An samu ci gaba a rigakafin maleriya

Zazzabin cizon sauro ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin mutane.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Zazzabin cizon sauro ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin mutane.

Gwaji na karshe da aka yi wa wani maganin rigakafin zazzabin cizon sauro -- na farko da ya taba kai wa wannan mataki -- ya nuna cewa maganin yana bayar da 'yar kariya ga kananan yara daga cutar mai kisa.

Bayanan gwajin maganin da aka wallafa a mujallar nan ta harkokin lafiya, The Lancet, sun nuna cewa maganin mai suna RTSS ya bayar da kariya ga kusan yawan yara daya bisa uku wadanda aka yi wa rigakafi da shi.

Masana kimiyya sun ce duk da karancin tasirinsa, ya zuwa yanzu, maganin shi ne gaba wajen rigakafin cutar ta zazzabin cizon sauro, wadda ke hallaka sama da yara rabin miliyan a duk shekara a Afrika.

Jagoran masu yaki da cutar na kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya ta Medecins Sans Frontieres, Martin de Smet, ya ce duk da karancin tasirin maganin zai kare rayukan mutane da dama.

Ya ce'' ina ganin maganin zai yi amfani sosai musamman a kasashen da ake fama da cutar matuka.''