An yi jana'izar wadanda aka kashe a Borno

Jami'an tsaro a Nigeria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rahotanni sun ce har yanzu ana zaman dar-dar a kauyukan da abun ya shafa.

An yi jana'izar mutane fiye da 40 da wasu 'yan bindiga suka kashe a wasu kauyuka hudu da ke kusa da garin Chibok a jihar Borno.

Rahotanni sun ce mazauna yankin na ci gaba da zama cikin zullumi, tun bayan harin da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a ranar Lahadi inda kuma suka kona coci hudu.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba akan hare-haren.

A watan Afrilun da ya gabata ne 'yan Boko Haram suka sa ce 'yan mata fiye da 200 a garin Chibok da ke jihar Borno kuma har yanzu ba a gano su ba.