Sabon rikici ya barke a Wukari

Asalin hoton, AFP

Rahotanni daga Jihar Taraba a Najeriya sunce wani sabon tashin hankali mai nasaba da kabilanci da addini ya barke a kananan hukumomin Wukari da Ibi.

Bayanai sun nuna cewa an samu hasarar rayuka da dukiya, amma dai kura ta lafa.

Dama dai an dade ana zaman doya-da-manja tsakanin al'umomin yankunan, kuma ranar Lahadi da safe sai kona wani shagon harkokin wayar salula ya jawo sake tashin rikici.

Shagon da aka kona dai na wani Bahaushe ne, kuma Hausawa da Fulani sun yi zargin cewa Jukunawa ne suka kona shi, lamarin da ya haifar da cacar baki tsakanin matasan bangarorin biyu.

Daga bisa kuma lamarin ya ta'azzara, har ya kai ga kashe-kashe da kone-kone tare da amfani da muggan makamai da suka hada da bindigogi.

Shugaban matasan Hausa Fulani na Karamar Hukumar Wukari, Malam Audu Ali, ya gayawa Sashen Hausa na BBC cewa an kashe kimanin mutane 30 a rikicin.

Shi ma shugaban matasan Jukunawa na Karamar Hukumar Wukarin, Mista Zando Hoku, ya tabbatar da cewa kona shagon ne musabbabin tashin hankalin, amma ya musanta hannun 'yan kabilarsa a kona shagon.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji, ya ce ana bincikin musabbabin tashin hankalin.

Rahotanni daga yankin Ibi, mai makotaka da Wukarin, sun nuna cewa rikicin ya bazu zuwa can inda nan ma aka bada labarin asarar rayuka da dukiyar jama'a.