Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II

A ranar Litinin 9 ga watan Yunin 2014, aka rantsar da sabon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, inda Gwamna Rabiu Kwankwaso ya mika masa takardar soma aiki.

Sabon Sarkin Kano, Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ya maye gurbin marigayi, Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu ranar Juma'a 6 ga Yunin, 2014
Bayanan hoto, Sabon Sarkin Kano, Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ya maye gurbin marigayi, Alhaji Ado Bayero wanda ya rasu ranar Juma'a 6 ga Yunin, 2014
Hakimai a Masarautar Kano sun yi wa Sabon Sarki mubaya'a, bayan da aka rantsar da shi a matsayin Sarkin Kano na 14.
Bayanan hoto, Hakimai a Masarautar Kano sun yi wa Sabon Sarki mubaya'a, bayan da aka rantsar da shi a matsayin Sarkin Kano na 14.
Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da na Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da mataimakinsa,Dr. Abdullahi Umar Ganduje suna sauraron jawabin mai martaba sabon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da na Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da mataimakinsa,Dr. Abdullahi Umar Ganduje suna sauraron jawabin mai martaba sabon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II yana karbar gaisuwa daga manyan bayin sarki da suka hada da Shamaki da Dan Rimi.
Bayanan hoto, Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II yana karbar gaisuwa daga manyan bayin sarki da suka hada da Shamaki da Dan Rimi.
Daya daga cikin hakimai a masarautar Kano, na karbar umurni daga Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II.
Bayanan hoto, Daya daga cikin hakimai a masarautar Kano, na karbar umurni daga Mai Martaba, Malam Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano tare da Dan Rimin Kano da Bakin rawani da kuma daya daga 'ya'yan Marigayi Sarkin Kano kuma Hakimin Fagge, Alhaji Mahmud Ado Bayero.
Bayanan hoto, Sarkin Kano tare da Dan Rimin Kano da Bakin rawani da kuma daya daga 'ya'yan Marigayi Sarkin Kano kuma Hakimin Fagge, Alhaji Mahmud Ado Bayero.
Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II tare da Shamaki da Dan Rimi.
Bayanan hoto, Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II tare da Shamaki da Dan Rimi.
Mawakan fadar masarautar Kano, na murnar rantsar da sabon Sarki a ranar 9 ga watan Yunin, 2014.
Bayanan hoto, Mawakan fadar masarautar Kano, na murnar rantsar da sabon Sarki a ranar 9 ga watan Yunin, 2014.