"Dakarun Nigeria na azabtar da jama'a"

Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarun tsaro Nigeria sun taka hakkin bil adama a fadan da suke yi da 'yan Boko Haram.
Babbar jami'ar Majalisar Navi Pillay ta shaidawa manema labarai a Abuja cewar sojojin Nigeria a lokacin yaki na kusan shekaru biyar da suka shafe suna yi da 'yan Boko Haram sun gallazawa jama'a tare da azabtarda mutane.
A cewarta sojoji sun yi kisan gilla sannan kuma sun tsare mutane ba bisa ka'ida ba.
Rikicin 'yan Boko Haram a Nigeria ya janyo mutuwar dubban mutane a arewacin kasar.







