An haramta sa nikabi a jami'ar Alkahira

Asalin hoton,
Jami'ar birnin Alkahira ta kasar Masar ta haramta wa ma'aikatanta mata sanya nikabi a cikin aji.
Jami'ar ta ce ta dauki matakin ne domin saukaka bayani tsakanin dalibai da malamai.
Haramcin shi ne na farko a wata jami'a a Masar kuma masu sharhi na ganin cewar matakin zai janyo cece-kuce.
Dokar ta soma aiki daga ranar Talata.
Galibin mata a Masar na saka Hijabi a bainar jama'a amma kuma cibiyoyin soji sun haramta wa masu nikabi shiga gine-ginensu saboda dalilan tsaro.







