Coronavirus: Darasin da duniya za ta koya daga yaki da Ebola

Ellen Johnson Sirleaf

Asalin hoton, Getty Images

Ellen Johnson Sirleaf ce ta zama shugabar kasa mace ta farko a nahiyar Afirka da ta jagoranci kasar Liberia na shekaru 12, har tsakanin 2014 zuwa 2016 lokacin da aka samu barkewar cutar Ebola da ta kashe kusan mutum 5,000 a kasarta.

BBC ta tambayi tsohuwar shugabar kasar wadda ta taba samun kyautar Nobel kan ra'ayinta dangane da annobar coronavirus.

Short presentational grey line

Ya ku jama'ar duniya,

A ranar 19 ga watan Oktobar 2014 a daidai lokacin da ake cikin rikicin cutar Ebola a Yammacin Afirka, jama'ar kasata a wancan lokaci kusan mutum 2,000 sun riga sun mutu kuma jama'a da dama na ci gaba da kamuwa da cutar.

Na rubuta wasika ga duniya inda na bukaci a tallafa min da jami'an lafiya da kuma kayan aiki.

Na bukaci a ba ni hadin kai daga kasashen duniya domin shawo kan abin da muke tsoro ya zama annoba a fadin duniya.

A yau ma zan yi amfani da wannan dama na kara jadadda goyon bayana a kan hakan.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

A shekaru shida da suka gabata, na yi bayani kan yadda yakin da aka yi a Liberia a can baya ya yi sanadiyar tabarbarewar tattalin arziki da fannin lafiya na kasar, wanda hakan ya sa cututtuka ke iya yaduwa a cikin sauri.

Na kuma jaddada yadda gudunmawar da duniya za ta bayar zai shafi rikicin Yammacin Afirka.

Na bayyana cewa duk wata cuta da ba za a iya tunkararta ba, ko ina take a fadin diuniya, kuma a duk kauyen da take, babbar barazana ce ga rayuwar bil adama.

Duniya ta amsa wannan kira nawa kuma an tashi tsaye.

President Barack Obama speaks during a meeting with Liberian President Ellen Johnson Sirleaf, Guinean President Alpha Condé(R), and Sierra Leonean President Ernest Bai Koroma(L) in the Cabinet Room of the White House April 15, 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Sirleaf, a fadar White House a 2015, inda take aiki da shugabannin kasashen Saliyo (hagu) da Guinea (dama) da kuma Amurka domin yaki da Ebola

An samu gudunmawa matuka daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Amurka.

A haka muka yi wannan yaki. A wannan dalili ne ya sa a halin yanzu aka samu riga-kafi da kuma magungunan rage radadin ciwon, wannan abin godiya ne ga masana kimiyya na duniya.

A daidai wannan lokaci da aka samu barkewar coronavirus, Ina kara mika kokon bara ga 'yan uwana a duniya.

Ina wannan magana ne da la'akari da cewa na san irin wahalar da kasashen nahiyar Afirka ke ciki, cutar za ta yi matukar illa idan ta yi kamari a nahiyar wadda ba ta shirya yaki da ita ba.

Dole mu yaki wannan cuta, mu karya lagonta.

Ebola safety poster

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Darussan da Liberia ta koya daga rikicin Ebola za a iya amfani da su wajen yaki da coronavirus

A bayyane yake cewa an samu nakasu wajen tunkarar wannan cuta a farkon barkewarta, daga Asiya da Turai har zuwa Amurka.

An ki daukar mataki kan alamun da suka nuna. An bata lokaci.

An boye bayanai, an sauya su. Mutane sun daina gaskata abu.

Karin Labaran da za ku so ku karanta

'Na yi irin wannan kuskure'

Tsoro ya sa mutane sun gudu, sun buya, suna neman kare abin da yake nasu ne, a yayin da mafitar daya ce, kuma tana nan cikin al'umma.

Na san haka. Na yi irin wadannan kura-kuran a 2014, haka ma sauran wadanda suke da karfin fada a ji na duniya. Amma mun gyara, kuma mun yi nasara tare.

Muna cikin tsaka mai wuya saboda yadda ake ta rufe kan iyakokin kasashe a duniya don hana yaduwar cutar.

A bayyane take cewa an samu matsala matuka wajen dakile coronavirus a lokacin da ta fara bulla.

Ellen Johnson Sirleaf
Getty Images
Every person, in every nation, needs to do their part. This realisation led to our turning point of disease control in West Africa"
Ellen Johnson Sirleaf
President of Liberia, 2005-17
Presentational white space

Kar mu bari mu dauki hanya marar bullewa a wannan karon. Hakan ba ya nufin cewa a bar kowace kasa da iyawarta ba. Sai dai kuma, akwai bukatar kowace al'umma ta dauki matakan kariya, kamar matakan rufe kan iyakokin nan zai yi amfani.

A yayin da nake kallon abin da ke faruwa daga gidana da ke Monrovia, abin da ke karfafa gwiwa a yau shi ne yadda ake nuna kwarewa da yadda ake musayar ilimi na kimiyya da kayayyakin aiki da magunguna.

Abin na faruwa a kasashe kuma yana ci gaba a kasashen duniya da dama, don haka dole sai kowa ya sa hannu wajen kawo karshen abin.

Karin labarai masu alaka

'Mun kasance masu juriya'

Wannan juriya ce ta kai ga sauya magance cuta a Yammacin Afirka.

A Liberia, mun jure wa annobar Ebola, mun jajirce, da bin matakai na lafiya da muke da su za su taimaka wajen yaki da cutar Covid-19.

Na yi imanin wannan hanyar ita ce muke a kanta.

Ina da cikakken imani kan kokarin mutum, imani da samun shugabanni a wannan lokaci a dukkanin matakai na al'umma, cewa bambancin addini da kabila ya shafe idan aka kwatanta da yadda muka hadu kan imani da girman addu'a da kuma Ubangiji.

A yayin da muka kasance a killaci a 'yan makwanni masu zuwa, ina addu'ar tabbatar da lafiyar al'ummar duniya, Kuma na bukaci kowa ya tuna cewa matsayin na 'yan Adam mun dogara ne da gaskiya cewa rayuwa mafi inganci ita ce rayuwa domin wasu.

Za ku iya sauraren Ellen Johnson Sirleaf tana karanta wasikarta a shirin Focus on Africa na BBC World Service a ranar Linitinin 30 ga Maris karfe 3:00 na rana agogon GMT.