Mutane10 sun mutu a wata fashewa a Bauchi

Asalin hoton, AFP
Wani abu da ake kyautata zaton bam ne da ya fashe a wani gidan karuwai a birnin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya hallaka mutane 10 da jikkata wasu 14
Lamarin ya faru ne a unguwar Bayan-Gari da ke cikin birnin na Bauchi, da kusan karfe goma na daren Juma'a, yayin da jama'a ke holewa a unguwar wadda ta yi suna da wuraren rawa da mashaya.
Kakakin rundunar yansandan jihar ta Bauchi, DSP Haruna Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kawo yanzu dai ba a tabbatar da ko hari ne na kunar bakin wake ko kuma dasa abin fashewar aka yi ba.







