Fulani na taro kan sha'anin tsaro a Nigeria

Kungiyoyin Fulani makiyaya a Nigeria da wasu kasashen Afrika na taron kwanaki 2 a Kaduna domin tattauna yadda za'a shawo kan matsalolin da ke addabar Fulani.
Manufar taron shi ne samar da hanyoyin zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Masana da sauran masu ruwa da tsaki za su gabatar da kasidu a taron wanda ofishin mai baiwa shugaban Nigeria shawara ta fuskar tsaro ya shirya taro.
Rikice rikice tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Najeriya kan yi sanadiyyar asarar rayuka da kuma dukiyoyi.







