Aikin N-Power: Tambayoyin da aka fi yi game da shirin rage raɗaɗin talauci a Najeriya

Asalin hoton, Twitter/npower_ng
- Marubuci, Daga Olaronke Alo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist, BBC Pidgin, Lagos
Wadannan su ne wasu daga cikin tambayoyin da jama'a ke yi kan shirin N-Power na 2020, kuma BBC ta tattara amsoshi na gaskiya na tambayoyin da ake yawan yi kan shirin N-Power.
Mutum sama da miliyan daya ne suka yi rijista a shirin N-Power wanda shiri ne na tallafa wa matasan Najeriya wadanda ba su da aikin yi inda kuma ake horar da su.
Ga wasu daga cikin tambayoyin da ake yawan yi da kuma amsoshin da suka kamata ku sani:

Asalin hoton, Twitter/npower_ng
Shin an fitar da takarda ta rijistar N-Power?
Amsa: Eh an fitar da ita.
Gwamnatin Najeriya ta buɗe shafin yin rijistar shirin ta intanet a ranar Juma'a, 26 ga watan Yuni da misalin karfe 11:45. An bude shafin ne ga 'yan shekaru 18-35 su yi rijista.
Gwamnatin ta ce za a rufe rijistar ne bayan makonni shida da fara rijistar.

Ta yaya zan shiga shirin N-Power?
Amsa: A je shafin N-Power na gaskiya wato - https://portal.npower.gov.ng.
Sai a zaba a daya daga cikin guraben nan uku - N-Power Knowledge, N-Power Volunteer corps, or N-Power build.
Daga wannan shafin, za ku ga shirye-shirye iri daban-daban da za ku iya zaba dangane da abin da ya dace da ku.

Ta yaya zan yi rijista da shirin N-Power na 2020?
Amsa: Da zarar an shiga shafin na N-Power, sai mutum ya cike hanyar sadarwarsa (Adreshin Email da lambar waya) ga gurbin da suka bayar na cikewa.
Ta hakan ne bayanan da ka cike zai dauke ka zuwa adireshinka na imel.
Da zarar ka tabbatar da adireshinka na imel, sai ka cike lambar bankinka ta BVN da ranar haihuwa da shekara a wannan tsarin (rana/wata/shekara).

Nawa ne albashin masu shirin N-Power?
Amsa: Albashin wadanda suke cikin shirin N-Power ya zuwa Afrilun 2020.
Shirin koyarwa na N-Power: 28,000-30,000 a duk wata.
Shirin noma da kiwo na N-Power: 25,000-30,000 a duk wata.
Shirin kiwon lafiya na N-Power: 30,000-40,000 a duk wata.
Shirin Community Education na N-Power: 10,000- 30,000 a duk wata.
Shirin ƙirƙire-ƙirƙire na N-Power: 10,000-30,000 a duk wata.
Shirin koyon ƙirƙirar manhajoji na kwamfuta na N-Power: 20,000-40,000 a duk wata.
Shirin koyon gyara kwamfuta da wayoyi da ƙirƙira na N-Power: 20,000-40,000 a duk wata
Shirin gine-gine da ƙere-ƙere na N-power: 27,000-30,000 a duk wata.

Mutum nawa N-Power za ta iya dauka?
Amsa: Kamar yadda hukumomi suka bayyana, shirin zai dauki mutane 400,000 da za su yi aiki a bangarori daban-daban da suka hada da aikin gona da koyarwa da gine-gine da ƙirƙire-ƙirƙire da kuma kimiyya da fasaha.
Tuni fiye da mutum miliyan daya suka yi rijista a wannan shirin.

Asalin hoton, Twitter/npower_ng
Ta yaya zan siga shafin intanet na N-Power?
Answer: Ziyarci npower.fmhds.gov.ng
Ka sanya adireshin imel dinka sannan ka kirkiri lambobin sirri domin soma rijista.

Mutum nawa ne a halin yanzu karkashin shirin N-Power?
Amsa: A 2016, gwamnatin Najeriya ta dauki mutum 200,000 a shirin N-Power.
A 2017, an dauki sama da mutum 300,000. Wadanda aka dauka aikin za su shafe shekaru biyu ne suna aikin kuma kowa za a ba shi na'urar kwamfuta da zai yi aiki da ita.
Shirin N-Power na 2020 na rukunin C na da niyyar daukar a kalla mutum 400,000.

Asalin hoton, @npower_ng Twitter
Mene ne shirin N-Power Agro?
Shirin N-Power Agro shiri ne da ke ba da dama ga matasa su koyi dabarun noma da kuma amfani da ilimin domin su dogara da kansu ko bayan shirin N-Power ya kare.

Mene ne shirin N-Power build?
Shirin N-Power Build shiri ne da zai koya wa matasa kusan dubu 75 da ba su da aikin yi dabaru daban-daban a bangarori daban-daban da suka hada da:
- Aikin gine-gine
- Ƙere-Ƙere
- Fasahar gyaran motoci
- Sarrafa gorar-ruwa da gas.

Me shirin N-Power yake nufi?
N-Power shiri ne da gwamnatin tarayya ta hannun hukumar walwala ta Najeriya ta kirkira domin samar da ayyyukan yi ga matasa wadanda ba su da aiki ko kuma ba su da kudin shiga.
Npower zai horas da mutane su samu kwarewar da za ta samar musu aiki.












