'Yadda na tsinci kaina a tsakiyar labaran ƙarya kan ɗan siyasar Senegal'

Illustration of Michelle Madsen at a laptop in one half of the picture, and a hooded figure representing 'Michelle Damsen' in the other.

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Daga Michelle Madsen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, 'Yar jarida mai binciken ƙwaƙwaf

Wata rana na fito daga ajin koyon rawa a Arewacin Landan a ƙarshen watan Janairu, duba wayata ke da wuya sai na ga lambobi da dama sun kirani daga nahiyar Afrika.

Ban san me ke faruwa ba - sai na duba saƙonnina na Facebook da Twitter - sai na ga ɗaruruwan saƙonni inda ake tambayata kan abu ɗaya - ni ce "Michelle Damsen", marubuciyar wani labari mai ban al'ajabi wanda ya zama abin ce-ceku-ce a Senegal?

"Lamarin cin hanci da rashawa yana girgiza ƙasata kuma sunanki na ciki."

"Mun damu tun bayan da muka ga wata maƙala da kika rubuta."

"Ni dan jarida ne daga Senegal kuma ina so na yi magana da ke!"

Illustration of a hand holding a phone with missed calls and messages.

Asalin hoton, George Wafula/BBC

Duk suna so su san ko ni ce na rubuta wata maƙala mai taken "Ƙalubalen da ake fuskanta wurin satar albarkatun ƙasa a Afrika", inda aka wallafa rubutun a wani shafin intanet na ƙasar Ghana a ranar 9 ga watan Janairun 2019.

A rubutun da aka wallafa, an zargi dan takarar shugaban ƙasar Senegal Ousmane Sonko da karɓar cin hanci mai kauri daga wani kamfanin mai na Turai kuma sunan "Michelle Damsen," ne a kan labarin.

Wannan na zuwa ne makonni kaɗan kafin zaben shugaban ƙasa a Senegal inda kuma Mista Sonko na ɗaya daga cikin manyan abokan karawar Shugaba Macky Sall na Senegal.

A matsayina ta 'yar jarida mai zaman kanta kuma wacce take da ƙwarewa a ɓangaren binciken kwakwaf kan cin hanci da rashawa a Yammacin Afrika, na rubuta labarai masu dumbin yawa kan batun Senegal da kuma kamfanonin mai.

Har ma na yi wani rubutu kan Mista Sonko bayan ya wallafa wani littafi inda yake zargin dan uwan shugaban Senegal Aliou Sall da cin hanci da rashawa - zargin da ya musanta.

Illustration of a woman with glasses with a screen reflected in the glasses.

Asalin hoton, George Wafula/BBC

Ni dai na san ba ni na rubuta labarin da aka wallafa ba, kuma na faɗa wa sauran 'yan jaridar da suka nemi ni hakan. Amma na girgiza da bayanan da ke cikin labarin da suka fito daga Senegal da kuma yadda cikin sauri aka danganta labarin da ni.

A jaridar Press Afrik ma har sunana aka kira kai tsaye, inda aka ce ni na rubuta labarin. Labarin kuma da aka wallafa a wata kafar labarai ta intaent wato Seneweb an ambato Frank Timis, wani ɗan kasuwa daga Birtaniya wanda ke kasuwanci a Senegal kuma yana da alaƙa da dan uwan shugaban ƙasar, wanda ni da wasu 'yan jarida muka samu tallafi domin gudanar da bincike.

An samu tallafin kuɗin ne daga wata ƙungiya ta aikin jarida a Netherlands, ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙiƙiro ƙungiyar bayar da tallafi ta Oxfam.

Wannan ne ya sa na ji tsoro bayan an ambato Oxfam a ɗaya daga cikin takardun da aka wallafa a labarai. Akwai tambarin kamfanin mai na Tullow Oil inda aka saka shi a matsayin hatimi a tsakiyar sunan Ousmane Sonko.

