Gwajin Coronavirus: Shin gwajin yawu duk mako zai zai iya kawo ƙarshen annobar?

Illustration of a woman spitting

Asalin hoton, Emma Russell

    • Marubuci, Fergus Walsh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan kiwon lafiya

Ya kuke gani idan da a ce rayuwa za ta koma daidai kamar da kafin bullar cutar korona? Babu sauran bai wa juna tazara, babu rufe fuska, babu tsoron cutar korona.

Sai dai babban dalilin sanya dokokin duk kokari ne na dakile cutar don hana yaduwarta. Abin da muke bukata shi ne hanya mafi sauri kuma sahihiya ta gano wadanda suka kamu da cutar da ke kusa da mu.

Matsala ta farko ita ce mutane kadan ne kamar mutum daya cikin hudu da ake gano sun kamu da cutar suke nuna alamunta a ranar da aka yi musu gwaji.

Hakan na sanya barazanar mutanen da ba su san suna dauke da cutar ba su yada ta.

Matsala ta biyu ita ce yin gwajin. Hanyar da ake bi wajen yin gwajin ita ce ta sanya wani dogon tsinke ta cikin hancin mutum har ya tabo maƙogoro don lakuto majina. Wataƙila don ina da jin abu a jikina, amma dai ina ga amfani da tsinke mai kan audugar nan don zaƙulo majina ba abu ne mai dadi ba.

Ba na jin zan iya dinga yin irin wannan gwajin duk mako kamar yadda Hukumar Lafiya Ta Burtaniya take so.

A woman receiving a swab test from someone in a visor

Asalin hoton, Getty Images

Matsala ta uku ita ce daukar lokaci. Idan aka dauki majinar sai an aika da ita dakin gwaji inda za a shafe 'yan sa'o'i ana gwajin. Mutum tara cikin 10 da ke zuwa cibiyoyin gwaji kan yi sa'ar samun sakamakonsu cikin sa'a 24. Amma ba za a iya samun sakamakon a take ba.

Don haka abin da muke bukata shi ne gwajin cutar korona sahihi, mai sauki kuma wanda ba zai ɗauki lokaci ba.

Ana ta gwada yin gwajin da za a iya samun sakamako da gaggawa, kuma hakan zai taimaka wajen samun ci gaba.

Amma gwajin yawu ne zai kawo irin sauyin da ake so.

Yi tunanin a ce abin da kawai kuke buƙata shi ne tofa yawu a cikin wata ƴar kwalba don a gano ko kuna da cutar korona.

To sai dai hakan ba yana nufin matuƙar sauƙi ba ne. Sai an aika yawun zuwa ɗakin gwaji, amma sakamakon zai fi na majina saurin fitowa.

Jayne Lees da iyalanta na daga cikin mutanen da ake yi wa gwajin yawu na gwaji da za a shafe mako hudu ana yi a Southampton.

The Lees family doing the spit test

Na ga yadda Jayne da matasan 'ya'yanta hudu Sam da Meg da Billy, suka zauna kan tebur a kicin, suka tofa yawu a kan cokali suka zurara yawun cikin ƴar ƙaramar kwalbar gwaji.

Jayne ta ce: ''Gwajin zaƙulo majinar ba shi da daɗi sam, musamman idan dama ba ka da lafiya. Gwajin yawun ya fi sauƙi sosai.''

Fiye da mutum 10,000 ne da suka haɗa da likitoci da muhimman ma'aikata da iyalansu aka sanya a cikin shirin gwajin a birnin.

Jayne spitting onto a spoon

''Mun yi tunanin yana da muhimmanci ƙwarai a yi la'akari da yawu wajen gwajin,'' in ji Keith Godfrey ta Jami'ar Southampton, wacce take taimaka wa wajen shirya gwajin.

''Tantanin da ke ajiye yawu ne waje na farko da kwayar cuta ke harba a jiki. Hakan na nufin yawun mutane ne zai fara kamuwa da cuta kamfin sauran kafofin shakar numfashinsu.

''Idan har muna son gano masu dauke da cutar a matakin farko, to wannan hanyar ya kamata mu dinga bi a nan gaba.''

Nasarar gwajin ya danganta da yadda ake iya gano ƙwayar cutar korona da kyau a gwajin yawu.

Gloved hands holding a sample pot of saliva

Ana duba samfuran da ake ɗauka a binciken na Southampton ne a Cibiyar Lafiyar Dabbobi da Tsirrai da ke Surrey.

Farfesa Ian Brown shugaban ɓangaren nazari kan ƙwayoyin cuta ya ce: ''Muna cikin matuƙar farin ciki. Mun cimma nasarori da dama a makonnin da suka gabata, ta wajen shawo kan matsaloli wajen yin gwajin yawun.''

Wannan shi ne abu mafi ban sha'awa. Idan har aka ci gaba da wannan gwajin yadda ya kamata, to kafatanin mutanen birnin Southampton fiye da 250,000 za su iya yin gwajin yawu duk mako.

Map of the UK with illustrations of droplets

Asalin hoton, Emma Russell

Wata tawagar masana kimiyya karkashin jagorancin Farfesa Julian Peto na Makarantar Tsafta da Magunguna na Kasashe da ke da yanyain zafi ta Landan sun ba da shawarar cewa za a iya yi wa kafatanin al'ummar Burtaniya gwajin yawu duk mako.

Sun ce annobar cutar korona za ta iya kawo karshe kuma a'amura su koma daidai kamar a baya idan har aka dinga sa ido a kan jama'a. Hakan na nufin yin gagarumin gwaji.

A yanzu dai gwamnati ta ce mutum 300,000 kawai za ta iya yi wa gwaji duk rana, amma za a bukaci kara yawan zuwa mutum miliyan 10 duk rana.

Yadda hakan zai kasance shi ne, ka aika da yawunka, cikin sa'a 24 sakamakon zai fito. Idan sakamako ya nuna kana dauke da cutar to kai da iyalanka za ku killace kawunanku.

Gidajen cin abinci da wuraren taruwar jama'a kuma za su bukaci ganin shaidar da ke nuna cewa ba ka dauke da cutar na gwajin da ka yi na baya-baya kafin a bar ka ka shiga.

Fatan shi ne gano cutar da wuri zai taimaka wajen dakile annobar.

A text message saying that a Covid-19 test came back negative

Bayar da hadin kai ne babbar damuwar. Mutum nawa ne daga cikinmu za su iya tofa yawu a cikin kwalba duk mako? Ba zai dinga daukar lokaci ba sannan zai taimaka wajen kawo karshen yin nesa-nesa da juna da ake yi.

Idan har ya yi aiki so za a daina sa takunkumi sannan miliyoyin mutane za su fito daga wuraren killace kai. Za ku sake samun damar rungumar abokai da kakanninku.

Makarantu za su dinga yi wa yara gwajin yawu a makarantu duk mako. Sannan za a dinga yin gwajin a gidajen kula da tsofaffi. Haka kuma za a samar da cibiyoyin gwajin a filayen jirgi ta yadda za a dinga yi wa matafiya gwaji cikin hanzari.

An yi wa Jayne Lees da iyalanta gwajin yawun har sau biyu kuma ba sa dauke da cutar. Kuma ina ga haka abin yake ga sauran mutane da ke cikin aikin gwajin.

Idan ana so binciken ya yi aiki, to ana bukatar ya dinga gano masu dauke da cutar da wadanda ba sa dauke da ita.