'Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa mutane sama da 20 ne suka mutu, sannan wasu da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Hakan ya biyo bayan wasu hare-hare da wasu 'yan bindiga sanye da kayan soji suka kai a yankin Fadan Karshi da kuma Nando na karamar hukumar Sanga dake kudancin jihar.
Wasu rahotanni dai na cewa an cafke daya daga cikin yan bindigar, yayin da aka dauki lokaci ana musayar wuta tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro.
Kudancin Kaduna na fama da rikice-rikice masu nasaba da kabilanci da kuma addini.







