An yi sulhu tsakanin masu rikici a Taraba

Asalin hoton,
Al'ummomi masu gaba da juna a garin Wukari na Jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kawo karshen zub da jini a tsakaninsu a jiya.
Daruruwan mutane ne aka kashe a cikin rikice-rikicen kabilanci da addini a sassa daban-daban na jihar musamman a cikin makonnin baya-bayanan.
Al'umomin Tiv da Jukun da kuma Fulani wadanda ke kai wa juna hare-hare sun amince cewa daga yanzu babu sauran zubar da jini da sunan kabilanci ko addini a cikin Jihar Taraba.
Bangarorin biyu sun yi alkawarin ba zasu sake kaiwa junansu farmaki ba.






