Shirin N-Power: Dalili biyar da ya sa ake alfarma wajen ba da aiki a Najeriya

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba ne Buhari ya sake jan kunnen masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran ma'aikatan gwamnati da su guji amfani da matsayinsu wurin nemo aiki ga waɗanda suke so
    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

A ranar Laraba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jan kunnen masu riƙe da muƙaman siyasa da sauran ma'aikatan gwamnati su guji amfani da matsayinsu wurin nemo aiki ga waɗanda suke so.

A wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da al'adu Lai Mohammed ya fitar, shugaban ya ce wannan ɗabi'ar ta saɓa wa dokar gudanarwa ta aikin gwamnati.

BBC ta tattauna da Nuradeen Dauda, mai fashin baƙi kan al'amuran yau da kullum da kuma Auwwal Mahmud, wanda mai sharhi ne kan batun tattalin arziƙi, kan dalilan da ya sa ake alfarma wurin neman aiki a Najeriya.

Kwaɗayi

Kwaɗayi da kuma zari na daga cikin abubuwan da ke sa samun aiki ke yin wuya a Najeriya, in ji Nuradeen Dauda.

A cewarsa, "akwai ma'aikatan gwamnati da dama waɗanda suka mayar da sayar da aiki tamkar sana'arsu, sai mutum ya ba su kudi kafin su ba shi aiki".

"Idan aka fitar da sanarwar neman aiki, a maimakon su bari kowa ya nema, sai su koma suna sayar da aikin."

Ya ce har sai a ga ana sayar da aiki naira dubu 500 zuwa miliyan daya.

Short presentational grey line

Alƙawuran 'yan siyasa

Jama'a da dama na ganin cewa cikin ayyukan 'yan siyasa musamman 'yan majalisa har da alfarma wurin samun aikin gwamnati bayan wakiltarsu da suke yi.

A cewar Nuradeen, hakan na faruwa ne sakamakon tun asali wasu daga cikin 'yan majalisar ne ke yaƙin neman zaɓe da cewa idan sun samu nasara za su samar wa matasa da aikin yi a wani lokaci ma na gwamnati.

Ya ce "aikin 'yan majalisa ba samar wa mutane aiki ba ne, sai dai za su iya mayar da hankali wurin ganin cewa an bi dokokin ƙasa wurin ɗaukar aiki tare da ba kowane ɗan ƙasa dama ya gwada ƙoƙarinsa".

Short presentational grey line

Rashin kyakkyawan tsari

NYSC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubun-dubatar matasa ne ke kammala karatun jami'a a duk shekara a ƙasar ba tare da samun ayyukan yi ba

Tsarin da aka gina Najeriya tun asali ba kyakyawan tsari bane, "itama ƙasar an gina ta ne bisa alfarma", in ji Auwwal Mahmud.

A cewarsa, yadda ƙasar take haka mutanen ƙasar suke, shi ya sa zai yi wuya a samu sauyi a ƙasar.

"Tsarin da muke tafiya kansa shi ne tsari da ake tafiya shekaru da dama kuma kan alfarma aka gina shi kuma har yanzu ƙasar ta ƙi ci gaba".

A cewarsa, rashin kishi da rashin ɗa'a na su kansu ma'aikatan da aka ɗauka shekaru da dama da suka wuce shi ya sa har yanzu ake cikin wannan tsari na alfarma.

Short presentational grey line

Bangaranci

Da dama daga cikin masu samun muƙamai na siyasa ko kuma aikin gwamnati abin da suke fara tunani shi ne ta ya za su azurta 'yan uwansu ko kuma na jikinsu, in ji Nuradeen Dauda.

Ya ce saboda yadda tsarin ƙasar ya taho, waasu ya zama dole garesu su yi hakan, idan ba haka ba 'yan uwansu da abokan arzƙinsu za su fara zaginsu kan cewa "sun samu ba su taimaki kowa ba".

Wannan dalili ne ya sa idan ɗan wata ƙabila ya samu muƙami, sai mutane su fara cewa "namu ya samu", ma'ana suna da mai uwa a gindin murhu.

Shi kuma wanda ya samu muƙamin zai yi duk wani ƙoƙari da zai yi wurin ganin cewa 'ya azurta 'yan uwansa ko kuma 'yan ƙabilarsa.

Short presentational grey line

Cin hanci da rashawa

Zai yi wuya a kawo wata matsala a Najeriya da ke ci wa 'yan ƙasar tuwo a ƙwarya ba tare da an lissafo da cin hanci da rashawa ba.

Batun cin hanci da rashawa za a iya cewa yana taka muhimmiyar rawa wurin alfarmar samun aiki a Najeriya.

Cin hanci da rashawa ya dabaibaye tsarin da ƙasar take da shi a ƙasa na ɗaukar aiki.

Akwai zarge-zarge da ake yi na ma'aikatu da sai ka biya maƙudan kuɗi kafin samun aiki, wasu ma'aikatun kuma su sayar da aikin ga wasu can daban kan kuɗi masu yawa.

Wannan layi ne

Sharhi: Mustapha Musa Kaita, BBC Abuja

Rashin aikin yi a Najeriya na ɗaya daga cikin matsalolin da suka addabi jama'ar ƙasar musamman matasa.

Dubun-dubatar matasa ne ke kammala karatun jami'a a duk shekara a ƙasar ba tare da samun ayyukan yi ba.

Abu na farko da matasa kan yi bayan kammala jami'a ko kuma kwalejojin ilimi ko na kimiyya shi ne rarraba takardun shaidar kammala karatunsu zuwa 'yan uwa da abokan arziƙi domin neman aiki

Ana yin hakan ne sakamakon ammanar da aka yi da cewa ba a samun aiki a Najeriya sai an san wani ko kuma sai idan mutum na da "ƙafa".

A Najeriya idan aka ce mutum na da ƙafa ko kuma doguwar ƙafa, ana nufin mutum ya san wani hamshaƙi ko kuma mai faɗa a ji ko kuma wani da ke da hanyar samo masa aiki ko kuma kwangila.

A wannan dalili ne ya sa waɗanda ba su da "kafa", kamar yadda ake faɗa suke rasa ayyukan yi, sai dai kaɗan daga cikin waɗanda Allah ya nufa da samun aiki.

Akwai wasu manyan ma'aikatu a ƙasar masu biyan albashi mai tsoka da mutane da dama ba su karambani wajen neman aiki a irin waɗannan wurare. Hakan na faruwa ne domin tuni an yi ammanar cewa idan baka san wani babba a ma'aikatun ba ko kuma a ƙasar, ba za ka samu aiki ba.

A baya-bayan nan sakamakon yadda matsalar rashin aikin yi ta ƙara ta'azzara, jama'a da dama na ƙoƙrin neman aiki a ƙasar ko ta halin ƙa'ƙa ko da kuwa don su saya da kudinsu ne.

Wannan layi ne