NDLEA ta kwace hodar ibilis a Kano

Hukumomi a Nigeria sun kwance hodar abilis da aka yi fasakaurinta daga kasar Brazil zuwa birnin Kano.
Jami'an hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasar-NDLEA sun damke Nnemeka Charles wanda ya shigo da hodar abilis din mai nauyin kilogram uku.
Mutumin ya kunshe hodar ibilis din a cikin kwallayen amsa kuwwa tun daga Brazil zuwa Nigeria.
Hodar ibilis din da aka kwace ta kai darajar naira miliyan 81.
Masu safarrar miyagun sun maida kasashen Afrika hanyar fasakaurin miyagun kwayoyi zuwa nahiyar Turai da Amurka.







