''Lokaci ya yi na ayyana MKO shugaban Nigeria''

Lokacin karatu: Minti 1
Wasu masu fafututukar kare hakkin dan adam a Nigeria, sun ce lokaci ya yi da za a ayyana MKO Abiola wanda ake kyautata zato shi ya lashe zaben shekarar 1993 da gwamnatin mulkin soji ta soke, a matsayin shugaban kasar.
Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a ranar Lahadi da aka cika shekara 23 da tunawa da ranar da aka soke zaben da Mista Abiola ya tsaya a karkashin jam'iyyar SDP.
Sun kuma ce dole ne wadanda suka tafka kuskure su fito domin neman gafara a kan zaben da suka soke.
A shekarar 1993 gwamnatin mulkin soji ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben da ake kyautata zaton Abiola ne ya ci, al'amarin da ya jawo ka-ce-na-ce a Najeriyar.
Daga Legas wakilinmu Umar Shehu Elleman ya aiko mana da wannan rahoto:







