboda muguntar ɗan adam

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Helen Briggs
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Environment correspondent
Wani rahoto da wata ƙungiyar tattalin namun daji ta WWF ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar namun daji da kusan kashi biyu bisa uku cikin shekara 50 da suka gabata.
Rahoton ya bayyana cewa yadda namun daji ke ci gaba da raguwa cikin sauri na ƙara ƙaruwa.
Kuma ya bayyana cewa ɗan adam na lalata abin da ubangiji ya ajiye tun fil azal.
Namun daji za su ci gaba da ƙarewa idan ana ƙona dazuka, da ci gaba da kama kifin da ke cikin teku, in ji Tanya Steele, Shugabar Ƙungiyar WWF.
"Muna lalata duniyarmu - wadda muke kira gidanmu - muna barazana ga rayuwarmu, da tsaronmu a nan duniya."
Me adadin yake nufi?
Rahoton ya dubi dubban dabbobin dawa daban-daban, waɗanda masu kula da dabbobi a faɗin duniya suka sa ido kan su.
Sun lissafa cewa an samu raguwar dabbobin da kusan kashi 68 cikin 100 a cikin dabbobi 20,000 da aka lissafa, da suka haɗa da tsuntsaye da da 'yan ƙwai da masu ja da ciki, da kifayen ruwa inda aka fara binciken tun a 1970.
Wannan raguwar da aka samu babbar hujja ce ta irin ɓarnar da bil adama ke yi wa duniya, in ji Dakta Andrewa Terry, daraktan wata ƙungiya ta kula da dabbobi da ke Landan, wanda shi ne ya bayar da ƙididdigar.
"Idan ba a kawo sauyi a wannan lamarin ba, adadin dabbobin ba makawa zai ci gaba da raguwa, wanda zai jawo ƙarewar namun daji da kuma barazana ga duniyar da muka dogara a kanta," a cewarsa.
Rahoton ya bayyana cewa annobar korona tamkar manuniya ce kan yadda ke da akwai dangantaka tsakanin ɗan adam da muhallinsa.
Wasu abubuwan da ake zargin cewa su suka kawo wannan annobar - ciki har da rasa muhalli da kuma amfani da cinikin namun daji - na kuma daga cikin abubuwan da suka sa aka samu raguwar namun dajin.

Wasu sabbin bayanai sun nuna cewa za a iya tsayar da rasa muhalli na dabbobi da kuma dawo da su yadda suke a da, idan aka ɗauki wasu matakai da kuma sauya yadda ake samar da abinci da kuma yadda ake cin abincin.
Yin hakan zai shafi yadda ake samar da abinci, da samar da makamashi da kuma kula da tekuna, in ji wani ɗan jarida da ke aiki a wani gidan talabijin na Birtaniya.

Asalin hoton, Getty Images
Ya za a misalta yadda aka yi asarar namun daji?
Wannan rahoton ya duba ko raguwar namun daji na zuwa ƙasa ne ko kuma sama. Rahoton bai bayyana takamaimai adadin dabbobin da aka rasa ba.
Raguwar da aka samu ta fi yawa ne a wurare masu zafi. Raguwar da aka samu ta kashi 94 cikin 100 a yankin Latin Amurka da kuma yankin Caribbean ita ce raguwa mafi yawa a duniya, inda tsuntsaye da macizai da dama suke cikin hatsari.
"Wannan rahoton na kallon abubuwan da ke faruwa ne a duniya da kuma buƙatar ɗaukar mataki domin dawo da yadda abubuwa suke tun asali," in ji Louise McRae na ƙungiyar kula da dabbobi ta Landan.
An kuma yi amfani da wannan binciken domin duba abubuwan da ake buƙata domin daina samun raguwar namun dajin.

Asalin hoton, Getty Images
Me sauran matakai da ake ɗauka ke nunawa dangane da rasa namun dajin?
Ƙungiyar International Union for Conservation of Nature ce ke tattara adadin dabbobin da ke da barazanar ƙarewa inda ƙungiyar ta yi bincike kan dabbobi da tsirrai sama da 100,000, an kuma samu cewa akwai sama da 32,000 da ke barazanar ƙarewa.

Asalin hoton, Getty Images
A 2019, wani kwamiti da aka kafa tsakanin gwamnatoci ya bayyana cewa akwai abubuwa masu rai kusan miliyan ɗaya da ke cikin barazanar ƙarewa, (dabbobi da tsirrai 500,000 da kuma ƙwari 500,000)
Rahoton WWF na daga cikin bincike daban-daban na irin wannan matsalar.
A Talata mai zuwa ne Majalisar Ɗinkin Duniya za ta bayyana binciken da ta yi kan irin wannan lamari a fadin duniya











