An kashe fitaccen Malamin Sunna a Syria

Gidan talabijin din gwamnatin Syria yace, an kashe wani fitaccen malami mabiyin mazhabar Sunni dake goyon bayan gwamnati sakamakon wani harin bam a wani masallaci dake tsakiyar birnin Damascus.
Gidan talabijin din yace, akan kashe malamin mai suna, Dokta Muhammed Al Bouti ne sakamakon harin bam da 'yan ta'adda su ka kai a masallacin Iman yayin da malamin yake gabatar da wa'azi.
Gidan talabijin din ya kuma ce, an samu asarar rayuka.