Tullow Oil da kuma Mista Sanko sun musanta duka zarge-zargen da ake yi musu inda kuma masu bincike suka yi sauri suka bayyana cewa takardun na bogi ne.

Oxfam sun bayyana mani cewa ba su karɓi wani tallafi ba daga kamfanin mai ɗin, amma sun biya Mista Sonko kudin horaswa a baya. Wannan ƙanshin gaskiyar ne ya sa da dama suka ɗauka cewa wannan labarin gaskiya ne.

Presentational grey line
Presentational grey line

Bayan na shaida wa 'yan jarida daga masu tabbatar da sahihancin labari na Afrika da kuma kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ni ban rubuta wata makala a jaridar Modern Ghana ba, wata jaridar Senegal ta wallafa labarin tana cewa ikirarin na karya ne.

Duk rade-radin da ka yi a kafafen yada labarai bai fi na sa'a 48 ba. A wannan lokacin duk inda ka duba sunanan za a gani a kanun labarai a Dakar kuma daya daga cikin jaridun ta je shafina na Facebook ta dauki hotona a wajen wani daurin aure domin gudanar yin labarinsu.

Na so in bincika wacece " Michelle Damsen" kuma ta yaya wannan makalar karyar ta bazu a Senegal kamar wutar daji.

Na tuntubi shugaban jaridar intanet ta Modern Ghana, Bright Owusu, wanda ya ce sun wallafa makalar a shafin ra'ayin mutane a shafinsu, wanda ke kawo ra'ayin mutanen Ghana da na wasu sauran sassan nahiyar Afrika.

Owusu ya ce marubucin jaridar Modern Ghana ya matukar kaguwa ya ga an wallafa labarin, ya kuma nemi ya ba wa jaridar kudi domin ta wallafa labarin.

Owusu ya ce jaridar ba ta taba karbar kudi ba domin ta wallafa wani rubutun ra'ayi daga wajen marubuci, amma tana karbar dalar Amurka 100 domin buga sanarwar 'yan jarida a shafinta.

Illustration of a woman on the phone while looking at a laptop

Asalin hoton, George Wafula/BBC

Mutumin da ya kira wayar in ji Owusu na da yanayin magana irin na 'yan Afrika.

Da bayanan da aka samu daga sakon email da marubucin ya aika wa Owusu da kuma kiran wayar da ya yi, ina amfani da layin "Orange" wani masanin kwafiyuta mai kuma binciken intanet a kamfanin Reckon Digital, na kokarin bibiyar bayanan marubucin.

Da aka duba layin 'Orange" din ana gano an yi masa rijisata a Amurka da sunan "Baba Aidara".

Na yi matukar kaduwa - Baba Aidara wani dan jarida ne da ke zaune a Amurka kuma mai yawan sukar gwamnatin Senegal. Kuma yana daya daga cikin abokan huldarmu.

Na yi magana da Aidara, wanda ya musanta cewa shi ne ya aika labarin. Ya ce sai dai in kutse aka yi masa, kuma yana zargin gwamnatin Senegal da aikata hakan.

Wani mutum da wata mata na kallon wani abu tare.
Bayanan hoto, Michelle na ziyartar shafukan da suka wallafa labarin, ciki harda Seneweb wadanda daga baya suka yi magana.

'Yan jarida da na yi magana da su a Senegal sun ce an fuskanci rikicin labaran bogi a kasar yayin zaben kasar na 2019, kuma duka bangarorin da suka nemi zaben sun ta yada labaran.

Amma da yawa daga cikin 'yan kasar na zargin labarin ya fito ne daga tawagar neman zaben shugaba Sall, wadanda suka kunshi kwamitinsa na yada labarai wanda ya hadarda kwararru kan abin da ya shafi inaten.

Na yi kokarin magana da tawagar Mista Sall da mai magana da yawun kungiyar, sai dai babu wanda ya yarda ya amsa tambayata ko kuma mu yi hira.

Michelle and a man watch a session in a parliament chamber
Bayanan hoto, Michelle na jira da gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin Senegal