Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Zimbabwe na son sasantawa ne da Turawan da aka kwacewa gonakinsu?
Kasar Zimbabwe na cimma yarjejeniya da manoma fararen fata na ciki da wajen kasar da suka rasa gonakinsu shekaru fiye da ashirin da suka gabata lokacin da aka kwace musu gonaki da manufar kawo karshen mulkin mallaka dungurumgum.
Wilf Mbanga, Editan shafin jaridar Zimbabwe, ya yi duba kan batun, da kuma ko hakan na iya farfado da alakar kasar da kasashen yamma.
Labarin cewa daga karshe gwamnatin Zimbabwe ta amince ta biya manoma fararen fata diyya ya ba duniya mamaki.
Mutane da dama sun fusata, sun kuma rika nuna takaicinsu a shafukan twitter da na WhatsAPP, babu wanda ya yi farin ciki da haka.
Sai dai shugaba Emmerson Mnangagwa, ya yaba da yarjejeniyar da ya kira "mai cike da tarihi",
karkashin yarjejeniyar manoma fararen fata kusan 3,500 za su raba diyyar Dala biliyan uku da miliyan dari biyar.
Yarjejeniyar ta yi tanadin cewa za a biya rabin kudaden ne cikan shekara daya, yayin da za a karkasa sauran da za a biya zuwa shekara biyar.
Sauran wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da wasu bakaken fatar manoma 'yan kasar Zimbabwe su 400 da kuma wasu kalilan daga cikin manoma farar fata na kasashen waje, kusan 37 daga cikinsu, wadanda aka ba su kariya ta Yarjejeniyar Ba da Hannun Jari ta (Bippa).
Kwanan nan gwamnatin ta bayar da sanarwar cewa za a mayar wa da wadannan manoman gonakinsu.
Kalilan daga gwamnatocin kasashen turai ne ke maida hankali kan batun da ya shafi filaye a yanzu.
Yawancinsu sun fi maida hankali ne kan abin da ya shafi kare hakkin dan adam da kuma matsalar cin hanci da rashawa.
Dukkanin wadannan matsaloli na faruwa karkashin shugabancin shugaba Emmerson Mnangwagwa wanda ya dare mulki bayan tursasawa tsohon shugaban kasar Robert Mugabe sauka.
Shekaru 20 da suka gabata sha'anin noma ne babbar hanyar samun kudin shiga da musayar kudi tsakanin Zimbabwe da sauran kasashen duniya.
A shekarar 2000 ne mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya gamu da gagarumin cikas daga jam'iyyar MDC.
Tuni bashin kasashen waje da ake bin Zimbabwe ya zarce kima, in da yanzu haka yakai kaso 73.
Fitaccen masanin tattalin arzikin kasar da ake girmamawa John Roberson ya ce yiwuwar gwamnati ta samun kudaden da take bukata bata taka kara ta karya ba.
''Babu ta yadda zamu iya biyan sabbin basuka alhalin bamu biya tsoffin da ake binmu ba'' in ji shi.
Amma ya ce idan aka farfado da tattalin arziki kila darajar da kasar ke da ita a duniya ta sake farfadowa.